Ka san inda ya kamata ka zauna a jirgin sama?

Shin wasu kujerun sun fi wasu ne ta fuskar inganci?
Bayanan hoto,

Shin wasu kujerun sun fi wasu ne ta fuskar inganci?

Kujerun jiragen sama ba tun yanzu ba ne aka fara yin su.

Kujeru na farko-farko da aka fara an yi su ne da asabari, amma kuma duk wani ma' aikacin jirgin sama da ka tambaye shi zai bayyana maka cewa sun yi ta samun ƙorafe-ƙorafe game da kujerun akai-akai.

Shin wasu kujerun sun fi wasu ne ta fuskar inganci? Kuma ta ya ya zaka iya gane irin wadannan kujerun?

Kusan duk wasu bayanai da aka fitar a jiragen sama na fasinja anyi su ne da niyya.

Misali, an yi amfani da launukan shudi ko kore ne bisa la'akari da halayyar dan adam saboda an yi amannar cewa wadannan launuka sun samu karbuwa a duniya kuma suna sanya natsuwa a zukatan mutum.

Koda yake basu cika aiki ba ga wasu fasinjoji masu kazar-kazar.

"A matsayi na na ma'aikacin jirgin sama tilas in saba da jin ƙorafi na fasinjoji " ka biya kudin kujera ne amma ban da dan sararin da ke gaban kujeran ko kuma wajen ajiye kaya dake saman kujeran. "

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wasu daga cikin mu har ana bamu cin hanci na chakulan ko kuma borodi".

Fasinjoji su kan ce "zan so idan zaka samo min wata kujera mai kyau" yayin da suke miƙa maka kyauta.

Ba sabon abu ba ne jin koke-koke game da rashin jin dadi na kujera ko kuma rashin wadataccen wurin da mutum zai ajiye kafar sa da kuma yadda wasu fasinjoji ke matsawa da kujerun su baya.

Zaka yi ta jin rade radin cewa wasu kujerun sun fi wasu, amma tambayar anan ita ce, ko hakan gaskiya ne ?

Amsar dai ita ce "Gaskiya ne."

Wacce kujera ce ta fi dadin zama?

Idan ka yi sa'a a bangaren da ake biyan kudi na masu ƙaramin ƙarfi zaka samu kujera dake da sarari wajen ajiye kafafuwa ko kuma ka samu damar iya matsawa da kujerar gaba ko baya kadan ko kuma kusa da kofar fitar gaggawa daga jirgi.

Sai dai batun ba haka yake ba a bangaren kujerun alfarma wato babbar kujera ko kuma na 'yan kasuwa inda wasu jiragen ba wai kawai sun tanadi kujeru masu sarari da kuma fadi ko laushi ba kadai, akwai kujerun da fasinja kan mike har ya kwanta domin yin barci.

A bangaren masu galihu ko kuma 'yan kasuwa, babban abun da za'a iya gani shi ne kujeru da fasinja zai iya kwantawa.

Andrew Shelton, shugaba kamfanin shafin shirya tafiye-tafiye ta Internet mai suna Cheapflights ya gargadi fasinjoji da su yi taka tsan-tsan game da wasu kujerun dake gaba, kusa da kofar fitar gaggawa da kuma wadanda ke bayan jirgi wadanda basa motsawa gaba ko baya.

Galibi kujerun dake bayan jirgi an tsara su ne tare da tagogin jirgi.

Zama kusa da wurin da ake ajiye abinci da sauran abin sha a jirgi ana samun hayaniya saboda kaiwa da komawa da ma'aikatan jirgi ke yi yayin da suke rarraba abinci ga fasinjoji.

Ina ya kamata ka zauna domin samun tabbacin wurin ajiye kaya dake saman kujera?

Yayin da mai yiwuwa za ka ji gargada a lokacin da jirgin sama ke tafiya idan aka shiga wani yanayi, da kuma dogon layin fasinjoji a lokacin da ake fita daga jirgi, ba'a cika samun fasinjoji da yawa ba a kujerun dake bayan jirgi, in ji Shelton.

"A mafi yawan jirage, fasinja zai samu shiga da sauri ne idan ya zauna a baya kuma babu wahala idan kana son ka tabbatar kai ne da kanka ka dauki kayan ka".

Abubuwan da suka kamata ka yi la'akari da su yayin da kake zaben kujera ta Internet.

Ko wasu kujerun sun fi wasu ne rashin hadari?

Wani binciken ra'yoyin jama'a da mujallar Time Magazine ya gudanar game da ƙididdigar hadurran jirgin sama da suka faru tun daga shekaru 35 da suka gabata ya nuna cewa kujerun da ke tsakiya a bayan jirgi ba su cika samun matsala ba a lokacin da aka samu hadari.

Koda yake wannan ba yana nufin suna da tabbaci ba ne.

Magana ta gaskiya babu wani wurin da za'a ce ya fi wani wuri a cikin jirgi ta fuskar hana jin rauni yayin da hadari ya abku kamar yadda Alison Duquette na sashen yada labarai a hukumar da ke kula da sufurin jiragen sama ta Amurka.

"Ya ce kowane hadari ya sha banban da wani amma dai ba kasafai ake samun abkuwar hadurra jirgin sama ba."

Idan aka samun bacin rana, Chris Lopinto na kamfanin ExpertFlyer ya ce sai a duba gefen da aka samar da ƙofofin fita ta gaggawa.

"Kusancin fasinja da wajen da ƙofofin suke shi ne zai sa ka sauka da sauri daga cikin jirgi, amma kuma idan kana jerin kujerun dake ƙofar fitar gaggawa, labarin daban yake.

Tabbas zama kusa da hanyar fita ta gaggawa zai taimaki wasu fasinjoji fita cikin jirgi da sauri- amma kuma wasu dake zaune kusa da tagar kofar fitar gaggawa ana ganin suna da ƙarfi wadanda idan matuƙan jirgin suka sanar da cewa an shiga cikin wani yanayi da ake buƙatar fitar gaggawa, wadanda ke zaune a irin wuraren su ne za su taimaka wajen saukar fasinjoji daga jirgin.

Ya danganta ga irin jirgin saman, da kuma irin yanayin da aka shiga da ake buƙatar fita daga jirgin cikin gaggawa da kuma abun da ma'aikatan jirgi ke bukata, mai yiwuwa za'a bukaci wasu fasinjoji su taimaka wajen fitowa daga jirgin.

Za'a buƙaci fasinjoji da ke zaune kusa da su taimaka su bude ƙofar domin fitar da mutane ko kuma da zarar an bude ƙofar su je ƙasan jirgin su riƙa taimaka wa fasinjoji sauka suna kuma shaida musu cewa su matsa nesa da jirgin.

Ta ya ya zan iya samun kujerar da babu fasinja kusa da ita?

Galibin mutane suna sha'awar su kasance a gaba gaba, in ji Shelton.

A don haka ba abun mamaki ba ne kujerun da su ke can bayan jirgi da kuma wadanda suke tsakiya sune na ƙarshe da ake zabe.

Kujerun da ke tsakiya a can baya sune na ƙarshe da ake zabe.

Wato kenan idan zaka iya jurewa kujerun baya kuma kana tafiya ne a daidai lokacin da aka koma makaranta, za ka iya yin dacen samun kujeran da ke kusa da kai da babu kowa a kanta.

Ko zan iya kaucewa matsalar nan ta toshewar kunne?

Magana ta gaskiya ba bu wani bangare na cikin jirgi da ya kasance mai sauƙi- sauƙi ga fasinjoji dake fama da matsalar toshewar kunne idan ana magana ta fuskar ilimin kimiyya, in ji Dr Quay Snyder, shugaban cibiyar magunguna ta Aviation Medicine Advisory Service (AMAS):

"Ya ce amsar gajeruwa ce:

"Ko ina a cikin jirgi bai da bambanci idan ana batun toshewar kunne yayin tashi da sauka jirgi," in ji Dr Snyder.

Yaya batun rashin kyawun yanayi a sararin samaniya?

Kana jin lamarin ya kan yi sauƙi idan kana zaune a wasu kujerun?

Matakin farko shi ne hawa babban jirgin da ke tafiya a sama sosai.

Kuma wani labari mai dadin ji ga fasinjoji wadanda ke son kaucewa gargadar da ake ji a wasu lokuta yayin da jirgi ke tafiya a sama, shi ne zama kusa da fuka-fukan jirgin ya fi dadi fiye da kusa dakin direba ko kuma ƙarshen jirgi kamar yadda Dr Snyder ya bayyana.

Bayanan hoto,

A wasu jiragen ana fara rarraba abinci ne daga gaba

Ta ya ya zan samu kulawar ma'aikatan jirgi da sauri?

Ana fara rarraba abinci ne daga gaban wajen da matuƙan jirgi ke zaune a cewar Lopinto.

Sai dai wasu jirage su kan banbanta tsarin yadda suke aiki, kuma hakan ya danganta ne da ko jirgi na tafiya ne daga gabas zuwa yamma ko kuma arewa zuwa kudu.

Wani bangare ne babu hayaniya a cikin jirgi?

Tun kafin ka fara duba wasu abubuwa kamar ƙananan yara dake kuka, amma galibi gaban jirgi an cika hayaniya.

Koda ya ke wasu fasinjoji sun shaida min cewa sun tsani zama kusa da wurin da ake ajiye abinci da sauran abubuwa saboda za ka yi ta jin ma'aikatan jirgi suna ta surutai.

Andrew Wong na kamfanin SeatGuru ya kawo shawarar amfani da kujerun dake gaban wajen da ake ajiye kayayyakin abinci domin kaucewa jin ƙarar injinan jirgi.

A duk lokacin da ka ke son a sauya ma ka kujera to ya kamata ka riƙa murmushi kana fara'a.

Ko kujerun wasu jirage sun fi wasu araha ne?

Sayen tikitin jirgi wani babban aiki ne, domin yanayin zaben kujerun jirgi a matakin ƙaramin tikiti ya sauya a 'yan shekarun nan, in ji Andrew Shelton na kamfanin Cheapflights.

"Ya ce akasarin kamfanonin jirgi sun ƙara kudi akan kujerar da suka fi kowane, ko kuma suka ƙirƙire wasu kujerun da suka fi tsada ko kuma suka sanya su rukuni-rukuni kamar Premium Economy ko Extra Legroom.

Bugu da ƙari wasu kamfanonin jiragen suna ƙara kudi a lokacin da mutum ke neman a ajiye masa kujera.

Hakan yasa nuna takamammen kujera ke da wahalar gaske.

Abun da kawai mutum zai iya yi shi ne ya tsara tafiyar sa da wuri, muddin baya son a kai shi can baya kusa da ban daki na cikin jirgi.

Me zan iya yi domin in canza kujera kafin jirgi ya tashi?

Ga wasu matafiya da basa son zama a tsakiya, dillalai dake sayar da tikitin jirgi zasu iya taimaka musu, ko kuma suna iya yi da kansa ta Internet a daidai lokacin da aka bude fara rarraba tikitin kujeru domin ganin ko akwai wasu kujerun da ba'a riga an ba wasu fasinjoji ba.

Wata hanya kuma ita ce magana da masu aikin rarraba kujeru na jirgi ta wayar tarho ko kuma wajen sayar da tikiti, ko kuma daga ƙarshe ma'aikatan jirgi da ke nunawa fasinjoji wurin da zasu zauna suna iya sauyawa fasinja kujera kafin a gama shiga cikin jirgi.

Amma babban shawara ita ce, mutum ya riƙa mumurshi yana fara'a a duk lokacin da zai nema alfarmar a sauya masa kujera.

Bayanan hoto,

Ko kujerun wasu jirage sun fi wasu araha ne ?

Idan kana son karanta wannan labarin a harshen Ingilish latsa nan: Where should you sit on a plane?