West Ham za ta fara gasar Europa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption West Ham ta taka rawar gani a kakar wasannin bara

West Ham United za ta fara karawa a babbar gasa a sabon filin wasanta na Olympic a wasannin neman gurbin shiga gasar Europa League.

Kungiyar za ta fafata ne tsakanin wacce ta yi nasara da Shakhtyor Soligorsk ko kuma NK Domzale da za su buga wasan zagaye na uku a neman gurbin shiga Europa League.

Tun farko an tsara West Ham za ta buga karawar farko a ranar 28 ga watan Yuli, sai dai kungiyar ta nemi da a daga mata kafa zuwa wata ranar.

Hakan kuma ya biyon da Filin wasanta na Olympic ne zai karbi bakuncin taron wasannin motsa jiki tsakanin 22 zuwa 23 ga watan na Yuli.

West Ham ta kammala a mataki na bakwai a teburin Premier da aka kammala, ta kuma samu gurbin neman shiga gasar Europa, bayan da Manchester United wacce ta yi ta biyar a teburin ta lashe kofin FA.