Ka san ma'anar launin lakataye?

An sabunta wannan labari bayan da aka wallafa shi a karon farko a watan Mayun 2016.

BRENT WINEBRENNER

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin da Joshua Blue mataimakin shugaban makarantar Kennedy School a Hong Kong ya shirya wa ɗalibansa wani taro, ya sanya lakataye mai launin shanshanbale (shudi-shudi), domin ya fita daban a cikin ɗaliban ta yadda ba za su ƙosa da maganganunsa ba idan yana jawabi.

Malamin ya ce lakataye din yana da launi mai kyau amma kuma duk da haka ba ya fitowa sosai, abin da shugaban ya ke gani zai hana daliban gajiya idan suna sauraron jawabinsa.

A daya hannun Mista Blue mai shekara 35, ba ya son sanya lakataye me launin da yake da haske idan zai yi wa dalibai jawabi domin kada launin ya rika dauke musu hankali a lokacin jawabin.

Za ka ga kamar shirme ne kawai, amma kwararru sun ce kowane irin taron muta ne ne za ka yi wa jawabi, ma'aikata ko dalibai ko wani rukuni na jama'a na daban, idan ka sanya lakataye mai launin da ya dace hakan zai taimaka ma wajen isar da sakonka.

David Zyla marubucin littafin Color Your Style, wanda yake a New York ya ce, ''launi yana bayar da wani sako na musamman, za ka iya amfani da kwat (riga) daya amma da lakataye launi daban-daban, kowanne da irin sakon da zai bayar da kuma tasiri.''

Yanzu ka fara tunanin launin lakatayen da za ka sa zuwa taro na gaba? To ga yadda za ka zabi launin lakatayen da zai dace da kowane taro:

Launin ja me karfin mulki da iko

Ba wai katari ba ne ya sa kake ganin yawancin 'yan siyasa suke sanya jan lakataye da riga 'yar ciki (shat) mai haske da kuma kwat mai launi mai duhu ba.

Mark Woodman, mai fashin baki, wanda ya yi karatu a kan launi a birnin Laurel da ke Maryland a Amurka, ya ce ''launin ja lakataye ne na mulki, akwai wani abu da ke tattare da ja wanda ke nuna karfi da ado.''

Asalin hoton, Getty Images

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Yanayin jan naka ma yana da tasiri. Ja jazur na sa mutane su yarda da kai, yayin da jan da ba jazur ba da kuma launin ruwan hoda zai iya nuna irin tsarin sha'awar adonka da kuma kirkira.

Woodman ya kara da cewa, ''a shekara goma da ta wuce, lakataye mai ruwan hoda na nuna alamun goyon baya ga mata ne.'' Idan kuma kana son nuna cewa kana kan gaba a wani aiki ko ka nuna kai mai wani buri ne to sai ka sa lakataye mai launin ja mai sheki.

Lakataye mai ruwan Algashi

Ross Znavor, babban jami'i a kan harkokin kudi a New York, yana sanya lakataye jaja-jaja mai ruwan algashi (purple), maimakon cikakken ja idan za shi taron harkokin kasuwanci saboda launin yana ba mutum kwarin gwiwa kuma yana burge mutane a haduwarsu ta farko ma.

Ya ce, ''sanya lakataye mai launin da ba kasafai aka saba da shi ba, yana nuna wa mutane ko 'yan kasuwa cewa mutumin yana da kwqanciyar hankali da kwarin gwiwa, wanda kuma za ka so kulla alaka da shi.''

Lindsay ta ce, lakataye mai launin algashi wanda ake dangantawa bisa ala'da da sarauta da kuma dukiya, yanzu ya fara karbuwa a wuraren aiki.

Asalin hoton, Getty Images

Ta ce, ''maza na sanya riga 'yar cikin kwat mai launin algashi maras duhu sannan su daura lakataye mai launin algashi mai duhu, idan suna son su fita daban, a cikin taro, ba tare da sun rika daukar hankalin mutane ba.

Bakin lakataye

Zyla ta ce, ''duk da cewa ba lalle ka sanya bakin lakataye zuwa taron manyan jami'ai ba akai akai, amma sanya shi zuwa liyafa yana fito da mutum. Woodman kuwa cewa ya yi, sanya lakataye mai launin fatsa-fatsa zai iya fito da kai fes, ba tare da ana maka kallon wani wanda kamar ba a san gabansa ba.

Asalin hoton, Getty Images

Ya ce, ''launin fatsa-fatsa lakataye ne da zai sa a dauke ka wani dan zamani, idan kana son ya kara fito da kai sai ka hada shi da rigar shat mai launi maras duhu ko wanda bai turu ba sosai.

Koren lakataye

Launin kore na iya nuna abubuwa da dama kama daga alamar sabuwar rayuwa zuwa launin kudi a wasu kasashe, amma kuma abin mamaki, bai dace ba da wurin aiki domin za a iya daukar kamar ya yi bau ko kara da yawa.

Woodman ya ce, ''kana son a rika tuna ka saboda lakatayen da kake sanya wa ko kuma saboda kai kanka yadda kake?.'' Zabar koren lakatayen da ya dace abu ne mai wuya. Koren da ya yi haske sosai yawanci yana daukar hankalin mutane da yawa, kuma wani lokaci ma zai yi maka wuya ka iya samun kwat ko shat din da za ta dace da shi, in ji masanin.

Asalin hoton, Thinkstock

Duk da haka koren lakataye wanda bai turu ba sosai zai iya dacewa da shat mai launi tsaka-tsakiya.

A kasashe da dama ciki har da Ingila an dauki launin dorawa ko rawaya a matsayin launin lakataye na ainahi ko na al'ada, wanda zai nuna alamar dattaku da ado da kuma kuzari, kamar yadda Woodman ya bayyana.

Idan ka sanya lakataye mai ruwan dorawa, abokan aikinka za su iya zuwa wurinka ba tare da wata fargaba ko wani shakku ba, saboda launi ne na kwazo da ke alamta rana.

A wurin mutane da yawa, sanya lakataye mai ruwan dorawa, ''na iya nuna kwarin gwiwa da rashin shakku da kuma kyakkyawan fata a rayuwa,'' kamar yadda Eve Roth Lindsay, kwararriya kan siffa a Hong Kong, ta kara da cewa.

Sai dai ka yi hankali kada ka je ka yi kwaba idan za ka zabi launin lakataye ko kayan da za ka sanya. Misali a kasar Indiya farin lakataye na iya nufin mutum dan kasuwa ne, in ji Zayla. A China kuwa farin lakataye na nufin lokacin makoki.

Launin Shudi daban-daban

kana jin tsoron aikewa da sakon da ba shi ka yi niyya ba da launin lakataye dinka? To ka sanya shudin lakataye, wanda zai iya dacewa da komai. Shudin lakataye yana da amfani sosai saboda launin yana tuna wa mutane sama da kuma teku, wadanda ke kwantar da hankali, kamar yadda Lindsay ta ce.

''Shudi launi ne da ya fi kwanciyar hankali ka sanya,'' ta ce.

Asalin hoton, Getty Images

Lakataye shudi mai dan ado-ado a jiki yana sa mutum ya yi ruwan wani kwararren ma'aikaci kuma za a iya sanya shi a wurin wata harka ta kasuwancin duniya.

Shudin da bai nuna ba sosai yana nuna saukin kai da tunani, yayin da shudi sosai zai iya sa ka fito daban a cikin mutane, ta ce.

Shudi mai duhu yawanci yana tuna wa mutane kayan matukin jirgin sama ne shi kuwa shudi sosai launi ne da ka amince da shi wanda kuma ke bayar da karfin gwiwa, in ji Lindsay.

Ka zama daidai da duniya

''Lakataye masu launukan da ke nuna alamar zumunta kamar mai duhun kasa-kasa, da nau'in ruwan kasa daban-daban da launin hadakar ruwan hoda da na lemo da kuma ruwan dorawa suna dacewa da mutanen da suke mu'amulla da jma'a, kamar talla ko sayar da kaya da malamai da kuma ma'aikatun ayyukan jin dadin jama'a,'' in ji Lindsay.

Ka tabbatar lakatayen ba launin ruwan kasa ba ne wanda ba shi da wani zane-zane ko wani dan ado-ado a jikinsa, saboda za a iya daukar mutum kamar wani dakiki idan ya sanya shi.

Lakataye mai launin kasa-kasa mai kyalli na nuna alama ta kwanciyar hankali, masaniyar ta ce. Amma ka guji hada lakataye mai ruwan kasa da riga mai irin launin, domin idan ka damu da samun karin girma a wurin aikinka, to ka kaucewa wadannan launukan ma gaba daya.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. What the colour of your tie says about you