Ba zan yi amfani da Balotelli ba - Klopp

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Balotelli ya shafe kakar bara a matsayin aro a AC Milan

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya shaida wa Mario Balotelli cewa ya nemi wani kulob din domin ba zai yi amfani da shi ba.

Dan wasan na kasar Italiya, mai shekaru 25, ya shafe kakar bara a matsayin aro a AC Milan sai dai yanzu ya dawo Liverpool domin fara atisaye.

Tsohon dan wasan gaban na Manchester City ya zura kwallaye hudu tun lokacin da ya koma Liverpool a 2014.

"A yanzu ba zai iya fafutukar neman gurbin wasa da 'yan kwallo hudu ko biyar ba," a cewar Klopp.

A don haka muna bukatar shawo kan wannan matsalar. Akwai kungiyar da za ta iya daukarsa.

Balotelli ya zura kwallaye uku a wasanni 23 da ya bugawa Ac Milan a kakar bara, kuma ba ya cikin tawagar Italiya ta gasar cin kofin Turai da aka kammala a Faransa.