Conte yana son Cuadrago ya zauna a Chelsea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Antonio Conte ne sabon kocin Chelsea.

Sabon kocin kulob din Chelsea, Antonio Conte ya ce yana son dan wasan gefe na kulob din, Juan Cuadrago da ya cigaba da zama a kungiyar.

Tauraruwar Cuandrago, mai shekara 28, ta haskaka a gasar Serie A da kuma gasar kwallon kafa ta duniya a 2014, kafin ya koma Chelsea a kan £23.3m.

A watan Fabrairun 2015 ne dai Cuadrago ya baro Fiorentina zuwa Chelsea.

Juventus kuma ta yi aron sa a kakar wasa da ta gabata, a inda ya zura kwallaye hudu, a wasanni 28.

Conte ya ce "Ina son shi tun ina mai horas da Juventus. Zai dawo nan ba da jimawa ba don yin atasaye da kuma taka leda da mu."

Sai dai Cuadrago bai iya cin kwallo ko daya ba a wasanni 13.