Barazanar karyewar darajar kudi ga aiki a kasashen waje

Me za ka iya yi domin kare kudin shigarka?
Bayanan hoto,

Hoton wani kayataccen birni

A watan Janairun bara, an zabge albashin Rebecca Self da kaso 30 cikin dare guda.

Ba rage mata girma aka yi ba, ba kuma ma'aikatarsu ce ta kaddamar da tsarin tsuke bakin aljihu ba - karyewar darajar kudi, abinda kan yi barazana ga ma'aikata a kasashen waje da dama, ita ce ta karya darajar albashin Self.

Rebecca Self mashawarciya ce kan shugabancin kamfanoni da ke zaune a Zurich, Switzerland.

'Yar asalin Amurka ce, amma ana biyanta ne da kudaden kasashe dabam-daban - akan biya ta da dala sakamakon wani kamfani da take yi wa aiki a Qatar kuma wani kamfanin dabam da ta ke yi wa aiki a Sweden na biyanta da euro.

Ita kuma tana canja kudaden shigarta zuwa kudin franc na Switzerland.

Da yake ana biyan Self ne bisa yarjejeniyar da aka kulla tun kafin ta fara aiki, kudin da ta ke samu su na sama da kasa duk lokacin da darajar wani kudin ta karye ko ta karu.

Bayanan hoto,

Mutane da dama dake aiki a kasashen waje kan yi hada hada da takardun kudade na wasu kasashe a harkokinsu wanda ke da alfanu da kuma illa

Misali, a bara darajar franc din Switzerland ta daga.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Da ace a Switzerland kadai ta ke aiki, da kudinta zai kara daraja a kasar waje ke nan amma da yake ana biyanta da euro, sai ya zama albashinta ya ragu da kaso 30 da zarar ta canja kudin zuwa franc.

"Babu wani abu da zan iya yi akai," in ji ta.

Self na daya daga cikin mutanen da ke aiki a kasashen waje wadanda ke fama da matsalolin canjin kudi a rayuwarsu ta yau da kullum.

Mafi yawan lokuta akan biya su ne a wani kudin wata kasar, su ajiye su a samfurin kudin kasashensu, kuma su yi cefane da bukatun yau da kullum da kudin wata kasar.

Wannan matsala na zama barazana saboda karyewar darajar wani kudin a lokacin da ka ke aiki a kasar waje na iya haddasa sauyi a rayuwarka, samunka da kuma abinda ka ke iya taskacewa.

Irin haka ce ta fara a watan Yuni lokain da fam din Ingila ya karye bayan da Burtaniya ta zabi fice wa daga tarayyar Turai.

Ma'aikatan kasashen waje da yawa da kan aika da kudinsu gida sun fuskanci zabgewar albashinsu da kashi 10.

Yanzu haka ma'aikata kan yi la'akari da yadda karayar darajar kudi za ta iya shafar albashinsu kafin su amince su yi aiki a kasar waje.

Fitar Burtaniya daga tarayyar Turai ta sake karkatar da hankulan ma'aikata kan wannan barazana, a cewar Kate Fitzpatrick, wata babbar mashawarciya kan aiki a kasashen waje a kamfanin bai wa ma'aikata shawara na Mercer da ke birnin London.

Wasu kamfanonin kan yi gyaran albashi na wucin gadi idan an samu sauyin darajar kudi.

Mafi yawan manyan kamfanoni "na da tsarin tabbatar da darajar albashi ta hanyar sauya kudin da su ke biyan ma'aikata duk lokacin da darajar kudi ta karye ko ta daga da kaso 7 zuwa 12," in ji Fitzpatrick.

Bayanan hoto,

Bayan kuri'ar ficewar Burtaniya daga tarayyar turai, darajar kudin kasar ya yi faduwar da bai taba yi ba cikin shekaru 30

Nemi mafita kafin karbar aiki

Don haka masu neman aiki a kasashen waje sai su yi hattara.

Maimakon a biya su da kudin kasar da su ka je aikin, bisa tsarin albashi daidai da na 'yan kasa, Fitzpatrick na ganin zai fi kyau a yi mu su biyan rabi da rabi.

Wato a biya wani kason da kudin kasarsu ta ainihi, wani kason kuma da kudin kasar da su ke aiki.

Wani abinda ya kamata su lura da shi kuma shi ne daidaita haraji, wato kamfanin ya biya ma duk wani haraji da ya karu kan albashinka sanadiyyar aiki a kasar waje.

A binciken da kamfanin Mercer ya yi, kimanin kaso 68 na manyan ma'aikatan da ke aiki a kasashen waje ne ake biyansu bisa tsarin rabi da rabi, sai dai mafi yawan kananan ma'aikata ba sa samu wannan alfarmar.

Masu kasuwanci a kasashen waje su ma sun fara fito da dabarun da zasu kare kansu daga sauka da tashi na darajar kudaden kasashen da su ke kasuwancinsu.

Bayanan hoto,

Hada hadar kudade

Wata mai cinikin filaye ta hanyar intanet Stevie Benanty da mijinta Dan Miller za su tashi daga Faransa domin ci gaba da harkokinsu a Lisbon, babban birnin Portugal.

Su na amfani da manhajar cinikin kudaden kasashe ta intanet, Transferwise, domin biyan ma'aiktan wucin gadi da kudaden kasashe dabam-daban, abinda ke ba su damar musayar kudade bisa riba.

Da yake mijin da matar Amurkawa ne, ana biyansu ne ta hanyar aika musu da cakin kudi a bankinsu da ke New York.

Wata manhajar intanet, Earth Class Mail ce ke bude cakin kudin na su ta kuma ajiye musu dala a asusun ajiyarsu.

A lura da banki

Abu ne mai muhimmanci ga masu aiki a kasashen waje su duba yanayin samunsu, sannan su zuba jari ta yadda za su rage tasirin bambancin darajar kudi kan dukiyarsu.

Bayanan hoto,

Akwai mutane da dama da basu ji dadi ba na kuri'ar amincewa da ficewar Burtaniya daga tarayyar turai

Self ta ce ta na da asusun fansho a Switzerland da kuma wani a Amurka.

Kuma za ta ci gaba da ajiya a cikinsu har sai ta tsaida kasar da za ta yi ritaya a cikinta sai ta kwaso daga daya kasar da kadan da kadan.

Wadansu manyan bankunan na bada zabi ga mutanen da ke aiki a kasashen waje ta hanyar bada damar bude asusun ajiyar kudin kasashe biyu a tare domin amfana da bambancin darajar kudi.

Haka su kan su kamfanonin yanzu sun fara bai wa ma'aikatansu shawara kan yadda zasu alkinta kudinsu.

Misali masu biyan ma'aikata bisa tsarin rabi da rabi kan shawarci ma'aikatansu akan kaso na wa ya kamata a biya su a kudin kasashensu kuma kaso nawa ya kamata a biya su a kudin kasashen da su ke aiki.

Daga karshe dai, abu ne mai muhimmanci ma'aikata su yi nazarin yadda za'a biya su tare da shirya yadda za su yi ajiya da kuma zuba-jari, in ji Genie Martens, babbar darakta a kamfanin Air Inc, wacce ke bai wa kamfanonin kasa da kasa shawara kan tsare-tsaren kula da ma'aikata masu sauya wurin aiki daga kasa zuwa kasa.

Ta ce: "Ka yi nazari sosai game da tsarin biyan ma'aikata da ke aiki a kasashen ketare a kamfaninku domin ganin ko za ta biya maka bukatunmu da ka ke fatan cimma a rayuwarka." Idan kana son karanta labarin a harshen Ingilishi sai ka latsa nan: The financial gamble of working abroad