Leicester za ta sake daukar kofi — Scemeichel

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Leicester ce ta dauki kofin Premier 2016

Golan kulob din Leicester City, Kasper Schmeichel, ya ce kungiyar tasu za ta sake daukar kofin gasar Premier, a kakar kwallon kafa mai kamawa.

Schmeichel, mai shekara 29, ya shaidawa BBC cewa "Zan ba ka tabbacin cewa har yanzu akwai kishirwar sake lashe wani kofin."

Ya kara da cewa "Ya kamata mu maimaita abin da muka yi sannan mu ga yadda za ta kaya."

Sai dai kuma wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin dan wasan kulob din na kasar Faransa, N'Golo Kante ya bar Leicester zuwa Chelsea, a kan £30m.