Yadda dabi’ar ka ta fargaba ke shafar jarrabawar neman aiki

Ko ka san cewa dabi'ar ka ta fargaba na iya shafar jarrabawar neman aikin da ka ke yi ?
Bayanan hoto,

Ko ka san cewa dabi'ar ka ta fargaba na iya shafar jarrabawar neman aikin da ka ke yi ?

Idan ana magana akan batun jarrabawar neman aiki, za'a iya cewa mutum na da gaskiya idan ya dauka cewa irin yadda ya tsara takardar bayanan ilimi da ayyukan da ya yi ko yake yi da kuma yadda ya gabatar da kansa, kuma musamman yadda ya amsa tambayoyin da aka yi masa, zai iya sa ya samu aikin da ya ke nema.

Sai dai kuma dabi'ar mutum ka iya janyo masa cikas.

Domin dabi'un mutum za su iya bayyana ko shi wani irin mutum ne koda kuwa baya son wadannan dabi'un- wato kodai masu kyau ne ko kuma marasa kyau.

Kuma a mafi yawan lokuta ba mu cika sanin muna irin wadannan dabi'un ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ajiye ƙafafuwa a karkace zai iya sa a riƙa kallon mutum a matsayin wanda ke cikin zullumi

Mai yiyuwa mutum yana sane ko kuma ba tare da saninsa ba, yawan goge idanuwa, ko matse 'yan yatsun hannu ko kuma taba gashin kai zai iya sauya tunanin mai gudanar da jarrabawar daukar aiki fiye da yadda kake tunani.

Kamar yadda Isabel Schuermann, wani mai horas da ma'aikata kan kyawawan dabi'un aiki dake kusa da Frankfurt ke cewa.

"Tilas jikinka ya riƙa aikewa da saƙo".

Misali rashin hada ido zai iya aikewa da saƙon cewa mutum ba shi da gaskiya, ko kuma ajiye ƙafafuwa a karkace zai iya sa a riƙa kallon mutum a matsayin wanda ke cikin zullumi.

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Masu yin jarrabarar daukar aiki suna tantance gaskiya da kuma ilimi ta hanyar kallon ƙwayar idon mutum

Sai dai wani labari mai dadin ji anan shi ne, mutum zai iya magance wasu dabi'unsa marasa kyau, kuma matakin farko shine sanin irin wadannan dabi'un.

Amma wani gargadi shi ne yana da wahala a magance irin wadannan dabi'u idan mutum yana cikin zullumi.

Amma ga wasu abubuwan da ya kamaya mutum ya yi.

Ka fuskanci matsalar ka

Matuƙar ka amince da irin dabi'un ka, to lokaci ya yi da zaka magance su.

Ka riƙa sa kanka a matsayin wanda ke yiwa wani jarrabawa har sai ka shawo kan wadannan dabi'u.

Misali, kana iya rage yawan matse 'yan yatsun ka ko kuma kallon ƙasa a duk lokacin da kake magana da wani.

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Alamy

Daniela Lehmann-Stein, wacce ta jagoranci wata tawaga ta masu kula da ma'aikata a Nielsen dake Frankfurt, ta ce ya yin da take samun horo kan dubarun yadda za'a riƙa yiwa masu neman aiki jarrabawa, ta rubuta a takarda jerin abubuwan da ta saba yi ba tare da saninta ba, wanda kuma take son ta daina, misali ta rubuta cewa bata son yin wani abu da zai dauke mata hankali.

A maimakon hakan, Lehmann-Stein, wacce ita ce ke daukar hayan mutane aiki a shekaru 17 da take aiki a ɓangaren kula da ma'aikata a wani katafaren kamfani na son ta san wanda ke neman aiki idan ta ga yadda mutum ya yi wani abu ko kuma wani abu ya dauke mishi hankali.

Tantancewa ta na da matukar muhimmanci.

"Tantancewa ta na da matukar muhimmanci, saboda idan mutum ya bayyana kansa a matsayin wanda ba shi da zurfin ciki, kuma a bangare guda, aka ga ya ware kansa ya zaune gefe guda shi kadai, wannan zai janyo ta-ba-ba game da iƙirarin sa- a cewar ta".

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Alamy

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wata hanya kuma ta magance wata dabi'ar ita ce maida yanayin tamkar abun dariya.

Lehmann-Stein ta ce zan so a ce kowane mutum mai jarrabawar neman aiki zai riƙa nuna gaskiyar dabi'ar sa tare da ƙarin kwarjini ta wannan fuska.

"wannan bai bukatar wani mataki na mutum ya sake nazarin kansa domin ya fito da kansa- misali idan mutum ya san cewa mai yiwuwa zai yi ta goge idanuwa na, to zai iya yin hakan ta hanyar da zai bada dariya ."

Me ya ke sa mu ke yi ne?

Yanayi na rashin natsuwa yana da asali a halayyar dan adam, in ji Burch

Idan zaka gano dalilan zaka iya magance dabi'un da ka ke yi da ba su da ce ba.

Alal misali, Burch ya ce a wasu lokuta dalilan su ne fargaba saboda rashin shiryawa.

Ta ƙara da cewa ta ga yadda wasu mutane suka shawo kan wannan dabi'a ta hanyar kintsawa sosai a lokacin yin jarrabawar daukar aiki.

Daukacin abunda ya ƙunsa

Idan ka yi sa'a zaka iya samun mai yin jarrabawar daukar aiki kamar Schuermann, wanda sai ya kalli mai neman aiki daga sama har ƙasa.

"Kada ka taba fassara kallo daya kawai, kana bukatar hanyoyi hudu zuwa biyar kafin ka iya fassara ko wane irin mutum ne, " in ji Schuermann.

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Masu jarrabawar daukar aiki su kan kalli mutum daga sama har ƙasa

A ƙarshe dai shawarar a dauki mutum aiki sun danganta ne akan wasu dalilai da dama.

Schuermann ta ce idan ta tuna zamanin da take aiki a sashen kula da daukar ma'aikata a bankin Deutsche da ke Frankfurt, "wadanda ke dacen samun aiki ba wai kawai suna da ilimi ba kadai ta fuskar bangaren da suka ƙware, har ma suna da tarbiya, kuma sun iya magana tare da fahimtar yadda za su yi mu'amala da jama'a cikin yanayi na kwarjini."

Idan kana son karanta wannan labarin a harshen Ingilishi latsa nan: Are nervous ticks derailing your job interview