Ko ka san tasirin ƙurawa mutum ido?

Dan sandan kasar Chile da masu zanga zanga
Bayanan hoto,

Hoton masu zanga zanga da wani dan sandan kasar Chile yasa Kelly Grovier ta yi mana nazari akan tasirin da ƙurawa mutum ido ke yi

ƙurawa mutum ido yana da matukar tasiri.

Iya sake kallon mutum ba tare da ƙiftawa ba yana bukatar juriya da jarunta.

Ka ƙurawa mutum ido yana nufin ka nuna matsayin da ka ke da shi a duniya.

Wani hoto da wani dan jarida mai daukar hoto, Carlos Vera Mancilla ya dauka a Santiago babban birnin kasar Chile a wannan makon ya nuna irin tasirin da ƙurawa mutum ido ke iya yi.

An dai dauki hoton ne a lokacin zanga-zangar cika shekaru 43 da juyin soji da aka yi a kasar da Augusto Pinochet ya jagoranta na hambaradda da gwamnatin shugaba Salvador Allende a ranar 11 ga watan Satumbar 1973.

Hoton ya nuna wata matashiya cikin masu zanga zanga da ba ta ji tsoro ba tana tsaye gaba da gaba da wani dan sanda sanye da kayan damara tana kallon ƙwayar idonsa ta cikin hular kwano dake kansa.

Bayanan hoto,

Wata matashiya daga cikin masu zanga zanga ta ƙurawa dan sanda ido yayin zanga zangar cika shekaru 43 da juyin soji da aka yi a Chile a 1973

An dai dauki hoton ne a wajen babbar makabartar birnin Santiago, inda anan ne aka binne Allende kuma anan ne aka gudanar da addu'o'i ga mutuanen da suka bace lokacin mulkin Pinochet.

Hoton dai ya nuna fiye da gasar ƙura ido tsakanin masu adawa da kuma masu tabbatar da doka da oda.

Irin yanayin da aka ganin tsakanin 'yan makaranta da 'yan sanda manuniya ce da ta tabbatar da cewa ido ba wai kawai don kallo ba, yana da tasiri wajen nuna ƙarfi da iko.

"Duk wasu ayyuka masu kyau da suka shahara, a cewar John Ruskin wani mai sharhi, "sun samu asali ne daga kallo ba tare da shiga cikin duhu ba."

Ko da yake mu kan yi magana akan banbanci tsakanin kallo da kuma aikatawa tsakanin abun daya wuce da kuma abun dake faruwa.

Ruskin ya fahimci cewa ƙura ido wani aiki ne da ya kasance mafari wajen ƙirkiro wani abu.

Haka ma marubuciyar waƙokin soyayya Wordsworth, ta rubuta cewa "girmar duniya da kuma ido da kunne dukkan su abun da suka ƙirkiro ne ko suka fahimta".

Ka kalli wani abu yana nufin ka maida shi wani abu ta hanyar fahimtar abun.

Bayanan hoto,

Marina Abramović ta ƙurawa wani baƙo ido a lokacin fitar da wasu ayyukanta data yi a 2010

Irin fito na fito da aka gani tsakanin masu zanga zanga da dan sanda da aka dauki hoton a wannan makon ya nuna a zahiri yanayin da ake ciki, wanda ya janyo tambaya akan tasirin ƙurawa mutum ido.

Fiye da sa'o'i 736 Abramović tana ƙura ido kan duk wani baƙo da ya amince ya zauna kusa da ita a wani dakin adana kayayyakin tarihi da babu kowa a ciki a New York.

Idan kana son karanta wannan labarin da harshen Ingilishi latsa nan: don't blink first the power of a stare