Me ke sa mutum ya ji kamar aiki ya yi masa yawa?

Oliver Burkeman, ya yi nazari akan wannan batu a shirin rediyo na BBC Radio 4
Bayanan hoto,

Da alamu kamar ayyuka suna yi mana yawa fiye da kowane lokaci, amma ba haka lamarin yake ba a koda yaushe, in ji Oliver Burkeman, wanda ya yi nazari akan wannan batu a shirin rediyo na BBC Radio 4.

Bayanai game da rayuwa a wannan zamani na nuna irin yadda kusan kowane mutum kan kasance tamkar abubuwa sun yi masa yawa.

A ƙasashen da suka ci gaba, da dama daga cikin mutanen da aka ji ra'ayoyinsu sun shaidawa masu bincike cewa ayyuka suna yi musu yawa maimakon lokacin da suke da shi ga iyalai ko kuma abokan su.

Kuma akwai yiwuwar cewa ba'a nemi jin yadda akasarin mutanen da ayyuka kan yi musu yawa suke ji ba.

Wani nazari da aka yi a shekarar 2014 ya nuna cewa, daya daga cikin muhimmin dalilin da yasa mutane ba sa son bayyana ra'ayoyinsu a binciken jin ra'ayoyin jama'a, shine suna ganin kamar abubuwa sun yi musu yawa ne.

Jonathan Gershuny, na jami'ar Oxford na ganin kusan yawan aikin da suke yi dai-dai yake da sauran.

Amma mutanen na iya yin kuskure saboda yawan lokutan da suke dauka suna yin aiki koda irin aikin da za'a biya su ne ko kuma akasin haka bai ƙaru ba a nahiyar turai ko kuma arewacin Amurka a cikin shekarun nan.

Iyaye na wannan zamani wadanda suke damuwa cewa basa samun isasshen lokaci tare da 'ya'yan su, su kan shafe lokaci mai yawa fiye da iyayen da suka gabata tare da 'ya'yan su.

"Irin yadda kanun labarai a jaridu suka sauya cikin shekaru 50 da suka gabata, sun nuna cewa mata sun fi yin ayyukan wadanda ake biyan su albashi fiye da wadanda ba'a biyansu, yayin da maza kuma suka fi yin aikin da ba'a biyansu albashi fiye da aikin da ake biyan su, in ji Jonathan Gershuny na cibiyar nazarin amfani da lokuta dake jami'ar Oxford.

"Sai dai yawan aikin kusan iri daya ne."

Bugu da ƙari, bayanai sun nuna cewa mutanen da suka ce abubuwa suna yi musu yawa, galibinsu babu wasu ayyuka da suka yi musu yawa.

Ko me ke faruwa?

Amsar dai kamar yadda masana harkokin tattalin arziki ne ke cewa; idan tattalin arziki ya bunƙasa, kuma kudaden da mafi yawan al'umma ke samu ya ƙaru sannu a hankali, hakan na nufin lokacin da mutane ke da shi da basa yin komai zai yi ƙaranci, domin kowace sa'a guda tana da matuƙar muhimmanci.

A don haka sai mutane suka zama a takure wajen neman yin wasu ƙarin ayyuka, kuma wannan shine sakamakon irin aikin da akasarin mutane ke yi.

A shekarun baya lokacin harkar noma ko kuma masana'antu suka mamaye komai da komai, ayyukan da ake amfani da ƙarfi suna da wahala.

Babu yadda za'a ce mutum zai yi girbi ba tare da amfanin gona ya gama yi ba, babu yadda zaka samu wasu kayayyaki na amfani ba tare da an samar da kayan da za'a sarrafa kayayyakin ba.

Mutum ya riƙa cewa ayyuka sun yi masa yawa tamkar wata hanya ce ta nuna matsayin sa.
Bayanan hoto,

Mutum ya riƙa cewa ayyuka sun yi masa yawa tamkar wata hanya ce ta nuna matsayin sa.

Sai dai lokacin ya wuce da ake kira "aiki da ilimi" in ji Peter Drucker.

Tony Crabbe, wanda ya wallafa littafi mai suna the book Busy: How to Thrive in a World of Too Much. Ya ce ana samun ƙarin sakonnin emails da ƙarin tarurruka da kuma abubuwan da ya kamata a karanta tare shawarwari da kan biyo baya- Kuma irin tsarin fasahar wayoyin tafi da gidanka ya bada damar duba yadda zaka tsara abubuwan da kake son yi a gida ko kuma a lokacin hutu ko kuma a wurin motsa jiki.

Sakamakon hakan shine sai ka ji kamar abubuwa sun yi maka yawa, domin hali irin na dan adam.

Saboda irin matsin lambar dake taka mana burki, ba abun mamaki ba ne yadda muke rayuwa idon mu daya na duba agogo a kowane lokaci.

Sai dai wani bincike na halayyar dan adam ya nuna cewa la'akari da lokaci kan haifar da mummunar sakamakon na aikin da mutum ke yi.

Masana tattalin arziki irin su Sendhil Mullainathan da kuma masana kimiyyar halayyar da adam Eldar Shafir sun bayyana irin wannan yanayi a matsayin matsala da kan janyo cikas wajen yanke shawara.

A duk lokacin da al'amura suka yi maka yawa, akwai yiwuwar mutum ba zai iya takaita amfani da lokacin ka ba kamar yadda ake bukata.

Bincike ya nuna cewa mutane maza sun fi yin aikin da ba'a biyan su albashi fiye da mata shekaru 50 da suka gabata
Bayanan hoto,

Bincike ya nuna cewa mutane maza sun fi yin aikin da ba'a biyan su albashi fiye da mata shekaru 50 da suka gabata

Mutum ya ji kamar aiki ya yi masa yawa, wata hanya ce ta nuna matsayin sa

Domin ganin yadda abubuwan da basu dace ba, ka duba labarin da wasu masana irin su Dan Ariely ya bayar game wani mai gyara makulli da suka taba haduwa.

A farkon rayuwar sa mutumin bai ƙware ba wajen aikin gyara mukulli idan ya kan dauki dogon lokaci kafin ya iya bude ƙofa har a wasu lokutan ma ya kan karya makullin in ji Ariely.

Amma duk da haka, mutane na farin ciki su biya bayan ya yi musu aiki har ma da yi masa ihsani.

Sannu a hankali sai ya ƙware, koda yake sun yi ta ƙorafi game yawan kudin da ya ke caji har suka daina yi masa ihsani.

Zaka za ci cewa wadannan mutanen za su fi farin cikin idan yana bude musu gida ko kuma motar su cikin gaggawa, amma abun da suke so shine mai gyara makullin ya riƙa amfani da lokacin sa koda kuwa zai dauki dogon lokaci suna jira ya kammala aikin sa.

Galibi mu kan dauki irin wannan halayya ba wai kawai na wasu mutane ba har da halayyar mu inda ba mu cika damuwa da samun sakamako mai kyau ba, har ma saboda tsawon lokacin da muka dauka muna yin wani abu.

Idan kana son karanta wannan labarin a harshen Ingilishi latsa nan: Why you feel busy all the time when you're actually not