Mai Takwasara zai dambata da Shagon Tuwo

Image caption Dogo mai Takwasara zai dambata da Shagon Tuwo a gasar cin mota

Dogo Mai Takwasara na bangaren Guramada zai kara da Shagon Tuwo na Arewa a gasar damben gargajiya da ake yi a birnin Kano a ranar Talata.

‘Yan wasan biyu za su yi gumurzu ne a damben gasar da za a lashe kyautar motar hawa da aka fara tun ranar Lahadi a filin wasa na Ado Bayero Square dake birnin Kano.

Bayan nan za kuma a saka zare tsakanin Habu na Dutsen Mari Guramada da Shagon Bahagon Sarka daga Kudu.

Tun a ranar farko aka fitar da ‘yan damben Guramada hudu daga gasar, da suka hada da Shagon Shaf-Shaf da Cikan Guramda da Garkuwan Ali Fada da kuma Dogon Kyallu.

A kuma ranar Litinin aka cire ‘yan damben Kudawa uku daga wasannin da suka hada da Dan Sama’ila Shagon Alabo da Bahagon Mai Maciji da kuma Shagon Aleka.

Wadanda suka kai wasan zagayen gaba a gasar daga bangaren Kudawa da akwai Ebola da Shagon Mada.

Bahagon Sanin Kurna da Dan Inda da Dogon Bunza da Shagon Buhari da Shagon Sawun Kura ne suke tsaye a bangaren Arewa.