Yadda ake dashe a kwakwalwa domin magance shaye-shaye

Dr Rezai da tawagarsa Hakkin mallakar hoto WVU Medicine hospital
Image caption Dr Ali Rezai da tawagarsa sun yi aikin dashe a kwakwalwa a farkon watan nan

Ana yi wa mutane masu fama da matsanancin ta'ammali da kwayoyi dashe a kwakwalwarsu domin taimaka musu daina shaye-shayen, a wani mataki na gwajin maganin a Amurka.

An yi wa Gerod Buckhalter mai shekara 33 wanda ya yi fama da shan kwayoyi na fiye da shekaru goma dashen na kwakwalwa.

Ali Rezai shi ne likitan da ya jagoranci aikin dashen, ya kuma bayyana tsarin a matsayin "matakin daidaita kwakwalwa".

Sai dai ya ce ba abu ne da za a sakar wa kowa ya yi ba, domin bai kamata ya zamo wani mataki na sauya yadda aka kirkiri bil'adama ba.

Hakkin mallakar hoto WVU Medicine hospital
Image caption Gerod Buckhalter ya yi fama matsananciyar lalurar shan kwayar rage radadi bayan samun rauni a wurin buga kwallon kafa lokacin da yake da shekara 18

An yi wa Mr Buckhalter irin wannan aiki ne ranar 1 ga watan Nuwamba a asibitin West Virginia University Medicine Hospital. Kuma za a kara yin irin wannan aikin ga wasu mutanen guda uku.

Ana farawa ne da yin wasu jerin hotuna na kwakwalwa. Sannan ana fara aikin ne ta hanyar yin wani karamin rami ta cikin kokon kai, daga nan sai a zura wani siririn zaren laturoni zuwa daidai inda ake so a cikin kwakwalwa, inda ta wannan hanya ce za a iya sarrafa yadda mutum ke samun zakuwar yin wani abu, kamar son shan kwayoyi ko kuma wata dabi'a.

Akan sakala wani batiri a kasan kashin kafada, daga nan kuma sai likitocin masu ilimi kan dabi'un bil'adama da kuma likitoci gama-gari su rinka lura da yadda kwakwalwar ke aiki, domin ganin ko an samu raguwar zakuwar.

Tuni dai hukumar kula da abinci da magunguna ta Amurka ta amince da irin wannan aiki wajen yin magani ga masu fama da raunin hankali, da farfadiya, da kuma lalurar matsanancin son wani abu.

Akwai mutane kimanin 180,000 a fadin duniya da aka sakala masu wasu abubuwa a cikin kwakwalensu.

Hakkin mallakar hoto WVU Mecidine Hospital
Image caption Wannan hoton na nuna yadda aka yi dashe a cikin kwakwalwa

Wannan ne dashen kwakwalwa na farko da aka amince a yi wa masu lalurar shan kwaya, kuma ya kunshi wasu ayyuka masu wahala, wanda ya hado tawagar masana daga fannoni daban-daban, kamar masana dokokin zamantakewa, da masana tunani da ma wasu daga bangarori da dama.

Za a ci gaba da sanya ido kan wadanda aka yi wa dashen har nan da shekara biyu masu zuwa.

Dr Rezai ya shaida wa BBC cewa "Wannan wani magani ne ga wadanda sauran magungunan asibiti ko shawarwarin kwararru ba su yi masu aiki ba.

Ya yi la'akari da alkaluman da ke nuna cewa shan kwayoyi fiye da kima na daga cikin manyan dalilin da ke haifar da mutuwar mutane masu shekaru kasa da 50 a Amurka.

In da ya ce "Muna bukatar samo maslaha ga wannan matsala domin babbar barazana ce wadda kan haifar da takaici tsakanin iyali."

Hakkin mallakar hoto WVU Medicine hospital
Image caption Mr Buckhalter da iyalansa gabanin yi masa aiki

A farkon wannan shekara kungiyar masana ta UK Royal Society da ke Birtaniya ta yi gargadi game da hadarin yi wa dan'adam dashen na'ura a jiki, inda ta nuna damuwa game da shirye-shiryen wasu kamfanonin kirkire-kirkire irin su facebook da Neuralink wadanda ke son kirkirar irin wadannan na'urorin yin dashe, wadanda za su rinka sayarwa.

Tuni kamfanin Neuralink ya nemi a ba shi izinin fara gwajin irin wadannan na'urori a jikin dan'adam a kasar Amurka, inda za a rinka saka wasu na'urori cikin kwakwalen masu lalurar mutuwar barin jiki.

Yayin da shi kuma kamfanin facebook ke tallafa ma wani bincike da ake yi na kera na'urar sauraren sauti (headset) wadda za ta iya fassara abinda dan'adam ke tunani.

Dr Rezai yana tababa game da shigowar kamfanoni masu neman riba cikin irin wadannan kere-kere.

Ya ce "Ina ganin abu ne mai kyau a rinka zurfafa bincike a harkar kimiyya da ilimi. Amma a san cewa wannan ba abu ne da za a rinka amfani da shi wurin yadda aka halicci dan'adam ba, ba abu ne na kasuwanci ba."

Ya kara da cewa "Ya kamata a sanya ka'idoji masu tsauri, ba kamar yin zanen tatu (tattoo) ba ne wanda yake da sauki. Aikin tiyata yana da hadurra, ba abin wasa ne ba. Abu ne da za a tanada domin mutane wadanda ke da matsananciyar lalura, wadanda sauran magunguna suka kasa masu aiki, wadanda rayuwarsu ke cikin hadari.

Karin bayani