Betrand ya tsawaita zamansa a Southampton

Ryan Bertrand Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ryan Bertrand ya taka rawa sosai a Southampton

Dan kwallon tawagar Ingila, Ryan Bertrand, ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da buga tamaula a Southampton zuwa shekara biyar.

Bertrand mai shekara 26, ya koma Southampton da murza-leda daga Chelsea kan kudi fan miliyan 10 a cikin watan Fabrairun shekarar 2015.

Dan kwallon ya bi sahun Virgil van Dijk da Fraser Forster da James Ward-Prowse da kuma Steven Davis a jeren wadanda suka tsawaita zamansu a Southampton.

Betrand ya buga wa tawagar Ingila wasanni guda tara, har da karawa da ya yi a gasar cin kofin nahiyar Turai da aka yi a Faransa, wadda Portugal ta lashe.