Yadda za a yi aiki tare da mata-maza

Abokan aikin Quinn Nelson suna cike da tababar abin da ya kamata su yi lokacin da suka kasance a wajen aiki su ba a bangaren kowane jinsi suke ba. Hakkin mallakar hoto (Credit: Elizabeth S. Cameron/Quinn Nelson)
Image caption Abokan aikin Quinn Nelson suna cike da tababar abin da ya kamata su yi lokacin da suka kasance a wajen aiki su ba a bangaren kowane jinsi suke ba.

Daga Jessica Holland

30 ga Agustan 2017

Kokarin tabbatar da kimar mutuntakar mutanen da ba sa cikin jinsin mata ko maza ba, al'amari ne da ke bukatar sauya alkiblar fahimtar kimar mutuntaka da kalmomin da muke amfani da su, musamman a wajen aiki.

"Ina da tabbacin cewa akwai murtanen ba sa kaunar kasancewa haka ko samun kansu a yanayin," a cewar Quinn Nelson. "Kawai a birkice suke tattare da rudani."

Dalibar nazarin halayyar dan Adam a Jami'ar Calgary da ke Canada mai shekara 24 ta kwatanta yadda mutum zai kasance a cikin abokan aikinsa in ya kasance ba a daya daga cikin jinsi mace ko namiji ba - a shekaru kadan da suka gabata, kuma a hakan ake ta kokarin bayyana cewa jinsi ba zabi ba ne na alamun da ake bari a takardun neman bayanai a wajen aiki na guraben da ake yi wa alama da zanen akwatunan.

Abokan aikin Quinn Nelson suna cike da tababar abin da ya kamata su yi lokacin da suka kasance a wajen aiki su ba a bangaren kowane jinsi suke ba.

"Wadanda ba a kimanta su tsakanin jinsuna biyu - marasa jinsi" lakabi ne da ake yi wa mutane don fahimtar jinsinsu a matsayin mata-maza, wadanda babu su, ko ba su kasance a tsakanin jinsunan ba, sannan ba su da kimar jinsi takamaimai. Nelson, tamkar dimbiun mutane a rukuni daban-daban sun fi son a yi musu amfani da lakabi mara nuni da jinsi., kamar "su," sabanin "shi" ko "ita."

Daga 2 zuwa 58 zuwa karshen kirga

Shekaru kadan da suka wuce, ana ta fafutikar kimanta mutuntakar mutane da ba su kasance a rukunin jinsunan da al'ada ta fayyace ba, Facebook ya fadada jerin jinsuna da ake da zabi daga 2 Zuwa 58 a shekarar 2014 kafin bayar da dama ga masu ta'ammmali da shafin su yi amfani da siffar kimanta mutuntaka bisa al'adarsu a shekarar da ta biyo baya..

Kasashe da dama sun fara kimanta mutumtakar mutanen da ba sa cikin rukunin jinsuna.

Duk da cewa akwai dimbin bayanai kan yawan al'umma, yawan mutanen Birtaniya da suka cikee guraben akwatunan alamun rashin jinmsi ya kasance 0.4 cikin 100 a daukacin kidayar jama'a da aka gudanar a tsakanin shekarun 2001 zuwa 2011.

Birataniya a halin yanzu ta fara bin Kadin ko nazarin yadda za ta tattara bayanan rukunin marasa jinsi a kidayar jama'a ta shekarar 2021.

Sun ji cewa akwai abin da suke bukatar yi, amma ba su da tabbaci kan ko mene ne.

Duk da fadakarwar da ake yi game da rukunin marasa jinsi - kashi 50 cikin 100 na matasan karni na 21 suna da tabbacin cewa jinsi alama ce da nuni da rukunin mutane biyu, kamar yadda sakamakon wani bincikeen jin ra'ayin jama' ya nuna na Fusion a 2015, al'amarin da har yanzu yake tayar da hankali mutane irrin su Nelson su kasa samun natsuwa a wajen aiki.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

"Wadanda babu su a rukunin jinsuna biyu" ana kwatanta su a matsayin mutanen da suka tattare jinsuna biyu, wato mata-maza, ta yadda su ba sa cikin rukunin jinsuna ko sun tokare a tsakani, haka kuma ana iya daukarsu marasa jinsi ko wadanda jinsinsu ya kwaranye.

"Na ji cewa [abokin aikina] na da tunanin yin wani abu, amma ba su da tabbaci kan ko mene ne," in ji Nelson. Nima ban san ko mene ne ba."

Wani bincike da mujallar da ake wallafawa a shafin intanet ta gudanar mai taken lamarin da ya sha gaban jinsuna biyu (Beyond the Binary) a Maris din 2017 ya yi nuni da cewa kashi 1 cikin 100 daga mata-maza 225 na mutanen da ke jin cewa "suna da cikakkiyar kariya" dokar daidaito a wajen aiki da ake da ita a halin yanzu a wajen aiki, kuma kashi 42 cikin 100 na fama da matsalar halin da suka samu kansu a ciki bisa la'akari da kimar mutuntakar jinsin su a wajen aiki.

Misalan wadannan munanan al'amuran sun hada da zolaya, kimanta rashin jinsi, hana su amfani da bandakunan wajen aiki, akan kwace ayyukan yi da a ka ba su.

"Al'amarin ya tayar mini da hankali," a cewar J Fernandez, editan mujalla. "Idan ka ji cewa ba ka da natsuwa a mafi yawan kwanakinka, wannan na nufi karara lafiyar kwakwalwarka ta yi matukar tabuwa.

Samun natsuwa

Fernandez yana amfani da da daukacin nau'ukan wakilan sunan da ke nuni da mutane biyu ko fiye a Ingilishi, wato "they/their" kuma a halin yanzu ba shi ne alamar nunin jinsi ga abokan aiki a kan aikinsu ba.

Wannan ba wani abu ba ne bambarakwai (da za a ce ba a saba da shi ba), a cewar binciken jinsin mata-maza na 2016 Scottish Trans Alliance (Kungiyar Hadin gwiwar mata-maza a Scitland)), wanda ya gano cewa kashi 4 cikin 100 na mata-maza suna jin dadi a kodayausshe su bayyana kimar jinsin su a lokacin aiki, kuma kashi 90 cikin 100 suna da damuwar kada a wulakanta su.

"Ina tsoron bayyana kaina a matsayin mata-maza a wajeen aiki," in ji. "Ina ganin rashin bayyanawa karara wajen tafiya da mutanen da ba su da jinsi (mata-maza) shi ke firgita ni fiye da yadda ya kamata.

Samar da tsari karara da ke nuni da cewa mata-maza mutane ne da ake maraba da su, wadannan su ne matakan da muke dauka,' ta yadda za su rage wa mutane firgici."

Idan ka ji baka da natsuwa a mafi yawan lokutan rana, ta bayyana karara lafiyar kwakwalwarka ta dan tabu.

Irin wadannan al'amuran ban tsoro ba za a ce ba su da tushe ba.

Wani marubuci da ke zaune Landan, mai kwanaren shigar mata da gabatar da shirin rediyo na Ray Filar ya gano wannan lamari ne bayanan da ya aike da saqon imail ga abokan aikinsa da ke aiki a wata mujalla a lokacin, kan su bayyana jinsinsu, sannan wane juyin harshe (sarrafa kalmomi) ya kamata a yi amfani da shi yayin da ake nuni a kansu.

"Ba na jin cewa nau'ukan wakilin ssuna ne karshen lamari wajen damawa ko tafiya tare da mata-maza (marasa ggurbi a tsakanin jinsunan mace da namiji)," inji filar. "Sai dai su ne muhimman takun tarairayar kyautatawa."

Hakkin mallakar hoto (Credit: Alamy).

Jarumin nahiyar Asiya mata-maza Kate Dillon (a dama) wanda ake kira Taylor Mason sai mashahurin mai koyon aikin talabijin da asusun saka jari na hedge ya dauki nauyinsa a shirin Biliyoyi.

Duk da haka, filar ya gnao cewa kadan daga cikin abokan aikinsa sun yi watsi da nusarwar da aka yi musu ko "kawai sun yi watsi ko kin tuna abin da na bukace su da shiga."

Baya ga kasancewa "marar jinsi da ake ta maimaitawa tsawon shekara biyu," Filar ya ajiye aikinsa. Bisa la'akari da al'amuran da ya samu kansa a ciki, filar ya bukaci wuraren aiki da su aiwatar da tsare-tsaren da za su sshawo kan kyarar wariyar bambanci da ke nuna wa mata-maza (marasa gurbin jinsi a tsakanin maza da mata).

"A yi ta maimaita muhimmiyar horarwa da ilimantarwa a matsayin wani yanki na aiki," Filar ya bayar da shawara, "sannan ma'aikata mata-maza da masu aikin wucin gadi ta yadda za a ba su damar shawo kan matsalarsu don kada ta sake dirar musu in an yi amfani da ita.

Dangane da masu daukar aiki (kamfanoni ko ofishsoshi ko ma'aikatu) da ba su da masaniyar ta inda za su fara aiwatar da wadannan tsare-tsaren, Fernandez ya bayar da shawarar tunkarar kungiyar mata-maza don bayar da shawara, kamar kungiyoyin da suka hada da Gendered Intelligence (masu bin Kadin jinsi) da Scottish Trans Alliance (hadin gwiwar mata-maza a Scotland)..

"Lamarin ba shi da wani babban tashin hankali," a cewar Fernandez.

"Idan kana wani mata-maza a jerin ma'aikata, kawai ka tattauna da su kan abin da zai kawo musu saukin jin dadin rayuwa (ta aiki). Lamarin na da matukar sauki ta hanyar ba su tabbacin cewa babu wata matsala don an sanya tufafi na daban ko suna mabambanci.

Abokan iki na da gudunmuwar da za su bayar wajeen samar da kyakkyawan muhalin tarairayar mata-maza, a cewar Fernandez.

"Abin da ya taimaka mini shi ne yadda mutane suka kula, wajen karrama ni, suna amfani da wakilin sunan da ya dace, kuma su nemi afuwa idan sun yi kwaba, amma ba wani babbban abin damuwa ba ne, kawai a san yadda za a zauna a halin da ake ciki.

"Mafi yawan mutane na dari-darin bijiro da tambaya kan kowane ne mata-maza (mara gurbi a jinsuna biyu - mata da maza), 'Wane nau'in wakilin suna kafi ganin dacewarsa?'

"Amma kawai lamari mafi kyau wajen karrrama mutum, tamfar yadda za ka tambayi sunan mutum idan ba ka sani ba."

Matakan da za a dauka

Idan masu daukar aiki sun yi matukar kokari wajen tarairayar daukacin jinsuna da nunin furuci, kyakkyawan tasirin lamarin zai kasura ya bayyana karara.

Quinn Nelson ta koma aiki a matsayin mai karbar kudi da bayar da canjin ciniki a karamin kamfani sayar da kayan abinci, kuma a wannnan karon, sabanin fitowarta bayan da ta fara aiki, Nelson karara take bayyana alamun jinsin su a lokacin tattaunawa, kuma sun samu kyakkyawan yanayin da ya bayar da damar yin hakan.

Wannan bayana nufin a ce ko da yaushe lamarin na da sauki ba.

Daya daga cikin abokan ciniki ya fada wa Nelson za su kasance "sarauniyar masu kwanaren sanya tufafin mata" wani kuwa korafi ya yi ga hukumar gudanarwar kamfanin game da "mazan da ke sanya suturar mata."

Hakkin mallakar hoto (Credit: Ray Filar)

Nau'ukan wkailin sun aba su ba ne jigon tafiya da kowa-da-kowa, amma kyakkyawar hulda ce, a cewar marubuci mazaunin Landan, mai kwanaren shigar mata da gabatar da shirin rediyo na Ray Filar.

Akwai kyakkyawan yanayi game da lamuran. Da zarar abokin hulda ya kalli bajen da ke makale a jikin Nelson dauke da wakilin suna, sai ya ce lalllai zai sanar da abokansa su mallaki guda.

Wani namiji ya sanya yaro ya Makala jan farce, sai ya cika annnashuwa ganin nelson ta lailaye shafen farcenta da shi. Na ce: "Nakan yi kuka lokacin da nike magana kan lamarin, kuma ina yin kuka da zarar hakan ya faru."

Wannan lokaci na kulla alaka zai iya faruwa ne kawai, a cewar Nelson, saboda sun samu cikakkiyar natsuwa a wajen aiki.

"Zan yi matukar kaunar samun aiki a wurin da tsarin gudanarwarsa tuni ya saba tafiya tare da mata-maza," in ji Nelson.

"Ko akwai wajen wanka da aka kebe wa mutanen da babu su a jerin jinsuna (na mace da namiji), ta yadda ban a bukatar ilimantar da mutane, sannan in ji dadin yin aiki a wajen.

"Lamarin na da ban takaici ganin cewa akwai Karin aiki a gabanka da zarar an dauke ka aiki."