Al'ummar makiyaya ta ƙarshe a Iran

Makiyaya tun shekaru aru-aru

Asalin hoton, Pascal Mannaerts

Bayanan hoto,

Makiyaya tun shekaru aru-aru

Makiyaya daga ƙasar Iran 'yan ƙabilar Qashqai ɓangare ne na al'umar Turkic da suka fito daga tsakiyar nahiyar Asiya suka zauna a Iran tun a ƙarni na 11 zuwa na 12 kuma sun karaɗe yankin Sahara dake kudu maso yammacin Iran shekaru da dama da suka gabata.

A duk shekara, su kan yi tafiya tare da dabbobin su daga arewacin Shiraz zuwa wasu yankuna da ke kusa da tekun Fasha da ke da nesan kilomita 480 da kudanci.

Tsarin rayuwar su ta na tafiya ne daidai da rayuwar dabbobin su da kuma yanayin da su ke.

Sai dai sannu a hankali wannan tsarin rayuwa na ɓacewa.

Su kimanin dubu 400,000, an sha yin ƙokari domin sauya rayuwar waɗannan al'ummomi da ba su da yawa sosai domin su koma tsarin rayuwar al'ummar Iran.

Amma makiyaya 'yan ƙabilar Qashqai sun ƙi amincewa da haka, suna masu alfahari a matsayin su na mutane majiya ƙarfi da kuma 'yanci.

Asalin hoton, Pascal Mannaerts

Bayanan hoto,

Ghazal da matar sa Tarkkenaz a cikin bukka

Ghazal da matar sa Tarkkenaz sun shafe fiye da shekara guda suna zaune kusa da ƙauye Kohmare Sorkhi, mai nisan kilomita 50 da garin Shiraz, kuma su kan yi tafiyar kilomita 200 zuwa arewacin birnin Kazerun a lokacin hunturu.

Kamar dai akasarin ƙabilar Qashqai, sun ƙi su yi watsi da rayuwar su ta gargajiya inda suke ci gaba da rayuwar da suka gada tun daga iyaye da kakanni shekaru aru aru.

Ghazal tsohon malami ne da ke koyar da harshen Farsi ga 'ya'yan makiyaya na tsawon shekaru 30 kuma yanzu ya ajiye aiki.

Ya yi amannar cewa wannan aiki yana da muhimmanci saboda yana ba 'yan ƙabilar Qashqai damar jaddada 'yancin su da kuma al'adun su.

Sai dai yana da matuƙar wahala a samu malami da zai riƙa tafiya tare da 'ya'yan makiyaya.

A yanzu dai makiyayan 'yan ƙalilan ne suka cancanta, kuma waɗanda ke zaune a birane da ƙauyuka ba su saba da yanayin rayuwar sauran makiyayan ba.

Yayin da al'ummar ke fama da ƙarancin malamai, mai yiwuwa ƙananan yaran ba sa zuwa makaranta, ko kuma iyayen su ba su iya ɗaukar ɗawainiyar tura 'ya'yan su makaranta a birni inda kuma daga bisani galibi su kan zaɓi su zauna a can.

Asalin hoton, Pascal Mannaerts

Bayanan hoto,

Dattawa su ke ƙarfafa al'adu

Dattawa su ke ƙarfafa al'adu

Sajewa cikin al' amuran siyasa tun daga shekarun baya ya sa 'yan ƙabilar Qashqai da dama sun yi hijira zuwa manyan birane da ƙauyuka, inda bunƙasar manyan birane ya sa aka mamaye wuraren da su ke kiwo.

Sai dai tsarin rayuwar su ta ƙarfafa hadin kai da zumunci tsakanin iyalai 'yan ƙabilar Qashqai da kuma sauran al'ummomi.

Madina 'yar uwar Ghazal ce wacce mijinta ya rasu shekarun da suka gabata, kuma a halin yanzu 'yan uwanta ne ke taimaka mata tun bayan rasuwar sa.

Yanzu dai tare su ke tafiya ko ina cikin kasar, kuma tana ganin ba abu ne mai yiwuwa ba ta yi watsi da rayuwar da aka haife ciki ta makiyaya ta kuma ta yi renon 'ya'yan ta a ciki.

" Ta ce mun saba da irin wannan rayuwar, ban taɓa zama a birni ba, kuma ba zan taɓa komawa in zauna a birni ba, anan rayuwata ta ke".

Asalin hoton, Pascal Mannaerts

Bayanan hoto,

Mutane da dabbobin su

Akasarin 'yan ƙabilar Qashqai na ganin rayuwa ba za ta taɓa yin dadi ba muddin ba bu dabbobin su saboda su ne ginshiƙin rayuwar su.

Su kan yi amfani da dabbobi domin samun nono da man shanu da kuma nama domin amfanin yau da kullum, kuma su kan sayar da ƙananan dabbobin a kasuwar Shiraz domin samun kudin saye wasu abubuwan da su ke buƙata.

ƙaruwar matsalar da ƙabilar Qashqa ke fuskanta ta kiwon dabbobin tana matuƙar kawo cikas ga 'yancin su.

Domin ana samun ƙaruwar 'yan ƙabilar Qashqai da su ke barin sana'ar su su koma cikin birni.

Asalin hoton, Pascal Mannaerts

Bayanan hoto,

Sana'ar saƙar hannu ta shahara

Shekaru aru- aru, 'yan ƙabilar Qashqai sun shahara a Iran wajen saƙar darduma da sauran kayayyaki da ake yi da auduga, kayayyakin da ake kiran su da "Shiraz" kuma nan ne babbar kasuwar da ake sayar da kayayyakin.

Audugar da ake nomawa a yankuna masu tsaunuka kusa da Shiraz na da matuƙar laushi da kuma kyau fiye da sauran audugan da ake nomawa a kasar Iran.

A yanzu, Tarkkenaz da sauran mata 'yan uwanta na saƙar kayayyaki da audugar da 'yan kasuwa ke bin su har ruga suna saye.

Asalin hoton, Pascal Mannaerts)

Bayanan hoto,

Zamani riga

Bambanci da zamani ya haifar

Matasan ƙabilar Qashqai kan nuna zumuɗi tare da sha'awar rungumar ci gaban zamani ya haifar da kuma buƙatar ƙarfafa al'adun su.

Mohammed Reza (wanda shi ne na farko a hagu a hoton da ke sama tare da abokansa), shi ne ƙarami daga cikin 'ya'yan Ghazal da Tarkkenaz, kuma ya kusa kammala horon shekaru biyu domin shiga aikin soja.

Tun da farko dai ya so ya zama makanike ne kwanda har ya ke fatan a ƙarshe ya buɗe gareji a Koohmare Sorkhi.

Babban wansa Ali Reza, ya koma birni shekaru biyar da suka gabata inda ya buɗe shagon sayar da kayan abinci ya bar iyayensa a ruga tare da dabbobin su.

Sannu a hankali sai duk aka watse aka bar Ghazal da matar sa Tarkkenaz inda suke faman neman wanda zai kula da dabbobin su.

Suna samun taimako ne daga ɗan uwan Ghazal wanda ke biyan kuɗin ga wanda ke musu kiwon dabbobi a kullum, aikin da ya kamata 'ya'yan su ne za su yi musu.

Asalin hoton, Pascal Mannaerts

Bayanan hoto,

Duniya sabuwa

A lokacin da mu ke tare da Ghazal da Tarkkenaz, ana bukin auren Qashqai a Koohmare Sorkhi.

Angon ya gayyace mu zuwa bukkar sa inda ya amince mu dauki hotonsa tare da amaryarsa, a wani yanayi da ya ce bai taɓa gani ba a rayuwarsa, kasancewar wannan shi ne karon farko daya taɓa magana da wani mutum bare.

Asalin hoton, Pascal Mannaerts

Bayanan hoto,

Kade kade da raye raye da tsarin rayuwa

'Yan kabilar Qashqai a kowane lokaci kan yi iƙirarin kasancewar su ƙabila ta musamman da al'adun su suka sha banban da sauran al'ummomi a Iran.

Koda ya ke suna bin tafarkin addinin Musulunci a tsarin auratayya, amma kuma su na amfani da lokutan bukukuwan aure domin sake jaddada al'adunsu ta hanyar kaɗe kaɗe da raye raye da nuna jarunta a fagen yaƙi da kuma tsarin yadda su ke sanya suturin su.

Haka kuma a lokutan bukukuwan ne sauran makiyaya 'yan Qashqai ke haɗuwa da juna saboda yadda galibi su ke zaune nesa da juna a rugagen su.

Asalin hoton, Pascal Mannaerts

Bayanan hoto,

Nesa da juna

Duk da kasancewar su Musulmai, kamar sauran Iraniyawa, makiyayan Qashqai ba su cika samun haɗuwa da manyan Malamai ko hukumomi na Musulunci ba.

Suna bin tafarkin addinin Musulunci wajen gudanar da bukukuwa kamar aure da mutuwa, amma 'yan ƙalilan ne daga cikin su ke yin azumi a watan Ramadan.

Tsarin rayuwar su ta makiyaya ta ba su damar ci gaba da jaddada 'yancin su a tsawon shekaru.

Wannan hoton Azal ne ɗan uwan Ghazal a irin bukkokin ƙabilar Qashqai.

Asalin hoton, Pascal Mannaerts

Bayanan hoto,

Jajircewa saboda gaba

Al'ummar makiyayan Qashqai na matukar alfahari da al'adun su, koda ya ke ba za'a iya tabbatarwa ba ko matasan da ke tasowa yanzu za su ci gaba da ƙarfafa tsarin rayuwar da iyayensu su ka ginu akai ba.

Ghazal dai na son ci gaba da rayuwa a matsayin makiyayi ta kowane hali.

"Ya ce ba zan taɓa iya zama a gidan da ya ke da bangon daki da rufin kwano ba, ai mutuwa kawai zan yi saboda rashin isasshen iska, domin kullum zan riƙa mamakin me na ke yi kuma me zai sa in zauna a wurin. Zan riƙa ji tamkar ina gidan yari ne ko kuma kamar na ci amanar iyayena da kakanni.

Mu 'yan ƙabilar Qashqai ne kuma daban mu ke da wasu ƙabilu"- in ji shi.

Idan kana son karanta wannan labari a harshen Ingilishi latsa nan: The last nomads of Iran