Yanayin da arziƙi kan zama tsiya!

A lokacin da ka saye gidan da ka ke ƙauna amma sai ya kasance yana cike da matsaloli
Bayanan hoto,

A lokacin da ka saye gidan da ka ke ƙauna amma sai ya kasance yana cike da matsaloli, ko me ya kamata ka yi bayan da ka saye abun da ya zame maka ala-ƙa-ƙai?

Yayin da a karon farko Sherilyn Faluta ta sayi gidanta a watan Yulin wannan shekarar, ba ta taba zaton cewa cikin watanni biyu za ta kashe makuden kudade ba wajen gyara gidan.

Koda yake ta duba gidan kafin ta saya, amma babu wanda ya gano cewa akwai matsalar aikin famfo da ta haddasa lalacewar daukacin gidan tare da na'urorin da ke sa sanyi da kuma zafi a cikin gidan.

Gwaji tare da gyara gidan yana da matukar tsada, kuma ana buƙatar a sake yin daɓen ƙasa a dakin dafa abinci da kuma wurin da ake yin wanki saboda katakon duk sun ruɓe.

Kuma gyara wadannan wuraren zai laƙume dala dubu tatalin kafin gida ya koma yadda ake buƙata.

Babban abun takaicin shine yadda lalacewar sabon gidan ya sa Faluta ta fara rashin lafiya, kuma tilas ta fita daga cikin gidan kafin a iya yin aikin gyara gidan.

"Zai laƙume dala dubu tatalin kafin gida ya koma yadda ake buƙata," in ji Faluta, mai shekaru 40, wacce ke zaune a North Carolina a Amurka.

Ta riga ta kashe kusan dala dubu goma wajen yin gyara a gidan ba ya ga kudin da take kashewa a Otel da ta kiyasta cewa tana kashe dala $1,600 a duk wata guda.

Matuƙar gidan da mutum ya saya yana da matsala, zai iya daukar mutum har tsawon rayuwar sa wajen gyara wa.

Kuma wannan wani abu ne da baka taɓa zato ba.

"Na koma gida na a shekarar 2003, kuma sai bayan da na shafe wasu shekaru ne a gidan na gano cewa ina zaune ne a wani tsohon mahaƙar ma'adinai na kwal," in ji Virginia Nolan, wacce ke zaune a birnin Michigan na Amurka.

Tuni dai ta gyara matsalar tsagewar bango da kuma daɓen ƙasa tare da matsalar ruwa a gidan.

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Matsalar fanfo da ba'a gano ta ba tana iya haddasa babbar matsala

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kudaden da ake kashe wa wajen gyara gida suna iya ƙaruwa cikin gaggawa.

Domin a Amurka fiye da rabin mutanen dake da muhallin kansu sun fuskanci matsalar da ake buƙarar gyara cikin gaggawa a shekarar data gabata, kamar yadda wani binciken jin ra'ayoyin jama'a da kamfanin dake gyara gidaje na HomeServe dake Amurka ya gudanar.

A Burtaniya, kashi 5 cikin 100 na kudaden masu gidaje na tafiya ne wajen gyara gidaje a cewar hukumar ƙidaddiga ta kasar.

A wasu lokuta matsalolin da su ke ɓoye suna iya zama babbar matsala ta ƙasa baki daya— Misali a New Zealand, wani rahoto na kamfanin Price water house Coopers ya ce an kashe kimanin dala biliyan goma sha daya da miliyan dari uku wajen gyara aikin kafinta na rufin gidaje har 89,000 tun daga shekarar 1994 zuwa 2004.

A Canada kuma sai da aka yi ta gyara matsalar yoyon ruwa a dubun-dubatan manyan gidaje na bene irin gidajen da al'ummomin Burtaniya da Columbia ke ginawa.

Idan aka sayar ma ka da madaci maimakon zuma, me ya kamata ka yi ?

Akasarin mutanen da suka tsinci kansu a irin wannan yanayi kan dora alhakin hakan ne a wuyan wasu mutane, wanda hakan ke nufin shigar da ƙarar wasu da suke da hannu a lamarin.

Sai dai kafin ka dauki matakin zuwa gaban ƙuliya domin neman haƙƙin ka, akwai wasu abubuwa daya kamata ka yi la'akari da su:

Akwai hujjar da za ka gabatar: Kana bukatar kafa hujja da dokoki saboda akwai yiwuwar zaka yi ta neman wanda zai dauki alhakin matsalar — misali, wanda ya duba maka gidan, ko kuma kamfanin inshora na ainihin mai gidan, ko kuma tsohon mai gidan da sauran su.

Mai yiwuwa sai dai daga bisani ka shigar da ƙara kuma akwai yiwuwar kudaden ka su ƙare wajen dawainiya wanda kuma ya danganta ne ga yanayin.

Duk wani abu da baka san shi ba, to baka san shi, kuma babu yadda za'a yi ka nemi abun da baka sani ba.

Tsawon lokacin shiryawa: Kafin ka sa yi muhalli, ya kamata ka samu ƙwararru su duba maka da kyau, mai yiwuwa ko ƙwararre da yake da takardar shaida, ko dan kwangila, ko kuma wasu ƙwararru kamar masu gyara fanfo da wutan lantarki domin su tantance maka yanayin aikin da aka yi a gidan, in ji Timothy Frie, wani dillalin gidaje dake Florida.

"Ya ce abun da baka san shi ba, to baka san shi, kuma babu yadda za'a yi ka nemi abun da baka sani ba."

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Tun kafin ka kammala ciniki, yana da kyau ka kira ƙwararru su duba maka

Galibi wannan yana faruwa ne watanni kafin kammala cinikin gidan, amma kuma sanya wani ƙwararre cikin harkar shine yafi dacewa.

A kwangilolin da aka bayar na wasu gidaje akan ware wasu kudade na ko-ta-kwana, wanda yake ba mai sayen gidan damar fita a ciniki matuƙar binciken gidan ya gano wasu manyan matsaloli.

"Kafin ka sanya hannu a yarjejeniyar sayen gida, ka nemi shaida game da lokacin ƙarshe da aka duba abubuwan dafa ruwan zafi da tagogi da wutar lantarki da aikin fanfo da kuma rufin gidan, kuma ka tabbatar akwai takardun iznin yin gidan," in ji Hannah Maundrell, Editan shafin kasuwanci ta Internet dake Burtaniya wato money.co.uk.

Domin tabbatar da cewa babu abun da baka gane ba, ka duba yiwuwar sayen gidan da ke da inshora da kuma kariya daga kashe kudade ta fuskar shari'a.

" Wannan zai taimaka idan aka gano wata matsala bayan kammala ciniki, saboda mai sayen gidan na iya samun kariya ta fuskar kashe wasu kudade na neman masu biyan tara saboda sakaci," a cewar Lorna Munro, wata lauya a ofishin lauyoyin na Blake Morgan a Burtaniya.

Ka yi yanzu: Ta tanadi takardun komai da komai. Ka dauki hotunan matsaloli daya bayan daya tare da bayaninsu da kuma aikin da ake bukatar yi domin gyara matsalolin.

Wadannan sun hada da jerin aikin gini da kayayyakin aikin da ake buƙata da na'rori da kuma kudin da za'a biya ma'aikatan da su ka yi gyaran.

Ka duba dokoki: Matuƙar ka yi amannar cewa mai gidan ya yi ƙoƙarin wajen ɓoye maka wasu matsalolin dake gidan, kana da hujjar daukar matakin shari'a.

A wasu wuraren ana bukatar duk wani mai gida ya bayyana duk wani abun da ya sani game da gidan da ka iya rage darajar sa, in ji Frie.

Amma yanayin abubuwan da ake bukata su kan sha ban-ban daga wannan yankin zuwa wancan.

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Mai bincike gida zai iya gano wata matsala da za ta laƙume makuden kudaden a gidan da ka ke matuƙar ƙauna

Ka kira dillali mai kula da gidan ka. Dillalin da ke kula da gida ta wajen shi ya kamata ka fara saboda da hannun sa wajen sayen gidan.

Dillali mai mutunci kan iya duba matsala tare da bada shawarar da ta dace a cewar Michael McGrew, wani dillali dake birnin Kansas.

Sake duba mai binciken ka. Shin ko wanda ya bincika maka gidan ya duba komai da komai da yanzu kuma aka gano wasu matsaloli?

Idan babu wani abu da a lokacin da me binciken ya gano cewa ba su yi daidai ba, za'a iya cewa matsala ce da ba'a ganta ba.

Sherilyn Faluta ta ce ta shafe makwanni tana rashin lafiya, ba ta iya zuwa aiki, wannan matsala ta shafi dan kudin da take da shi.

Kira kamfanin inshorar ka. Kamfanin inshorar aihinin mai gidan da ka saya za su iya magance wasu matsalolin.

Misali, matsalar da Faluta ta shiga, kamfanin inshorar ta sun gyara mata matsala guda daya tal, wato gyara ban daki daya laƙume dala dubu biyu da dari shida, kuma an ce "da babu gara ba dadi".

Duba takardar cinikin ka: mai yiwuwa kana da wata dama ta samun sauƙi da zata sa ka bi hanyar gyara kafin ka dauki matakin zuwa gaban ƙuliya. Sasantawa wata hance ta magance matsala cikin sauki in ji McGrew.

Ka yi amfani da basira: Zuwa gaban kuliya shine matakin ƙarshe, domin idan ba za ka samu abun da ka ke bukata ba bayan ka tuntubi duk wadanda lamarin ya shafa, daga nan ne zaka yi tunanin garzaya wa kotu.

Idan kana son karanta wannan labarin a harshen Ingilishi latsa nan: When a dream home becomes a disaster