Kekuna 10 da suka fi kyau a duniya

Kekuna 10 da suka fi kyau a duniya

An fara wallafa wannan labari ranar 17 ga watan Fabrairu 2016, amma an sake sabunta shi ranar 17 ga watan Yulin 2018.

An linka samar da kekuna a duniya har sau hudu tsakanin shekarar 1950 da 2007, kamar yadda wata kungiyar kare muhalli da ke Amurka, 'Earth Policy Institute', ta ce.

A tsakanin wannan lokacin kuma dai motocin da ake samarwa su ma an linka su sau biyu. Wannan abu ne da ya ci gaba da faruwa har zuwa yau, sakamakon tsadar mai da cunkoso a birane.

Kuma a shekara 12 da ta wuce, keke ya samu cigaban da za a iya cewa kamar tuna baya, sakamakon kayayyakin da aka samu na kera shi marassa nauyi, da dabaru na kiyaye hadari da jin dadi, da na'urar sanya wa keken ya yi tafiya kamar babu.

Sannan kuma a yanzu ana kera kekuna masu kyau. Kananan masu kamfanonin kera kekuna suna farfado da kekuna irin na da, wadanda ake ingantasu da wata sabuwar fasaha ta zamani.

Daga irin wadannan sabbin kekuna ga wasu guda goma da muke ganin sun fi kyau.

BSG Wood.b Duomatic Wannan keke ne da kanfanin BSG na Faransa ya kera da karfe da katako.

Duk da cewa da katako aka yi gundarin jikinsa, to fa yana da kwari da inganci sosai, kuma amfani da aka yi da goran ruwan da aka yi wa fenti ya sa keken ba shi da nauyi sosai (35Ibs).

Kudinsa ya kai Yuro 3190 kusan dala 4230 kwatankwacin naira miliyan daya da dubu 400 (a canjin naira na bayan fage).

Kamfanin kera kekuna na Pashley da ke Biritaniya, wanda tun zamanin Sarki Geroge na biyar na Ingila ya yi fice wajen yin kekuna na musamman, shi ne ya yi wannan laulawa (Parabike).

Wannan sabon keken ya nuna yadda kamfanin na Pashley ya nutsa cikin tarihin Biritaniya, inda ya tuno da lokacin yakin duniya na biyu, lokacin da sojin Biritaniya suka yi amfani da wani keke da suke nadewa su goya da kayansu a baya, domin shiga yankunan kasar Faransa da aka mamaye a lokacin.

Farashinsa fan 545 kusan dala 900, kwatankwacin naira dubu 288.

Kamfanin kere kekuna na Amsterdam mai suna Vanmoof, wanda ya dade kekunansa na cin kasuwa a manyan biranen duniya tun shekarar 2009, inda yake cin lambobin gasar keken da ya fi kyau, shi ne ya yi wannan keken, 'S Series', kamar yadda kirarsa ta da can take sai dai ya saukaka kayayyakinsa ba kamar yadda a wancan lokacin suke a cakude ba.

Keken yana da giya takwas wanda hakan ke sa a iya hawan tsauni ko wuri mai tudu da shi cikin sauki, kuma birkinsa kusan ya fi na wasu kekunan da suka fi shi kira da tsada aiki da kyau. Kudinsa dala 1,048, kwatankwacin naira dubu 335.

Jakin Keke

Wannan keke kirar Biritaniya ne, kuma ana masa lakabi da Jakin Keke, wanda kyawu ko kamanninsa ya saba da na keke da aka saba gani. Masu kirarsa sun fi bayar da fifiko a kan karfi da saukin kira da kuma saukin amfani da shi a birane.

Ba kamar sauran kekuna na daukar kaya ba da tsawonsu ya kai kafa takwas, wannan keke mai suna Jaki, wanda za a iya daukar kaya masu yawa a kariyarsa ta baya da ta gaba, ba shi da tsawo sosai domin ma za a iya ajiye shi a kofar gida ba tare da ya tsare hanya ba.

Kudinsa fan 499 kusan dala 830 kwatankwacin sama da naira dubu 260.

Kamfanin tufafi na Velonia da ke kasar Estonia, wanda Indrek Narusk ya kirkiro, shi ne ya yi keken wanda ya sanya wa suna Viks.

Wadanda suka yi shi suna gargadin duk wanda zai hau shi ya yi hankali da yadda zai yi amfani da birkinsa wanda aka makala a hannun keken saboda sirintakar hannun (fadin karfen hannun 30mm), amma kuma ma suna ganin abin da ya fi shi ne a guji amfani da birkin.

Farashinsa ya dogara ne da yadda mutum yake son a kera masa shi.

Wannan keken an kera shi ne a Singapore, da itacen gora da kuma zuma (zuma dai da ka sani) domin kare shi daga tsagewa.

Keken na kamfanin GreenChamp wanda aka kirkiro shi daga kudin da kungiyar Kickstarter mai bayar da tallafi ta Amurka ta bayar, an yi shi ne domin yara masu koyo. Kudinsa dala 165, kusan naira dubu 52,800.

Kamfanin da ya samar da kekuna ga 'yan wasan tseren keke na kasar Japan a gasar wasannin Olympics ta 1968, a birnin Mexici Cherubim, ya samu abin da zai yi alfahari da shi na daga irin kekunan da ya kera a baya.

A yanzu Shinichi Konno, dan mutumin da ya kirkiro kamfanin Hitoshi Konno, ya kirkiri wannan keken wanda zai zama abin da zai sa a tuno da kamfanin.

Kera HummingBird da Shinici-san ya yi ba yana nufin sake samun suna ba ne a gasar Olympics, domin ya wadatu da sunan da ya yi na kasancewa wanda ya kirkiro kekunan da suka fi kyau a duniya. Ba a bayyana farashin keken ba.

Masu kera kekuna masu amfani da batur suna kara bullowa da dabaru na ingantawa da kuma gyara fasalin kekunan, kamar yadda kamfanin Faraday da ke Oregon a Amurka, ya tsara wannan keken, ya boye batirinsa da saurin wayoyinsa a cikin jikin keken.

Keken (porteur) zai iya tafiyar kilomita 24 da batir, kuma idan rana ta fadi zai fara nuna wata alama ta fitila abin da ke nuna rana ta fadi.

Ga kuma kariya domin daukar littattafai da sauran kayan mai shi. Farashinsa dala 3,500 kusan naira miliyan daya da dubu120.

Kada ka damu da kudin wannan keken (Engeenius Cykno) wanda ya fi na sabuwar mota kirar Alfa Romeo MiTo. Babu wani abu na daban da wannan keke mai amfani da batir, dan kasar Italiya.

Duk da batiri da sauran tarin kayayyaki na aiki da lantarki da yake da su ba shi da nauyi sosai ( 57Ibs).

Ana yi masa cikakken caji a gida tsawon sa'a hudu, wanda kuma da wannan cajin za ka iya tafiya da shi hade da tukin feda har nisan kilomita 60.

Ana sayar da shi a kan farashin dala dubu 22, kwatankwacin sama da naira miliyan bakwai.

A wurin mutane da yawa da za su ga wannan keken za su dauka keke ne kamar sauran kekuna gama-gari.

Amma a wurin miliyoyin 'yan Afrika da suka dogara ga keke wajen sufurin kansu da iyalansu da kuma kayayyakinsu, Buffalo kamar yadda sunansa yake, keke ne gagara misali.

Keken wanda kungiyar bayar da agaji ta Amurka mai suna 'World Bicycle Relief' ta kirkiro shi, mutane ne da ta baiwa horo suke hada shi a wuraren da ta samar a kasashen Afrika da yawa.

Daga nan ne kuma sai a rika raba su ga kungiyoyin sa kai ko kuma a sayar wa masu bukata a nahiyar ta Afrika. Kirarsa ta yi kama da kekunan da na Biritaniya na yawan bude idanu.

Kamar dabbar da aka dauki sunanta aka sanya masa 'Buffalo' wato bauna, keken an kera shi yadda zai dace da yanayi irin na amfani a Afrika, da daukar kaya da hanyoyi marassa kyau da kuma rashin kula akai akai. Ana sayar da shi a kan dala 150 kusan naira dubu 48.

Aeolian Ride

Wannan keke Aeolian Ride wanda Jessica Findley ta kirkiro a 2004 a matsayin martanin bannar da aka samu a Lower Manhattan a 2011.

Duk yadda wani keke ya kai ga lalacewa ana ganinshi da kyau idan aka kwatanta shi da wannan keke, wanda aka yi masa wani tsari da yake kara wa kansa iska a lokacin da yake tafiya, daga iskar da ke kadawa a lokacin da yake tafiya.

Tun lokacin da aka kaddamar da shi, an yi amfani da shi a gasar wasanni a Rio de Janiero da Milan da Hong Kong da Los Angeles da kuma kananan birane irin su Halifax da Nova Scotia da Bremen da ke Jamus.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The 10 most beautiful bicycles