Kun san abin da ya sa kewar baya ke da alfanu gareku?

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Daga Tom Stafford

Ko hoto ne ya bijiro da al'amarin, ko sumbatar farko ko wata dukiya, kewa na tattare da juya akalar tunani ga lokacin faruwar lamari da wurin da ya faru.

Daukacinmu na sane da zaki da rashin jin dadin abin da ya gabata, musamman in an kawata shi da launukan furanni ko ya jika da jini a yammacin hasken rana.

Lakabin "nostalgia" - kewa, wani likitan kasar Switzerland ne ya kirkirota a shekarun 1600 don nuna zakuwar son komawa gida a tsakanin sojoji. A halin yanzu mun san cewa ta sha gaban zakuwar komawa gida (ko abin da ya shafi sojoji), idan muka kai makura a kewaya za ta iya zama tsananin sosawar zuciya ko nisan tunanin baya.

Sai dai, ta yiwu, aikinta ya sha gaban sosawar zuciya. Dimbin binciken da masanin dangantakar aikin kwakwalwa da dabi'a, Constantine Sedikides ya aiwatar na nuni da cewa kewa na iya zama madogarar da za mu dafa don kulla alaka da wasu mutane ko al'amuran da suka faru, ta yadda za mu ci gaba ba tare da tsoro ba, sai babbar manufa.

Sedikides ya samu karsashin gabatarwa daga abin da aka yi wa lakabi da Tarairayar Fargaba (Terror Management Theory TMT), wadda akalla ta kai 8,000 a daukacin jinsi (tsakanin mace da namiji) fiye da sauran nau'ukan mahangar tantance tasirin aikin kwakwalwa a dabi'u.

Ta yi nuni da cewa bukatun dan Adam a tasirin aikin kwakwalwa ga dabi'u shi ne yadda za mu tunkari abin da babu makawa sai ya faru na daga mutuwarmu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tushen wannan bin kadin nazarin tasirin aikin kwakwalwa a al'adu na Sigmund Freud, wanda ya dan sauya mahangar daga jerin fahimtar da aka samu ta zamani, inda ta karkata akalla al'amuran da ba a dauke su da kima ba, wadanda suka hada da daukar kwakwalwa kamar kwamfuta.

Sakamakon waje-gwajen da aka wallafa a shekarar 2008 sun yi amfani da managartan dabarun gwaji na Mahangar Tarairayar Fargaba: ta yarda wadanda aka bi kadin lamuransu, aka bukaci su yi tunanin mutuwarsu, inda za su amsa tambayoyi kamar cewa: "Bayyana a takaice irin sosuwar da zuciyarka ta yi da ka tuna mutuwarka."

(Wani rukunin mutanen na bijiro musu da bukatar su kaddara wa kansu jin zafin ciwon hakori da wani abu mara dadi, amma wanda babu shi a zahiri da yake barazana garesu.)

Mahangar Tarairayar Fargaba (TMT) ya yi nunin cewa daya daga cikin amsar da aka bayar kan tunanin mutuwa shi ne jajircewar gaske kan yalwar rayuwa, saboda haka bayan sun gama kawo madogararsu.

Sai aka bukaci wadanda aka bi kadin lamarionsu da su nuna amincewarsu da bayanin cewa: "Rayuwa ba ta da ma'ana ko manufa," ko "daukacin fafutikar rayuwa shirme ne da babu ma'ana."

Daga amsoshin aka kimanta wadanda aka bi kadin lamarinsu a ma'auni kan kimar matsayin tunaninsu game da ma'anar rayuwa.

Amsoshin sun tasirantu ne da kimar zakuwar mutane ga kewa. Masu binciken sun gano cewa sauran wadanda bin kadin lamarinsu game da mutuwarsu ta yiwu sun yi hakan ne saboda damfaruwar tunaninsu game da rashin ma'anarta, sai dai a jerin wadanda suka ce ba su cika yin kewar abin da ya gabata ba aka samu bambancin.

Mutanen da aka bibiyi lamarinsu an kimanta su a matsayin wadanda suka fi zakuwar kewar abin da ya gabata, kuma ba su samu matsalar jin cewa akwai mummunar illa game da mutuwarsu ba (sun kimanta rayuwa cike da matukar ma'ana, tamkar dai rukunin da aka kebe).

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Bayanan gwaje-gwajen da aka sake sun nuna cewa masu zakuwar kewayar abin da ya wuce su na karancin tunanin mutuwa, haka kuma ba su cika yin fama da kadaici ba. Kewar abin da ya wuce, a irin wannan mahangar, ya bambanta ne tsakanin nakasu da tsunduma ciki. Masu binciken sun yi masa lakabi da "ma'anar bijiro da madogara."

Muhimmin bangare a lafiyar kwakwalwa

Kewar abin da ya gabata wajen adana kyakkyawan tunani mai sosa zuciya ne, ta yadda a za mu iya kai wa ga wani abu da saninmu, kuma ta yiwu mu kulla alakar ci gaban al'amura a rayuwarmu ta yau da kullum don inganta tunaninmu.

Irin wadannan managartan nau'i mai sosa zukata game abin da ya wuce na harkokin rayuwarmu suna taimaka mana wajen kyautata dabarun tunkarar rayuwarmu nan gaba.