Ebola ya lashe gasar dambe ta Kano

dambe
Bayanan hoto,

Ebola ya ce yana alfahari da nasarar da ya samu

Ebola ne ya zama zakara a gasar damben gargajiya ta jihar Kano ta Ganduje National Dambe Championship.

Ebola dan damben Kudu ya samu nasarar ne, bayan da ya doke Bahagon Sanin Kurna daga Arewa a turmin farko a wasan karshe da suka yi a ranar Lahadi.

Inda dan damben Arewa ne ya yi na uku, bayan da ya buge Habu Bahagon Na Dutsen Mari na Guramada a turmin farko.

Ebola wanda ya lashe gasar ya karbi motar hawa da kofi da kuma lambar zinare.

Shi kuwa Bahagon Sanin Kurna wanda ya yi na biyu a wasannin an ba shi babur da kofi da lambar azurfa.

Yayin da Inda da ya kare gasar a mataki na uku ya karbi kudi naira dubu hamsin da lambar yabo ta tagulla.

Habu na Dutsen Mari ya karbi kudi naira 20,000 bayan da ya kare gasar a matsayi na hudu.