Stock City na zawarcin Berahino

 Saido Berahino Hakkin mallakar hoto Getty

Stock City ta taya dan wasan West Brom Saido Berahino kan kudi fam miliyan 20.

Sun ce za su bayar da fam miliyan 17 da kuma miliyan uku na talla, kan dan wasan na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekaru 21.

Yana da shekara daya ragowa a kwantiraginsa.

Kudin ya yi kusa da abinda West Brom ta sanya kan dan kwallon, mai shekara 22.

Sai dai akwai yiwuwar za a dakatar da ciniki har sai kulob din ya sayo wanda zai maye gurbinsa, inda suke neman Diafra Sakho.

Crystal Palace da Watford ma na neman daukar Berahino.

A baya West Brom ta yi watsi da yunkurin Berahino na barin kulob din domin komawa Tottenham.