Mene ne zai magance mutuwar al'aura?

Na'urar "The Orgasmatron" (Stuart Meloy)

A wannan wata labarai sun bazu a duniya game da rahoton abin mamaki na dashe maballin zunguro dadin jima'i.

Na'urar Orgasmatron mallakar fasahar Dokta Stuart Meloy ce, a wani dan karamin akwati da ake soka wayarsa ta cikin jijiyar laka da ke aikewa da sakon dadi a duk lokacin da mai amfani da ita sha'awa ta bijiro masa.

Ta kan lume cikin ta yadda wannan fasaha ke bijiro da jin dadin ban mamaki.

"Kila kai ne mai neman labarai na shida ko na bakwai da ya kira ni, don haka nike mamakin abin da ke faruwa," Meloy ya fada mini cikin rudani.

Rudaninsa a bayyane yake. Ba da dadewa ba rahotanni kan na'urar sun kebanta ne a Mujallar Masana Kimiyya ta New Scientist mai shekara 13, wadda ba da dadewa bat a bazu a shafin sadarwar Reddit, wata matattarar alkinta tarihin al'amura masu ban sha'awa.

Tsawon lokaci Meloy ya sha fama wajen neman jan hankalin wadanda za su bayar da tallafin kudin kera na'urar, ba tare da ya yi nasara ba.

Meloy likita ne kuma abokin hadin gwiwar kafa babban asibitin tarairayar zafin ciwo na Advanced Interventional Pain Management, inda ake yi wa masu jin tsananin zafin ciwon magani.

A wannan cibiya ta fara aikin dashen na'urorin lantarki.

Abin da ake likawa a jijiyoyin laka zai ta tura tartsatsi a hankali, a hankali da ke dusashe matsanancin zafin ciwo.

Sai kawai a irin wannan aiki na dashe, wani majiyaci ya bayar da rahoton jin wani abu daban, amma ba mara dadi ba: na'urar ta cusa zakwadin dadi.

Meloy ya fahimci cewa managarciyar fasahar da ke hannunsa na iya zama waraka ga maza da matan da ke fama da mutuwar al'aura.

Bayan shekara 10, lokacin da Meloy ya samu nasara a likitanci, sai aikin na'urar zaburar da jin sha'awar jima'i ta Orgasmatron ta samu cikas.

Daya daga matsalolin shi ne na'urorin lantarki da ake amfani da su za su lakume kudi har Dala dubu 25 ($25,000).

Meloy na da kwarin gwiwar cewa na'urar Orgasmatron za ta iya sarrrafa makamashi kadan na sa'a guda ko wacce rana.

"Harbawa ba kakkautawa na tsawon kwanaki ba ita nike ganin za ta taimaka wajen shawo kan matsalar mutuwar al'aura ba," in ji shi.

"Wasu daga cikinmu dole su je wurin aiki. "Abin takaici babu abin da zai maye gurbinsa, kuma ya kasa jan hankalin masu kera kayan aikin likitanci su yi guda.

Sai batun biyan kudin dashen na'ura ya taso har ake tunanin wane ne zai biya. "Kamfanonin inshora ba za su biya kudin abin da ake ganin gwaji ne ba," kamar yadda ya bayyana.

Duk da haka Meloy ya yi wa daruruwan majiyata dashen na'urar don tarairayar shawo kan zafin ciwo (wasu daga cikinsu sun bayar da rahoton kyakkyawan tasiri), don haka dashenta don warkar da rashin kuzarin al'aura keta doka ne.

Duk da zuzuta labarin na'urar da aka yi har yanzu ba ta nuna managarcin tasirin warkar da matsalar mutuwar gaba ba, kuma duk wanda ke tunanin yin karyar zafin ciwo don samunta, to yana tattare da jin takaici.

Don samun amincewar Hukumar kula da ingancin abinci da magani (FDA), Meloy sai ya yi "muhimmin gwaji," al'amarin da zai ci kudi har dala miliyan shida. "Wannan shi ne kudin da ba ni da su a halin yanzu," in ji shi.

Kadarkon dadi

Abin mamakin shi ne, Meloy ba shi ba ne mutum na farko da ya yi tunanin cusa maballin dadi a jikin mutum.

A shekarun 1950, wani likitan Amurka, mai suna Robert Gabriel Heath, lokacin da yake kokarin magance matsalar kwakwalwa a sashen nazarin aikin kwakwalwa da sakon intata a Jami'ar Tulane da ke New Orleans.

Heath ya so kirkiro wani abu mai tasiri kamar goshin masarrafar kwakwalwa da ake amfani da shi wajen warkar da hauka wanda har yanzu ana amfani da shi, sannan ba shi da wata illa sosai.

Heath ya gano cewa ta hanyar farfado da mahadar hagu da damar zuciya zai iya zaburar da zakwadin dadi da ke tauye mummunar dabi'ar tashin hankali a wasu marasa lafiyar.

Kuma da zarar an bijiro musu da dadi marasa lafiyar sai su kasance cikin annashuwa.

Daya daga marasa lafiya ya kwashi tartsatsin 1,500 cikin sa'a uku, amma gaba daya sun nuna kyakkyawar samun natsuwa. (Sabanin beraye da aka kwata musu irin aikin, al'amarin da cushen a kashin kai ya kusa kai wa ga sukewa).

An samu rahoton yadda maballin bijiro da dadi na Heath ya sanya aka kawo masa ziyara daga Hukumar leken asiri ta CIA, wadanda suka so sanin ko wannan fasahar za ta iya haifar da zafin ciwo, ta yadda za su yi amfani da ita kan masu adawa da gwamnati ko su rika juya akalar kwakwalwarsu.

Sai Heath ya kori mutumin daga dakin bincikensa. "Idan ina son zama jami'in leken asiri, da na zama dan leken asiri," kamar yadda ya kwarmata wa jaridar New York Times a hirarsa. "Na fi son zama likita mai maganin cututtuka."

Wasu da suka yi zamani da Heath sun yi tunanin mummunar illar da ke tattare da karya lagon karsashin kwakwalwar dan Adam.

Jose Manuel Rodriguez Delgado, daya daga cikin masu binciken da suka gano dabarar sarrafa jin dadi a kwakwalwar marasa lafiya.

Kuma ya ware tartsasin lantarkin kwakwalwa managarciya da ake juya akalarta.

Sai dai tunanin mutane game da cushen kwakwalwa ya tsananta lokacin da ya wallafa littafinsa "Zahirin juya akalar kwakwalwa: hanyar bunkasa tunanin al'umma a shekarar 1969, inda Delgado (a iya cewa ya bayyana karara) ya kwantar da ruruwar kwarmaton salon marubuci George Orwell da aka yi wa na'urar, ya kuma karfafi gwiwar al'umma su rungumi fasahar.

Idan kowa zai amince a yi masa dashe don kawo daukin shawo kan bacin rai da jin zafin ciwo, duniya za ta kasance wuri mai dadi, a cewarsa.

Masu bincike biyu da suka dan yi aiki tare da shi sun yi kwarmaton cewa za a yi amfani da na'urar ne wajen kashe karsashin zanga-zangar bakaken fata a cikin biranen Amurka.

Sai aka daina samun tallafi, sannan bayan samun managartan kwayoyin magani da ke warkar da cutar tabin hankali, sai tartsatsin lantarkin kwakwalwa ya bace tare da dimbin akwakun bijiro da dadi.

Ko da yake Meloy shi ne mafi zakuwa kan alfanun da ke tattare da na'urorinsa, inda amfani da su ke nuni da juya akalar al'umma ba "ita ce manufar aikinsa ba."

Yana da kwarin gwiwar cewa sabuwar sha'awar na'urar "Orgasmatron" za ta sake bayar da damar tabbatuwarta.

Idan hakan ya kasance, za mu sa ran ganin maballin bijiro da dadi like a jikin mutane? Ba da wuri ba, a cewar Dokta Petra Boynton, mai bincike kan jima'i a Jami'ar Kwalejin Landan.

"Har yanzu ban ga na'urar ba da magunguna ko kayan da ke shawo kan matsalolin jima'i fiye da magungunan bakam (makwafin magani da ba na gaske ba)," a cewarta.

"Na fi damuwa da aikin kawo daukin shawo kan matsalolin da kamata ya yi a ce an magancesu ta hanyar kyautata tunani, ko bayanai kan matsalolin jima'i, da samar da makwafin jin dadi, tare da fahimtar yadda jikinmu ke aiki."

Don haka idan na'urar "Orgasmatron" ta samu shiga kasuwa, sai ka dauka kawai ka mallaki akwakun bijiro da tartsatsin lantarkin dadi mai karfi manne a kafadarka.

Ga masu son ta'ammali da wanan fasahar kirkira, kawai sai mutum ya yi kokarin sanin wanda ke rike da akalar maballanka.