Ko me ya sa yawan fushi tsakanin ma’aikata ke karuwa?

Kana son lalata na'urar gurza takarda yayin da ka fusata ?
Bayanan hoto,

Kana son lalata na'urar gurza takarda yayin da ka fusata ?

Shin ko mutanen da kake aiki tare da su suna harzuka ka har ba abun da kake so illa ka yi musu ehu tare da tayar da hakarkari ?

Hakika, za ka fi samun sauki idan ka amayar da ake abunda ke cikinka, sai dai rashin boye fushin wani abu ne da ba'a cika so ba a wajen aiki.

A wasu lokuta hakan yana janyo a kore ma'aikaci daga aiki. Akasarin mu mun fi son boye fushin mu.

Sai dai da gaske fushi a wajen aiki yana ci gaba da zama abun damuwa kamar yadda masana ke cewa:

Lucy Beresford wata kwararriya ce kan halayyar Adam wacce ta yi nazari akan wannan matsala a shekarar 2007 a nahiyar turai.

Bayanan hoto,

Lalata na'urar gurza takarda a wani fim da aka yi a 1999 da 'yan wasa kamar Ron Livingston da David Herman da Ajay Naidu suka fito

A cewar Lucy Beresford, kashi 83 cikin 100 na ma'aikata sun taba ganin yadda wani abokin aikin su ya fusata a wajen aiki yayin da kashi 63 suka taba harzuka a cewar bincikenta. Wasu bincike daban daban da aka gudanar sun nuna irin wannan kiyasi.

Shin ko muna ba mutane damar su fusata a wuraren da suka dace ?

Daga cikin abubuwan da ke tada hankali a wajen aiki son hada da sukurkucewar na'urar kwamfuta, matsalar na'urar gurza takarda, fushi, abokan aiki wadanda ba su da kwazo yin aiki da kuma shugaban da bai san ya kamata ba.

Wani abun mamaki kuma shine samun wasikar email a lokacin da mutum ya tashi daga wurin aiki na janyo irin wadannan matsaloli kamar yadda wani bincike da aka gudanar a jami'ar Texas a Arlington a shekarar 2015 ya gano.

Sai dai akwai hanyoyi da suka fi dacewa don magance yanayin da mutum ya harzuka, - wato mutum ya shiga wani daki inda zai fitar da fushin sa, a wasu lokuta da taimakon karamar sanda na wasan kwallon gora.

A wurin sai ka fitar da fushinka wajen farfasa wani abu, yayin da zaka bar wani mutum ya kwashe tarkacen daka farfasa.

Rayuwar wajen aiki na ci gaba da zama abun takaici ga wasu ma'aikata da dama har ta kaiga wasu ma'aikata na ganin basu da yadda zasu yi, kamar yadda bincikenta ya gano.

Bayanan hoto,

Michael Douglas da ya fito a fim a din Falling Down a shekarar 1993

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"Ya ce muna ba mutane dama su amayar da fushin su a wani wuri da ba shi da hadari," in ji Ed Hunter, mutumin da ya kirkiro The Break Room, da aka bude a birnin Melbourne na kasar Australia, a watan Maris.

"Wannan wata hanya ce na bijirewa."

Gajiya a lokacin aiki na ci gaba da zama abun damuwa ga masu kamfanin Aussie da ma'aikatan su kamar yadda rahoton da kamfanin inshorar lafiya Medibank Private ya fitar.

Gajiya a lokacin aiki ya janyowa 'yan kasuwar Australia asarar dala biliyan $10 a shekara a cewar wani rahoto da aka fitar a 2013.

Mutane su kan yi sha'awar su farfasa na'urar gurza takarda, muna duba irin wadannan na'urori kusan 15 a kowane mako.

"An shaida mana cewa kada mu farfasa wasu abubuwa domin huce fushin mu, mu natsu in ji Stephen Shew, wanda yana cikin wadanda suka kirkiro wasannin Battle Sports a Toronto na Canada, wurin da ke da wani daki na amayar da fushi da sauran abubuwa da aka bude a watan Afrilun 2015.

"Ko kuma idan ka farfasa wasu abubuwa to tilas sai ka sayo su ka mayar'.

Amma idan a dakin huce takaici ne, za ka iya yin haka ba tare ka shiga wata matsala ba."

Huce takaici akan na'urar

Kamfanin Battle Sports ya gano cewa wasu na'urorin da ake amfani da su a wuraren aiki na jan hankulan ma'aikata.

"Mutane suna son farfasa na'urar gurza takarda. Muna duba irin wadannan na'urori kusan 15 a kowane mako, in ji Shew.

Bayanan hoto,

Ko boye fushi abu ne mai kyau?

Wuraren da suka bi sahu wajen samar da dakunan da ake huce takaici tare da farfasa abubuwa sun hada da Rage Room da ke Budapest da wasu wuraren kasuwanci a Amurka kamar Anger Room a Dallas, Texas da Tantrums LLC a Houston, Texas da kuma Smash Shack da ke Jacksonville, a North Carolina.

Kara harzuka mutum

Ko irin wadannan yanayi na fusata na taimakawa wajen kawadda gajiya? Amsar ita ce a'a.

Domin kamar zuba fetur ne akan wuta.

Harzuka ba ita ce hanyar da ta fi dacewa ba wajen magance fushi, in ji Farfesa Brad J Bushman na jami'ar jihar Ohio.

Bushman ya wallafa a wani bincike da aka gudanar a 2002 daya nuna cewa - Harzuka a matsayin wata hanya ta fitar da fushi ba ta aiki.

Domin rashin yin wani abu ya fi alfanu.

"Tamkar zuba fetur ne don kashe wuta, zai kara tada wutar ne.

Mutanen da suka fusata na shiga cikin wani yanayi da zai sa jinin su ya hau, kuma a lokacin da suke amayar da fushin su, zai sa jinin su ya ci gaba da tashi, in ji Bushman

Sai dai Bushman ya bada shawarar cewa maimakon haka, sai a yi dubara da za ta sa fushin ya fita a hankali ta hanyar kawadda hankalinka wajen yin wani abu da bashi da alaka da abun da ya saka harzuka, kamar kallon wasanni ko fina-finai da zasu sa ka dariya.

Babu magani

Hakika dakunan da ake samar wa don huce takaici mutane sun fi son yadda zasu farfasa abubuwa don huce fushi daga wurin aiki ko kuma cin amana tsakanin masoya ko kuma tsananin bacin rai.

Irin wadannan dakuna na huce takaici basa magance dukkan fushin ka.

Shew ta ce kashi 60 cikin 100 na wadanda suka fi zuwa irin wadannan dakuna na huce takaici mata ne.

Ka natsu ka ci gaba da rayuwa

Kada ka yi fushi: Mutanen da ke da sanyin rai an fi shan wahala wajen shawo kansu idan suka fusata, amma idan aka samu abinci mai gina jiki kwakwalwa tafi iya sanyaya zuciya.

Jinkiri: Ka natsu ka bari hankalinka ya kwanta, ka kirga 1- 10 kafin ka maida martani. Idan kuma ka yi matukar fusata to ka kirga 1-100!

Shakatawa: Ka huta ka ja dogon numfashi ko kuma ka saurari wakoki masu sanyaya rai.

Yi wani abu dabam: Ka tuna wani abu dabam ko kuma ka gwada yin wasannin na wasa kwakwalwa.

Idan kana son karanta wannan labarin a harshen Ingilishi latsa nan: Need to smash a printer with a baseball bat now you can