PSG ta nada Kluivert daraktan wasanninta

Patrick Kluivert Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Patrick Kluivert ya taka rawa sosai a lokacin da ya ke murza-leda

Paris St-Germain ta bai wa tsohon dan kwallon tawagar Netherlands, Patrick Kluivert aikin daraktan kwallon kafar kungiyar.

Kluivert mai shekara 40, ya ajiye aikin horar da matasan Ajax masu shekara 19, domin yin aiki tare da sabon koci Unai Emery da zai jagoranci PSG a bana.

Kluivert ya buga wa Ajax da Barcelona da kuma Newcastle tamaula, ya kuma yi aikin mataimakin kociyan tawagar Netherlands.

Tsohon dan wasan Barcelona ya ce an martaba shi da aka ba shi aiki a PSG.