Ko ka tsani mutane? To ga abun yi!

Domin samun nasara a duniya, mutanen da suke da zurfin ciki na amfanin da wadanan dabaru.
Bayanan hoto,

Domin samun nasara a duniya, mutanen da suke da zurfin ciki na amfanin da wadanan dabaru.

Tun kafin gari ya waye ne Josh Manheimer ya ke fara aiki kuma cikin tunani mai zurfi.

A yau ya duba irin kalmomin da suka da ce a yi amfani dasu wadanda za su zaburadda mutane su keta ambulan domin karanta wasiƙa da zarar an ajiye a kofar dakin su.

Mutane masu zurfin ciki ba su cika buƙatar a yaba musu ba domin su ƙara himma, kuma mutane ne masu matuƙar tunani a duk lokacin da suke yanke shawara.

A gidan gona dake Vermont a ƙasar Amurka, Manheimer ya rubuta abun da ya kira " tarkacen saƙonnin email".

Shi dai ya na daga cikin wadanda suka shahara a duniya, domin da zarar ka latsa kalmar "direct mail copywriter" a manhajar matan-bayi-baya-bata, zaka ga sunansa ya fito a sama.

Ya ce "wannan shine aikin daya fi dacewa da mutumin dake da zurfin ciki."

Koda yake ba wai baya yin magana bane, ya kan isar da sako ta hanyar email, domin bai taba haduwa da abokan huldarsa ba.

A kowane lokaci yafi son ya fita waje yana riƙa tafiya tare da karensa ko kuma ya riƙa ba dawakai abinci.

" Ya ce ina jin kaina tamkar diyar barewa ce da ta bace a dokar daji"

Bayanan hoto,

Gilibin masu zurfin ciki sun fi maida hankali kan abubuwa kuma mutane ne masu matuƙar tunani wajen yanke shawara

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Gwagwarmayar sa ta yi kama da ta mutanen dake da zurfin ciki wadanda kusan sune rabin al'umma.

Ba sa jin kunya, amma sun fi son yanayin da babu wata hayaniya domin su yi tunani mai zurfi.

Kuma wannan ba yana nufin masu zurfin ciki basa samun ci gaba a rayuwar su ba ne, muhimmin abu ga kowa shine ya samu aiki da ya dace da shi.

Akasarin al'umma na da wata dabi'a data yi kama da ta masu zurfin ciki.

Bamu cika sakin jiki ba a kowane yanayi, a wasu lokuta mun fi son mu yi tunani mai zurfi ba tare da wasu mutane sun dame mu ba, bamu cika son fadin abun daya shafe mu ga kowa da kowa ba domin mun fi son mu zauna na wani lokaci mu kadai ba tare da wani mutum ba.

Sai dai mutanen dake da zurfin ciki alal misali, basu cika son a yaba musu ba domin su ƙara himma, su mutane ne masu matukar tunani wajen yanke shawara, kuma wannan wata dabi'a ce mai muhimmanci ga kowane irin aiki.

Tushen al'amari

Wasu dai kan yi kicibis da irin aikin da ya dace da su ne.

Michael Motylinski lauya ne dake California, Ya ce- "ina aikin dana tsana a rayuwa ta- akai-akai zaka riƙa mu'amala da mutane."

Bayanan hoto,

Michael Motylinski ya koma tsibirin Virgin Islands domin yin aikin sa na lauya - kuma yanzu kulla aure tsakanin ma'aurata fiye da 250 a shekara guda

Motylinski ya sauya aiki ne bayan da dan uwansa ya nemi da zama wakili a lokacin daura aurensa.

A don haka ya yi kwas ta Internet akan yadda mutum zai zama wakili ko shaida a wajen daura aure.

Daga bisani dai ya koma tsibirin Virgin Islands domin ci gaba da aiki a matsayin lauya.

"Ya ce an sha tambaya ta ko na san wani dake zama wakilin don kulla aure, sai in ce musu ai tuni na samu lasisi zama wakili, daga nan ne fa sai na riƙa samu kiran waya akai-akai daga masu shirya bukin aure, da masu wuraren shakatawa a gabar teku."

Kuma duk da cewa ana bukatar ya tsaya a gaban jama'a, yanzu ya zama wakili wajen daura auren fiye da ma'aurata 250 a shekara guda.

'Ya ce irin wannan aikin ya fi dacewa da mutum mai zurfin ciki".

"A ranar daura auren, hankulan jama'a su kan karkata ga abubuwa masu yawa ta yadda babu ma wanda ke lura dani"

Ya ƙara da cewa "ina tsayawa ne a gaban taro in karanta wasu kalmomi dana tsara, kuma daga bisani bayan an kammala komai sai in sulale in fita ta kofar dake baya ba tare da wani ya lura da ni ba."

Motylinski dai ya auri wata budurwa dake tsibirin kuma suna da 'ya'ya biyu kuma a halin yanzu matar sa tana da juna biyu.

Wasu dabi'u dabam

Zai iya kasancewa mutumin dake kallon kansa a matsayin mai zurfin ciki ya sauya aikin da yake yi gaba daya.

Wani matashi mai suna Dan Nainan yanzu ya samu abun yi ne ta hanyar yin barkwanci a gaban dubban jama'a, amma da farko ya fara aiki ne a matsayin injiniya a Silicon Valley.

Aikin da yake yi ya hada da nunawa jama'a a zauren taro yadda zasu yi amfani da kayayyaki kamfanin.

Yana matukar ƙaunar tafiye-tafiye da yake yi zuwa ƙasashe kuma bai cika son yin bayani ba a bainar jama'a.

Ya dauki wasu matakai domin kawadda fargabar da yake fuskanta wajen yin magana a gaban jama'a, inda ya yi karamin kwas tare da mai wasan kwaikwayon nan Judy Carter.

Nainan ya ce ya tuna cewa lokacin da ya yi matukar kokari inda har ya riƙa nunawa abokan aikin sa faifen bidiyon kuma daga nan ne aka buƙaci ya bayyana a gaban wani taro a Las Vegas da mutane kusan 250 suka halarta."

Bayanan hoto,

Dan Nainan kenan a karon sa na uku da yake tsayawa gaban jama'a su kimanin 2,500 a wani taro na sayar da kayayyaki

A yanzu dai yana zaune ne a birnin New York inda yake samun abun hannu a matsayinsa na mai yin barkwanci.

Ya bayyana irin yadda canjin aiki daga matsayin injiniya zuwa mai barkwanci ya sauya rayuwar sa ta aiki da kuma yadda mutane ke kallon sa.

Daukar darussa a fanni wasanni ko kuma iya yin jawabi a bainar jama'a abu ne da ake bada shawarar yi a matsayin wata hanya ta shawo kan faduwar gaba da jin kunya a lokacin aiki.

Gregory Pontrelli, shugaban kamfanin Lausanne Business Solutions na ganin akwai bukatar kada a riƙa kuskuren fassara hakan a matsayin mutane masu zurfin ciki.

"mutum zai iya kasance wanda ba shi da tsoro amma kuma yana jin kunya ko kuma yana fama da faduwar gaba" in ji shi.

Bayanan hoto,

Mutane ka iya kasancewa wadanda ba su da zurfin ciki amma kuma suna jin kunya ko kuma fama da faduwar gaba.

Pontrelli ya kuma ƙalubalanci wata sana'a da ake ganin ta fi dacewa ga masu zurfin ciki- domin ko a sauran sana'o'i da ake ganin basu da ce ba da masu zurfin ciki kamar tallar kayayyaki, ana bukatar dabaru a bangaren.

" Ya kara da cewa wasu kamfanoni kan yi kuskure tantance masu neman aiki ta hanyar yin jarrabawa, amma kamata ya yi masu daukar aiki su amince da banbance-banbancen dake tsakanin al'umma domin ta haka ne za'a iya yanke shawarar data dace wajen fahimtar abokan ciniki.

Yin and yang

Irin banbance banbancen dake tsakanin al'umma za'a iya ganin su a gidauniyar da wasu fitattun kamfanoni suka kafa, misali Steve Wozniak mutumin da tare da shi ne aka kirkiro kamfanin Apple ya hadu da wani mutumin da ba shi da zurfin ciki wato Steve Jobs.

Shi ma Bill Gates ya yi irin wannan a kamfanin Microsoft tare da Paul Allen daga bisani kuma da Steve Ballmer.

Ya yin da a Facebook kuma akwai Mark Zuckerberg da Sheryl Sandberg.

Bayanan hoto,

Bill Gates tare da Steve Ballmer a 1998

Wannan dai wata dubara ce da Deidre Woollard ta aiwatar.

A kamfanin Audie Chamberlain ta samu wani abokin hulda wanda halin su ba iri daya ba.

Ta ce ina matukar ƙaunar mutanen da ba su da zurfin ciki, koda yake bana tunanin duk mutanen da suke da zurfin ciki za su amince da ni, domin ni a ganina, suna zama a matsayin garkuwa ne ga al'umma.

Nainan ya ce yana fuskantar matsala wajen dangartakar sa da mutane.

"Ya ce ina matukar samun matsala wajen yin magana da mata fiye da tsayawa gaban mutane 2,000 domin nishadantar da su.

Bayanan hoto,

Josh Manheimer ya fi son ya fita ya ba dawakai abinci fiye da ganawa da abokan ciniki

Wasu mutane da dama dai da ke da zurfin ciki daga bisani su kan sauya aiki da kuma basirar su wajen dangartakar su .

Misali, marubuci Manheimer sun hadu da matar sa Renee ta hanyar shafin Internet.

Tana aikin samar da kayayyakin kwalliya inda take zaune a Peru kuma ba ta jin turanci ya yinda shi kuma bai jin harshen Spaniya.

Hakan ya nuna tasirin sakonnin sa na emails bayan manhaja ta fassara sakonnin, ya yi nasarar shawo kanta domin ta bar inda take a Lima, ta zo ta zauna da shi a gidansa na gona.

"Ya ce ba ta taba sanin ina Vermont ya ke ba, ga shi tana bukatar kayan sanyi, amma kuma bayan wata biyar sai muka yi aure a asirci."

Idan kana son karanta wannan labarin a harshen Ingilishi latsa nan: hate people here are the jobs for you