Yadda za a kauce wa rubuta mummunan sakon imel

email Hakkin mallakar hoto Getty Images

Daga Alina Dizik

5 ga Satumbar 2017

A makonni kadan da suka gabata, ya haifar da rudani a lokacin da ta aike da sakon Twitter, ta zabi yin amfani da cin zarafin wani cikin ruwan sanyi don kaskantar da shi a wajen aiki ta hanyar -i-mail: ta hanyar amfani da jimla sassauka "dangane da sakon i-mail dina da ya gabata."

Tattare da dukunkunannen sakon cin mutunci, marubuciya , kuma mai talllata haja da ke birnin Washington DC ta umarci wadanda ke tare da ita ( a shafin sadarwa) da su baza sakonninsu.

Sakamakon dai ya zama mabudi, inda sakon ya bazu a tsakanin daruruwan mutane, wadan suka yi ta yada wannnan sako marasa cutarwa a sakonnin i-mail din in an kwata furta shi da ce-ce-ku-cen baka a dukunkune.

Sai dai, muna tura munanan kalamai a sakonnin i-mail dinmu cikin rashin sani.

Sakon i-mail wajen dasa bama-bamai (tayar da hankali) ne, saboda ba ka san yadda mutane za su mayar da martani ba.

Idan ka aike da sakon i-mail da kyajkkyawar manufa har ya haifar da mummunan martini, kana iya zama abin zargi kan kuskuren da kee bayyane karara.

Tun daga kan "kamar yadda ka sani" zuwa "a taimake ni da shawara, dimbin martini shafin twitter na nuni da cewa musayar sakonnin i-mail sun zama takaddamar ce-ce-ku-cen zamantakewa, inda amfani da munnunar kalma bisa kuskure a lokacin da bai dace ba, cikin suaki zai iya harzukawa ko fusata mutane.

Bibiyar rubutu na wani lokaci

Daukacinmu muna isar da ma'ana ta kai tsaye, sabanin kimar kalmomi da yanayin furucinsu tare da manufar sakon i-mail dinmu.

Hatta tsawon rubutun i-mail da nahamunmu (ko rashin kimanta matsayin kalmomi) na nuni da wani abu kan tsarin tunaninmu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Sai dai lamarrin na da wahala a gano yadda yadda muka tarkato su zuwa ga wasu.

A kai-a kai mukan latsa maballin aikewar sako (send) ba tare da dan dakatawa mun yi has ashen yadda za fasssara sakon a wajen wanda ya isa gare shi/ita.

Ba mu cika tambayar kanmu ba: na yi bayani karara, ko ba za a fahimce ni ba?

"Mun natsu da cewa a irin wannan kafar (aikewa da sako) ba ma bnukatar tuhumar kanmu: shin na yi bayani karara?

Ko za a yi mini mummunar fahimta?" a cewar Naomi Baron, Farfesar nazarin harsuna a Jami'ar Amurka ta Washington DC , kuma mrubuciyar kalmomin allon kallo (Words on the Screen): makomar karatu a duniyar kwamfuta.

Bayan an aike da sako, ta kara da cewa, "mutane da dama za su yi maka hukunci (kan manufa ko ma'ana)."

Tabbatar da gaskiyar lamari

A 'yan shekarun nan, i-mail na kara zama hanyar sadarwa mafgi inganci, musamman saboda kafar isar da sako a kan kari kamar 'Slack.'

Matasan ma'aikata yanzu suna da tabbacin cewa "i-mail ta tsofaffin mutane ce," a cewar Baron. "Irin wannan dabi'a tna sauya kasurar nagartar yadda i-mail ta zama," in ji ta.

Sai dai kauce wa tsarin al'ada na rubuta jimlolin sakon i-mail da aka saba da shi zai nuna cewa kana da karancin ilimi, a cewar Madhumita Lahiri, Farfesan Ingilishi sa Jami'ar Michigan da ke Ann Arbor, wanda ya yi aiki a Indiya da Afirka ta Kudu da Birtaniya kafin ya koma Amurka da zama.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Don kauce wa zama mutumin da koma-bya, kalmomin irin su "zuwa ga" ko "ina fatan kana/kina cikin koshin lafiya" na da kyau a fara sakon i-mail da sulkdon taimaka wa mai karu ya samu saukin fahimtar abin da kake rubuto masa, a cewar Lahiri.

"Akwai hanya mafi dacewa wajen farawa da karkarewa da ke nuni da cewa ka san abin da kake yi."

Kauce wa nuna rauni

Ko da yake kana son nuna kwarewa wajeen amfani da i-mail, al'amarin d ake nuna kimar mutuntakarka da haskaka kyakkyawar manufarka, a cewar Alex Moore, abokin hadin gwiwar turakar inganta ayyukan i-mail na Bloomerang a San Francisco.

Matasan ma'aikata suna da tabbacin cewa sakon i-mail na tsofaffin mutane ne.'

Kamar yaddda yake kunshe a binciken Booomerang na shekarar 2016 dangane da kamala i-mail, inda aka tattara bayanai kan sakonni 350,00, daukacin wadanda suka kasance managartan sakonni da munana, an gano cewa an samu martini da ya hauhawa kan sakonnin i-mail din da kashi 10 zuwa 15 cikin 100 wadanda suka fi zama tsakatsaki ('yan ba ruwanmu).

"Ba ka son tsananta zama mai kyakkayawan sako ko mafi munin sako, amma dai mutane za su mayar da martani da abin da cikin zukatansu a rubuce," inji Moore

A yi cikin sauki

A cewar binciken Boomerang, sakon i-mail da aka yi cikin sassaukan kalamai yana samun kyakkyawar amsa.

Binciken da kamfanin ya gudanar ya bayyana cewa i-mail din da aka rubuta a daga mai karatu a matakin aji na uku yana samun martini da kashi 53 cikin 100 in an kwatanta da kashi 39 cikin 100 na mai rubutun da yake a matakin karatun jami'a, da kashi 46 cikin 100 na matakin share fagen koyon karatu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ci gaba da amfani da sassaukan kalamai zai taimaka wajen kauce wa mummunar fahimta da aka dora a ma'aunin al'ada.

Za ka dauka cewa kana kyautatawa da sarkakiyyar kalamanta, amma a hakikanin gaskiya ka karke da nuna wasu kalamai da ba ssu dace ba, a wajen wani sashe na wannan duniya, kamar yadda Lahiri ya yi gargadi.

A Birtaniya, ta ce, rubuta cewa "abin takaicin shi ne…" ko "na yi nadamar.." an daukesu kalaman mutuntawa da kyautatawa, amma za su iya harzuka masu karatu a wani wurrin daban.

Alal misali a Amurka, "Lamari ne mafi sauki a yi dimbin godiya," inji ta. "kalamai irin su 'ina tsoron' za su iya zama manuniyar mummunan tunani sabanin kyautatawar a Amurka kawai."

A lura da kyau kan sarkakiyar alamomin rubutu

Ra'ayoyi sun bambanta in an yi la'akari wajen sanya alamar motsin rai da digge-dige da manyan bakake, da kuma abin da amfani da su ke nuni da shi ga wanda aka aika wa a sakon i-mail.

Yayin d amatasa ke zafafga kalaman sakonnin i-mail dinsu da alamomin motsin rai don nuna nagartar abota, tsofaffin ma'aikata kuwa suna amfani da su ne a matsayin takatsantsan da takaita kalamai.

A wajen masu shekar ashirin da doriya "alamar motsin rain a nufin kai aboki ne nagari, yayin da kwanan wata ke nuni da cewa da gaske kake yi," inji Lahiri.

Dige-dige na da rudarwa, inda suke nuni da karshen jimla ga tsofaffin mutane, amma suna nuni da mummunar manufa ga matasa.

Daukacin kalmomin da aka fara da manyan baki a sakon i-mail na nuni da fushi a wajen wasu, sai dai bah aka lamarin yake ba , a wajen tsofaffin mutane, a cewar Lahiri.

Duk mukan yi ishara da mabambanciyar fahimta da salo-salon harshe a rubutunmu.

Kuma fassara sakon i-mail kan bambanta a tsakanin jinsi. A binciken da ta gudanar, ta nan ne ta gano cewa matan da ba sa amfani da alamar motsin rai, suna maimaita haruffa (bakake- tooo ko zooo) ko sauran alamun da ke nunin muhimmanci sosuwar rai a i-mail dinsu wadanda akan fassara a amtsayin bacin rai a wajen wwasu da sakon ya isa gare su..

Sai dai mazan da ke aikewa da sakonnin i-mail kai tsaye ba tare da nuna sosuwar rai ba ko kadan ba haka suke kasan cewa ba, kamar yadda ta gano.

Sannan maza sukan aike da takaitaccen sakon i-mail, wanda a mafi yawan lokuta yake kunshe da barkwanci, wanda idan ya isa ga masu karanta sakon i-mail din ba su cika fahimtarsa ba, kamar yadda yadda Tannen ta ankarar.

"A yi takatsantsan kana bin da irin wadannan sakonni ke n8uni a kanka da yaddda za a fassara shi," in ji ta.

Juyin furuci

Duk da cewa yana da matukar alfanu a fara rubbuta ssakon i-mail da nuna kyautatawa cikin kwarewa, za ka iya bin kyakkyawan tsarin da aka sani yayin da kake kulla alaka, har ka saba da wani.

Wata dabarar da Tannanen ta bijirro da ita ita ce kwaikwayon kalaman mutumin da akek aike wa sakon i-mail din.

Idan har yanzu kana cikin damuwa kan yadda ake fassara sakonnni i-mail dinka na hada-hadar kasuwanci, to kirrkirarriyar fasaha za ta taimaka a nan.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Amfani da maballan shafukan sadarwar intanet da suka hada da martanin Booomerang da bibiyar kalamai na Watson da ke IBM za ssu tiamaka wajen warware boyayyar ma'anar d ake kudundunee a sakonka ko na wani daban.

"Daukacinmu muna nuni da ambambantan tsarin tunani da sarrafa harshe a rubutunmu," a cewar Rama Akkiraju, wani Injiniya a IBM, a bangaren Watson da ke reshensu na San Jose a California.

Irin wannan kirkirariyar basira kan bibiyi komai tun daga kan zabar kalma da tsawo da ka'idojin rubutun nakala don nuna maka cewa kai mai kambama kai ne ko mai kyakkyawar mu'amala ko kwarin gwiwa.

Yi tunanin kammalawarka

Hanyar da ta fi dacewa a kammala rubuttun i-mail ita ce nuna kyakkyawan zato da godiya, a cewar Boomerang Moore.

Hanya mafi kyawu ta kammala rubutun sakon i-mail, ita ce ta nuna karamci, a cewar Boomerang's Moore.

Kammalawa na iya kasancewa da "godiya har a gaba" nkamar yadda yake kunshe a sakamakon binciken da Boomerang ya gudanar da ya tabbatar da amincewa kasha 65 cikin 100.

Sai dai tsanantawa gme da amrtani, alal misali "kada a yi sako-sako wajen kira" zai zo a matsayin kaskantarwa fiye da taimakawa, a cewar Lahiri.

"Tabbas zazzafan kalami ne aka jero a dukunkune," saboda zai sa mai karatu ya zurfafa tunani kan tasirin martanin su, a cewarta.

Duk wani abin da aka rubuta yana tattare da hadarin yi masa mummunar fasssara, don haka da zarar ka aike da martini cikin hanzari, sai ka sake bibiyarsa, ta yadda ba za ka fada tarkon wadanda ake ganin a matsayin masu harzuka cikin fushi.

Sai dai idan kawai abin da kake bukata ke nan.