Le Guen yaki amsar kocin Super Eagles

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Le Guen ya horas da kungiyar wasa ta Kamaru.

Sabon kocin da hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF, ta nada ranar Litinin, Paul Le Guen, domin ya jagoranci kungiyar wasa ta kasar, Super Eagles, ya yi watsi da karbar mukamin.

Le Guen dai yaki amincewa ne sakamakon wasu sharudda guda biyu da aka gindaya masa kafin ya amince da nadin.

Sharuddan dai su ne dole sai Le Guen din ya dawo Najeriya da zama sannan kuma za a gindaya masa wasu sharuddan na tabbatar da Super Eagles ta yi nasara, a abubuwan da ta sa a gaba.

Sai dai kuma hukumar ta kwallon kafar Najeriya, ta bakin Sakatare Janar dinta, ta ce daman can ba a nada Paul Le Guen din ba, illa iyaka dai kwamitin kwararru na Hukumar ya bayar da shawara cewa a nada shi.