Abin da ya sa ba ka bukatar shugaba mai faran-faran

Kasancewar shugabanka na da fara-faran ba ya nufin ka samu shugaba na gari. Manaja mai tsanani da takurawa shi ne zai ingizaka ka zage damtse. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kasancewar shugabanka na da fara-faran ba ya nufin ka samu shugaba na gari. Manaja mai tsanani da takurawa shi ne zai ingizaka ka zage damtse.

Kowa na bukatar shugaba mai faran-faran da jama'a.

Idan shugaba mai faran-faran shi ne wanda zai karramani da aikina, ya kalubalance in kara dagewa, kuma ya ke bukatar ganin na ci gaba da samun kwarewa, to ni ma ina son haka.

Amma mutane da dama kan kalli shugaba mai matsawa a matsayin mai kama-karya.

Abin da mutanen ba su gane ba shi ne: kasancewar ka na da shugaba mai faran-faran, baya nufin ka na da shugaba nagari.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk mutum ne da aka sani da neman kwazo daga ma'aikatansa kuma yana samun haka

Na sha ganin shugabanni wadanda kan ce su na bukatar ma'aikatansu su zage damtse sai dai kuma daga baya sai in fahimci cewa so su ke ma'aikatan su so su.

Baya ga haka, su na son mutane su yaba musu, su dauke su a matsayin 'abokai'.

Irin wadannan shugabannin su ne ke tsoron idan su ka sa wa ma'aikatansu ayyuka masu wuya, su ka kuma nemi su yi fiye da abinda ma su ka sa su, darajarsu za ta karye.

Saboda haka, sai su rage matsa wa ma'aikatan wani lokacin ma ba tare da sun sani ba.

Hakan na jawo ma'aikatan su rage kwazo.

Mafi ingancin shugabannin da na sani, a fannin bincike ko kuma koyarwa, na mayar da hankali ne kan samar da sakamako na zahiri.

Wadannan shugabanni masu samu cikakkiyar nasara ba su damu da sai an so su ba.

Abinda su ke nema daga ma'aikatansu shi ne aiki tukuru ba tare da sassauci ba - kuma ma'aikatan sun san da haka.

Alal misali, fitaccen dillalin filaye da gidaje na kasar Amurka, Bill Sanders.

"Kowa ya san Bill na bukatar sakamako na zahiri," in ji Ronald Blankenship, tsohon shugaban kamfanin zuba jari a harkar filaye da gidaje na Verde Realty kuma abokin Sanders na kut-da-kut.

"Idan za ka yi masa aiki, ka na bukatar ka mai da hankali wurin cimma manufar da aka sa gaba."

Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption Rashin fargaba ga ma'aikaci wajen jingine dokoki ka iya karawa ma'aikaci kimi a tsakanin sauran ma'aikata

Wadannan fitattun shugabannin ba sa tsoron kafa doka tare da tabbatar da cewa an bi ta.

Abin mamaki kuma, tsananinsu tare da tabbatar da an cimma manufa, kan sa masu aiki a karkashinsu su kara girmama su.

Kai abin ma ya wuce girmamawa har ya kai ga darajtawa da kimantawa kai wani zubin ma har da kauna.

Amma fa matsantawa ba ya nufin cin zarafi.

Ko da yaya za ka gane idan ka na neman fadawa cikin tarkon zama shugagaba mai faran-faran?

Yi la'akari da wadannan tambayoyi - ka ga guda nawa ka ce 'e'.

Cikin shekarar nan, ka sauya wa wani ma'aikaci manufofin da ka ke so ya cimma, fiye da karo guda, bayan da ya gaza manufofin da ka ke so ya cimma?

Cikin shekarar nan, ka taba kyale wani da ya saba dokarka ba tare da ka hukunta shi ba?

Ka kan bai wa ma'aikata wani alawus na musamman ko da sun gaza cimma manufa - saboda kawai "sun kokarta"?

Ka na gaza sa wa ma'ikatanta bayyanannun manufofin da ka ke so su cimma?

Bayyanannun manufofi su ne wadanda su ka kasance kayyadaddu, wadanda za'a iya aunawa, za'a iya cimmasu, kuma aka hada su da iyakantaccen wa'adi.

Ka kan kasa gaya wa ma'aikaci ya yi ba daidai ba saboda gudun bata masa rai?

Idan kuma ka tashi yin gyaran, ka kan sassauta harshenka?

Shin shugabanninka da abokan aikinka na daukarka a matsayin mai saukin kai da tausayi?

Shin masu aiki a karkashinka na yin lako-lako idan su ka kai wani gaci, ba tare da kokarin kai wa mataki na gaba ba?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba mai tsanani zai iya sa a fuskanci matsin lamba amma yakan tunzura mutane su kara kwazo a aiki

Idan ka samu kanka ka na cewa 'e' ga tambayoyi uku ko fiye daga cikin wadanda aka ambata a sama, mai yiwuwa ne ka afka cikin tarkon zama 'Shugaba mai faran-faran'.

Idan haka ne kuwa, to lokaci ya yi da za ka sauya dabi'unka.

Idan har ka na so a girmamaka ba kawai a so ka ba:

Ka samar da 'littafin manufofi', inda za ka bayyana abubuwan da ka ke so kowanne ma'aikaci ya cimma, inda kuma za ka rika rubuta bayanai game da ayyukansu na yau da kullum, tare da duk wani mataki da ka dauka na ganin sun cimma muradunka.

Duk rahoton da ka fitar, ka sake duba manufofin da ka sa a gaba.

Shin sun kai matuka?

A bayyana su ke kuma ana iya kididdige su?

Ka da ka rage don kawai wani ya gaza cimma manufa.

Shin da akwai wata hanyar da za ka iya sa gasa tsakanin ma'aikata wurin cimma manufofin da aka sa gaba?

Hakan zai iya sa su zage damtse kuma ya hana ka sassautawa idan wani ya gaza.

Ka koyi yadda ake gaya wa ma'aikata cewa aikinsu bai yi ba:

Kiyaye bayyana bacin rai ka tsaya kawai ga hujjoji na zahiri; duk wanda ya kauce hanya ka sanar da shi da wuri; ka mayar da hankali kan yadda za a gyara gaba ba wai sukar baya kurum ba.

Shugabanni masu faran-faran na iya jin dadin zama da ma'aikatansu, amma ba sa samar da sakamako na azo-a-gani.

Shugabanni masu tsanantawa su ke samar da hakan.

Idan kuma ka na aiki ne karkashin shugaba mai faran-faran, to kar ka gamsar da kanka cewa komai ya yi daidai.

Idan har ba ka samun ci gaba a sana'arka, tare da koyon sababbin abubuwa, to gaskiya ba a tsaye ka ke cik ba, an bar ka a baya.

A rayuwar aiki ta zamani - inda kalubale ke iya bullowa daga ko'ina kuma a kowanne lokaci - tafiya sannu-sannu ba hanyar samun nasara ba ce.

Idan kana son karanta wannan labarin a harshen Ingilishi latsa nan: Why do you need a nice Boss