Zuniga zai yi Watford wasanni aro a bana

Hakkin mallakar hoto AFP

Watford ta dauko dan wasan tawagar Colombia, Juan Camilo Zuniga, mai taka-leda a Napoli, domin ya buga mata wasanni aro a bana.

Dan kwallon mai shekara 30, ya koma Napoli a shekarar 2009 daga Siena, inda ya yi aiki tare da sabon kociyan Watford, Walter Mazzarri shekara hudu a Italiyar.

Dan kwallon shi ne na hudu da zai buga wa Watford tamaula a bana, bayan da ta sayo Christian Kabasele da Jerome Sinclair da kuma Isaac Success.

Zuniga mai tsaron baya, ya yi wa tawagar Colombia wasanni 62, ya kuma yi wa Napoli wasanni 125.