Me ya sa Turawa ke tururuwar wankan tururin ruwan dumi?

Hakkin mallakar hoto (Credit: Kristof Minnaert)
Image caption Kristof Minnaert dan Belgium da yanzu ya samun natsuwa da yin hutu a dakin wankan suracen rufin daki tare da abokan aikinsa na kamfanin sarrafa dabarun wasannin na'ura don nishadi da ke Helsinki

Daga Lennox Morrison

21 ga Oktobar 2016

Sakon Edita (23 ga Disambar 2016): Zuwa karshen wannan shekarar, BBC zai dawo muku da wasu daga jerin labaran da kuka fi sha'awarsu daga 2016

Ba zan taba mantawa da karon farko da na zauna zindir, kugu-da-kugu a kan bencin katako tare da shugaban wajen aikina.

Wannan shi ne makon farko na sabon aikina a kamfanin sarrafa na'urar kwamfuta da ke kusa da Heidelberg a kasar Jamus.

Ni dan asalin kasar Scotland ne, inda gwamutsuwar shakatawar aiki ke nuni da zuwa mashaya. Ban taba mafarkin zan kasance a waje tunbur tare da abokan aikina, balgacen kankara na fadowaa fatata.

A gareni wannan al'ada na da matukar rikirkitarwa. Amma a Jamus da Holland ko Finland ba wani abu ba ne bambarakwai (ko sabon abu zama zigidir tare ) da abokan aiki.

Kuma a Finland al'amari ne da aka yarda da shi ka zauna kugu-da-kugu tare da shugabanka na wajen aiki zindir babu tufafi.

Lamari ne da aka saba da shi ka je ka zauna a dakin surace tare da shugabanka na wajen aiki.

"Finland kasa ce da ba a nuna fifikon matsayi. Ba ma tsaurara tsarin zamantakewa bisa kimar matsayi (fifiko)," inji Katariina Styman, Shugbar kungiyar wankan surace ta Finland da ke Helsinki.

"Lamari ne da aka saba da shi ka zauna tare da shugabanka na wajen aiki. . Wuri da ake watsi da da kimar matsayin aiki ko matakin albashi.

A wannan kasa ta Arewacin Turai da ke da yawan al'umma kimanin miliyan 5.5, akwai gidan surace guda ga kowane rukunin mutane biyu, a cewarta. Mafi yawan kamfanoni suna da gidajen wankan suracensu.

Ka taba yin mamaki ko rikirkicewa ko kaduwa da tsarin al'adun wata kasa ta daban? Baza labarinka a kafarmu don bibiyarsa tare da mu.

Sabanin Jamus, inda ake gwamuwa (maza da mata) a gidan wankan surface, al'adar mutanen kasar Finland ita ce idan ka fita daga da'irar iyalanka - maza da mata sukan ziyarci wajen wankan surface daban-daban.

Ko a hakan ma, sababbin zuwa wadanda ba 'yan asalin Finland ba a karon farko kasancewa tare da abokan aiki a bukokin shakatawa ba lallai ba ne mutum ya samu cikakkiyar natsuwar hutu yadda ya kamata.

"Lamarin tamkar matakin kaiwa ga gaci ne don shawo kan lamarin." Inji Kristol Minnaert, dan kasar Belgium da ya koma Helsinki a shekarar 2013 ya kama aiki da kamfanin tsara wasannin na'ura don nishadantarwa.

Dakin shirye-shiryen kamfanin da ofisoshinsa da ke Espoo suna dakin wankan surace a rufinsu. "Sai ka tube zindir sannan ka isa wajen.

Za ka ji an yi maka tsawa ko wulakantaka idan harka daura mayafin wanka (tawul) ko gajeren wandon ninkayar kurme," a cewar Minnaert, mai shekara 30 babban jami'in fasahar zayyanar wasanni

Bayan shafe shekar auku, sai kawai ya ji ya samu natsuwa, ta yadda kowane yammacin ranar Juma'a sai ya yi wankan surface tare da abokan aikinsa, inda aka saba da surbar barasa sannan a fito waje a tube ba tare da sutura ba.

Hakkin mallakar hoto (Credit: The Finnish Sauna Society)
Image caption Kungiyar masu ta'ammali da gidan surface da ke kusa da birnin Helsinki

Shi da rukunin abokansa sukan shafe tsakanin sa'a guda zuwa uku a dakin wankan surace kowane mako, yayin da ba sa gudanar da taro, sai dai su yi 'yar tattaunawa kan aiki, a wani lokaci kuma su fito da wata kyakkyawar dabarar aiki da zarar su koma sun zauna kan teburansu.

"Lamarin ya yi dna kwatankwacin zuwa mashaya, amma kadan ake sha, a wurin da ake gumi," inji shi. ""Ya fi kyau a lokacin hunturun sanyi sabon yanayin kan kai - 30 digiri bisa ma'aunin Salshiyos a wajen farfajiyar. Idan ka koma ciki sai ka kara samun kuzari.

Madallah da gayyatar da shugaban wajen aikinsa ya yi masa, Minnnaert ya kuma shiga kungiyar masu wankan surface ta kasar Finland da ke kusa da Helsinki, inda ake yin al'adar tafasa ruwan zafi maitururi da itace "hayakin dakin surace" ana sanya murhun azurfa da gungumen itace yana kallon ruwan (tekun) Baltic.

A nan ttsofaffin shugabannin kasa da sauran hamshakan mutane ke haduwa a tunbur tare da sauran masu zuwa wankan surace, inda suke samun damar yin tsallen tsundumawa cikin ruwa ko da a lokacin hunturu ne, inda ake huda kafar kankara.

Tommi Uitto, babban jami'in mataimakin shugaban kamfanin hada-hadar kasuwancin kayan sadarwa a kamfanin sadarwar duniya na Nokia, ya bayyana cewa: "A dakin wankan surace babu abin da ke nuni da mukamai, babu sutura.

Ba a nuna jiji da kai, don haka wurin na da mutuntawa, kuma tunaninka da kalmominka aka barka da su, haka lamarin yake ga wani mutumin, ta yadda alakar kawai ta mutum da mutum ce kawai, kuma daukacin wata kawai an kawar da ita."

Kamfanin Nokia yana da dakunan surace a daukacin rassansa uku dd akle kasar Finnalan. "An ware su," inji Uitto. "Kowane dan kasar Finland da ya nemi aiki a kamfanin Finland yana sa ran akwai wajen wankan surface a kamfnain."

Farko fara aikin Uitto an dauki dakin surface a matsayin wajen gudanar da kasuwanci, a cewarsa. Kuma rukunin ma'aikata kan taru gaba daya a dakin surace don bikin murnar samun nasarar kamfanin da koluluwar nasar ko kimar matsayin da ya kai, sabanin zuwa gidan sayar da abinci ko mashaya.

Amma a shekarun baya-bayan nan, sai dai an rage bai wwa gidajen wankan surace muhimmanci, saboda ta wani bangaren kamfanonin Finland sun zama na duniya, sannan harkokinsu na kara cukurkudewa, a cewarsa.

Sannan tun da mata da maza na ziyarar gidajen wankan surace daban-daban, a wajen mutane da dama ba sa jin dadin taruwa don tattunawa kan harkokin kasuwanci.

"Lamarin na nuni da cewa ba daidai ba ne a raba rukunin mutane gida biyu," in ji Uitto.

Kasan al'adu

Yayayin da gidanjen wankan surrace (saunas) suka shahara a Arewacin Turai, a kasashe irin su Sweden da Rasha da Netherlands al'adu da dabi'u sun yi matukar bambanta.

Jan Feller, mukaddashin manajan Daraktan Cibiyar hadin gwiwar ciniki ta Jamusawa da mutanen Finland da ke Helsinki, ya yi aiki a daukacin kasashen.

A wajen 'yan Finland, wajen wankan surace wurri ne da kake zuwa a kashin kanka tare da wasu mutane," a cewar mutumin mai shekara 41.

"A Jamus kuwa al'amarin da ya ta'allaka da kyautata ingancin lafiya."

A lokuta da daman a sha yin kokarin kare al'aura da ke tsakanin mahadar cunar kafafuna.

A kasar Finland, masu zuwa wankan surace (da tururin ruwan zafi) har kwara wa gawayi ruwa suke yi da kanbsu, amma a Jamus har ma akwai babban jami'i mai kula da wajen wankan surace da ke yin wannan aiki akai- a kai, lokuta daban-daban, a cewarsa.

"Kawai a hakikanin gaskiya za ka samu rubutattun dokoki manne a jikin bango dakin wankan surface a Jamus, al'amarin da idan mutanen Finland sun gani sai dai su yi murmushi kan lamarin," inji Feller.

A Jamus da Netherland kada ka sa ran samun gidan wankan surace a wajen aikinka.

Sai dai idan kana shiga wajen wasannin motsa jiki bayan an tashi daga aiki tare da abokan aikinka, akwai yiwuwar ka samu wajen wankan surace a wuraren wasannin motsa jiki.

Hakkin mallakar hoto Hill Creek Pictures
Image caption Yayayin da gidanjen wankan surrace (saunas) suka shahara a Arewacin Turai, a kasashe irin su Sweden, Rasha da Netherlands al'adu da dabi'u sun yi matukar bambanta

Lokacin da Sam Critchley wanda ya kafa kamfanin tallat ahajar kayan sadarwa na Spaaza ya fara zuwa Amsterdam daga aslain kasarsa ta Birtaniya shekaru 18 da suka wuce ya je yin wasan kwallon squash da abokan aikinsa.

Bayan kammala wasan, kowane (dan wasa) sai kawai ya fi zuwa wajen wankan surface ya tube zigidir. Babu wanda ma ya damu da ko kamfai da 'yar rigar ninkayar kurme, amma a matsayi na dan asalin Holland (Dutchland) guda sai na far son sanya wani abu. Sai ya zauna a dakin tururin ruwan zafi ya yakice lullubin tawul dinsa, a cewarsa.

"Kwatsam sai wannan mata abokiyar aikinmu ta fito daga wajen suracen ta tambayeni za ka zo cin abinci bayan ka kammala?

Daga nan sia ta bude kofa, inda nike iya ganin abokan aikina mata uku ko hudu a kan bencina suna zaune kan layi," kamar yadda wnai mai shekara 43 ya tuno da lamarin.

Matakin farko da na dauka shi ne dora hannuna a kan mahadar cunar kafafu."