Dalilin da ya sa shugabannin ke bukatar ririta fargabarsu.

fargaba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Fuskokin wasu mutane

Akwai dalilai da yawa da za su sa Catherine Ulrich ta samu kwarin gwiwa game da nasarorin da ta samu a bakin aiki. A gaskiya ma ta na da cikakkiyar hujjar da za ta sakankance cewa komai na tafiya daidai wa daida.

Ulrich ita ce jami'ar samar da sababbin haja a kamfanin Shutterstock wanda ya na daya daga cikin manyan kamfanin samar da hotunan amfanin yau da kullum a fadin duniya. Sai dai kuma Ulrich ta ce a kullum ta na cikin dar-dar.

"Ba zan iya rayuwa ba fargaba ba," in ji Ulrich. "Koda yaushe na kan yi tunanin abokan huldarmu za su sami hajar da tafi ta mu a wurin wani kamfanin. Ba mamaki hakan ya sa na zama wata iri, amma dai tsoro na daga cikin abinda ya sa mu ke ci gaba da yin zarra."

Wata iri? Ba lallai ba. Kasancewa cikin fargaba, shi ne babban makamin da ya kamata ka rike idan ka zamo na daya a wani fagen sana'a ko kasuwanci. Idan ka na shugabantar kamfani, ko wani sashe a cikin kamfanin wanda ya yi abokan kasayya zarra, fargabar mai zai biyo baya na iya zaman hanya daya tak da za ta sa ka ci gaba da rike kambunka.

Fargaba na da kyau

Damuwa kan abinda zai biyo baya, shi ne abinda ke ran Brust Aust don lokacin da zai tattauna da manyan shugabannin kamfaninsu. Aust ya na da babban aiki: shi ne mataimakin shugaban NASDAQ, kasuwar hada-hadar hannayen jari mai daraja ta biyu a duniya, bayan kasuwar hada-hadar hannayen jari ta New York. Ya kan fara tattaunawar ne ta hanyar yabawa nasarorin da kamfaninsu ya samu. Daga nan kuma sai su fara tattauna abinda abokan kasayyarsu ke yi.

"Fargaba ta na da kyau," in ji Aust. "Fargaba na sa ka yi tunanin abokan kasayyarka, wannan zai sa ka kara zage damtse."

Babbar hanyar amfana da fargabar ita ce samar da sababbin dabaru, a cewar Aust. A NASDAQ, su na da wani tsari mai taken GIFT, inda daukacin ma'aikatan kamfanin 4,000 ke kawo sababbin dabarun aiki. Duk shawarar da za a kawo sai ta hada da hasashen riba da faduwa, da cikakken tsarin gudanarwa, sai a mika ta ga manyan ma'aikata da za su yi nazari a kai. Shawarwarin da aka amince da su za a zuba jari tare da ware musu lokacin gwaji.

Ba duka ne ke nasara ba, amma hakan ba matsala ba ce, in ji Aust. Yarda da cewa ba laifi ba ne don an fadi a wasu lokuta, shi ke sa sababbin shawarwari su ci gaba da fitowa. Daga cikin sababbin dabarun da su ka yi aiki har da asusun hada-hadar hannun jarin kamfanonin da ke hannun daidaikun al'umma. Aust ya ce NASDAQ na matukar samun kudi da wannan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kula da aiki abu ne mai mahimmanci

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Aust ya kara da cewa ba NASDAQ ce ta kirkiro da wannan dabarar ba. Sauran abokan kasayya na yenta. Amma wannan na daga cikin sirrin daukaka; sa ido a kan abinda abokan kasayya ke yi.

"Duk lokacin da nake ganawa da manyan shugabannin kamfani, na kan tambayesu, 'me ku ke ji abokan kasayyarmu na cewa yanzu haka a tasu ganawar?'"

A cewar Aust, "Damuwa da su shi ne zai sa su kasa wuce ka."

Rike kambunka

Daga zarar ka sanya fargaba a cikin lamarinka, sai kuma ka tabbatar dabi'ar kamfaninka ta dace da ta masu rike kambinsu, in ji Chris Edmonds, mashawarci kan tafiyar da kamfanunnuka kuma marubucin littattafai bakwai, ciki har da 'The Culture Engine'.

A mafi yawan lokuta, kananan kamfanoni ne su ka fi damar samar da sababbin hajar da za su kai kasuwa, don haka wajibi ne ga manyan kamfanoni da su samo hanyoyin da su ma ba za a bar su a baya ba.

Idan kai babban ma'aikaci ne, hanyar ita ce ka karfafi na kasa da kai. Idan kuma kai karamin ma'aikaci ne to lokaci ya yi da za ka gwada karambani.

Ka bai wa mutanen da ke da basirar kirkira damar daukar hukunci da kansu. Wannan na bukatar manajoji masu karfin halin da za su karya dokoki mara sa ma'ana domin cimma abinda aka sa gaba.

Yi da wuri

Shutterstock ya kaddamar da wata sabuwar dabara a bana, wacca aka samar ta hanyar kafa gungun mutane biyar zuwa 10 wadanda su ke zuzzurfan tunani kan bukatun abokan hulda. Sabuwar dabarar, in ji Ulrich, ita ce samar da sabuwar hanyar binciken hotuna a shafin kamfanin na intanet. Sabuwar dabarar na bai wa abokan huldar Shutterstock damar saka hotunansu a shafin sannan su bukaci kamfanin da ya nemo musu hotunan da su ka yi kama da shi. Shekara guda aka dauka daga tattaunawa shawarar zuwa aiwatar da ita, abinda Ulrich ta ce ya yi gaggawa matuka a tsarin kamfanonin fasahar zamani.

Amma fa akwai hanzari ba gudu ba, in ji Ulrich. Samar da irin wannan yanayi ya na tattare da kasancewa cikin fargaba a koda yaushe game da abinda sauran kamfanoni ke shiryawa.

"Gaba daya rayuwata babu hutu saboda kullum ina cikin damuwa," in ji Ulrich.

Sai dai kuma akwai dimbin alfanu tattare da wannan dabi'a.