Jami'in tsaro na Kano Pillars ya bar aiki

Image caption Supritendent of police Shaaibu Bello ya ajiye aikin a ranar Laraba

Babban jami'in tsaro na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars CSP Sha'aibu Bello ya ajiye aikin na sa a ranar Laraba.

Wata sanarwa da jami'in yada labarai na kungiyar Rilwanu Idris Malikawa, ya fitar, ta ce Bello ya ajiye mukamin ne saboda sauya masa wurin aikin da aka yi daga Kano zai koma Abuja.

A cikin jawabin da aka fitar CSP Bello ya gode wa mahukuntan kungiyar da magoya bayanta kan gudunmowar da suka ba shi.

Ya kuma bukaci da a bai wa wanda zai gaje shi duk wata gudunmawa da ta dace domin ciyar da kungiyar da jihar Kano gaba.

A cikin shekarar 2009 ne aka nada CSP Shu'aibu Bello a matsayin jami'in tsaro na Kano Pillars.