Mene ne bambancin son jima'i tsakanin mace da namiji?

Mene ne bambancin son jima'i tsakanin mace da namiji? Hakkin mallakar hoto Getty Images

Makalun kimiyya kadan ne suka bayar da tabbacin cewa mutane sun yi ce-ce-ku-ce da muhawara fiye da ikirarin sanin bambancin yadda ake zaburarwar likon alakar kwakwalwar mace da namiji.

Daukacin abin da ake ta kai-kawo a kai su ne dabi'un da ke tattare da tarawar jima'i. Sai dai an sha samun hujjojin da ba su da nagarta imma har ba a yanke cewa daukacinsu shaci-fadi ne.

Haska hoton kwakwalwa da aka yi ya nuna cewa wuraren da ke lailaye da launin toka-toka "mabubbbugar farin ciki" a maza da mata ba su nuna hakikanin sassan sarrafa al'amura da ke cikin kokon kai.

Al'amarin kamar shaci-fadi ne yadda wasu masanan bunkasar kwakwalwa da ke nuni da cewa kwakwalen maza da mata dole suna da mabambantan muhimman kullin alakar, bisa la'akari da bambancin dabi'a.

Ta yiwu ka yi hasashen cewa saboda cunkoson masu tafiya makaranta da safiyar nan, sabanin jiya, tuni da an karkatar da akalar hanyar bisa dole.

Lamarin a bayyane yake ganin yadda wata makala ta bi kadin bambance-bambancen darsuwar tunkarar tarawar jima'i a tsakanin maza da mata da ke da alaka da hakikanin bazuwar tartsatsin sakonni a jijiyoyi.

Saura da me, bayan gano likon alakar da gungun masu bincike na majisalar likitanci da ke da dakin binciken kimiyyar rayuwar halittu a Cambridge da ke Ingila, al'amari ne mai sauki da ke nuni da bijirowar darsuwar jima'i tamkar kunnawa da kashewar bazuwar lantarki; ingiza jijiyoyi su fitar da sinadaran aikewa da sakonnin ankararwa ga jijiyoyi ta wata hanya ga maza, da kuma wata hanyar daban ga mata.

Abin da aka fahimta bai yi nuni da dabi'ar mutum da muke magana akai ba. Sai ma dai a ce an yanka ta tashi.

Abin da ke ingiza darsuwa da daukar al'amura bai daya a jikin wannan da waccan, lamari ne da masu bincike suka yi takatsantsan wajen kauce masa, ko da yake sun yi kwatanceceniya da jaba.

Misali kamar yadda aka fitar da su ta yadda za su dauki hankalin abokin Barbara ko tantance cewa abokin hadin Barbara shi ne na hakika.

Daukacin batutuwan shahararrun mujallu, abin mamakin shi ne, duk abin da suka yi nuni da shi kadan ne aka gano game da sinadaran aikewa da sakonnin tarawar jima'i a mutum.

Sinadarin "steroid androstenone" da ake ce yana daukar hankalin mata idan maza suka fitar da shi, kuma yana ankarar da maza cewa kwayayen mata na bukatar kyankyasar maniyi, amma dai babu wata kakkwarar hujja kan haka.

Mun fahimci cewa dai sakon ankararwar sinadaran tarawarar jima'i ba shi da makama. Akwai wani sinadari na musamman da ake yi wa lakabi da cVA (11-cis-vaccenyl acetate) da ke da maganadisun jawo macen kuda su yi ta soyayya, al'amarin ya hadar da waka da rawa daga nan kawai sai su hada baki da al'aura.

Amma a jikin maza sinadarin cVA tasirin aikinsa akasin haka ne; tauye soyayya, a wasu lokutan ma yakan harzuka musu tada jijiyar wuya, al'amarin da ke nuni da gasar namiji.

Kulla alaka

Abin tambaya a nan shi ne ko mene ne ke haifar da mabambantan salon tunkarar lamarin. A wasu daya daga cikin jinsunan ne ke yin "warin sinadarin jan hankalin jima'i," saboda yana da managarciyar makarbiyar sinadaran protein da ke shigar da sinadarin ankararwar.

Sai dai akai-akai, sinadarin cVA, wanda ke bijiro da darsuwar dabiar son jima'i a maza da mata irin guda ne, don haka za su iya gano shi, tare da 'fahimtar' sauye-sauyen salonsa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ayyukan binciken da suka gabata bambanci kadan suka nuna a tsakanin maza da amta, inda daukacin tartsatsin sakonnin mafi akasari nan take da zarar sinadarin cVA ya bijiro da shi, sannan sakonnin kan yi juyin sadarwa (karo na biyu a tunkudowar tartsatsinsu).

Gregory Jeffens da abokan aikinsa a Cambridge sun gano bambancin da ke tattare a matakin tartsatsin sakonni na gaba wato juyin sadarwa na uku. Bambanci na da ban mamaki kai tsaye; wadannan tartsatsin sakonni kullin alaka ne a hanyoyi daban-daban, wadanda ke ankararwa a wani sashe na kwakwalwar kuda (mai zukar furanni), sabanin turakun tafiyar tarragon jirgin kasa mabambanta.

Samun irin wadannan bayanai na tattare da aiki na kwarewa da jajircewa wajen gwaji a fannin kimiyyar kai-kawon sakonnin jijiyoyi a kwakwalwa.

Masu bincike sun hada hotunan mitsi-mitsin kwakwalwar kuda, al'amarin da ya yi nuni da raunin hanyoyin tafiyar sako guda, wanda ke "juya akalar" ma'aunin tafiyar tartsatsin sakonni a zirin silin jijiya.

Ta haka ne za su iya gano sashen ankararwa a kwakwalen namiji da mace, sannan a nuna bambancin da ke tsakaninsu bayan sun kai ga juyin sadarwar sakonni karo na uku.

Wadanne al'amura suka haifar da bambancin alaka? Jefferis da abokan aikinsa sun danganta ala'amarin da kwayar halitta guda, da ake kira "fruitless - mara-katabus," wadda masana kimiyya suka san cewa tana da muhimmanci a dabi'ar namiji.

Kwayar halittar ke tattare bayanai game da sinadaran proteins, sannan masu bincike sun nuna cewa samar da wadanann sinadaran proteins a juyin sadarwar sakonni mataki na uku shi ke kulle su a tsarin kwakwalwar namiji.

Da masu binciken suka jirkita wadannan tartsatsin sakonni a kwakwalwar mace sai aka samar da sionadaran proteins, kuma kwakwalwar mace ta kulla alaka da su tamkar ta namiji.

Shin juya wannan gudan sakon sadarwar ya isa yin tasirin sanya mace ta darsu da salon matakin namiji ga sinadarin cVA?

Saura dai a jira a gani, kuma ta yiwu irin wanan juyin-juya halin jinsi na bukatar Karin wasu "su juya irin na namiji" a samu kwaranyar sinadarin darsuwar jima'i.

Amma abin takaici ne a ce a kalla kan al'amarin da ya shafi tarawar jima'i, akwai al'amura karara game da bambancin da ke damfare a tsakanin kwakwalwar namiji da mace.