Yadda yawan ciwon kai ke jawo mantuwa da rudin kwakwalwa

Lamarin ya auku ne ga Paul lokacin hutun zafi Hakkin mallakar hoto (Credit: iStock)
Image caption Lamarin ya auku ne ga Paul lokacin hutun zafi

Shekara biyu da ta wuce, Paul Bolding mai shekara 63 ya yi hutu a Croatia, inda ya ziyarci gabar kogi a wani karamin tsibiri tare da matarsa Kirsty.

Sai suka yanke wa kansu yin ninkaya da bututun shakar iska, inda suka rika yin juyi, wannan ya shiga wannan ya fita ya kula musu da kayansu.

Paul ya yi kurme sai barci ya kwashe shi a kan tabarmar gabar teku da ke shimfide kan kananan duwatsu na wani lokaci. Da farkawarsa bai san inda yake ba, ko ya aka yi ya iso wurin.

Babu mamakin jin cewa Paul ya firgita. Matarsa ta kai shi inuwa, inda ta zaku da ganin cewa ta kwantar masa da hankali ya samu natsuwa don warware matsalar da ke tattare da shi.

Ta bayyana mini a wani shirin rediyo mai taken daukacin al'amuran tunani (All in the Mind) cewa, ta gano cewa bai zai iya tuna komai ba, domin tambayoyi iri guda yake ta yi.: Kina jin zafi ne ya baibaye ni? Kina jin cewa na yi barci a rana ne?" Al'amarin da ya yi ta faruwa kenan fiye da sau 20.

Ya kasa tuna al'amuran da suka faru kwana 10 da suka yi na hutunsu.

Kirsty na ta kai-kawo a tunani cike da dar-dar jin cewa ko ya kamu da cutar mantuwa. Taraddadin cewa ko za ta shafe tsawon rayuwa tana kula da shi, sai ta dawo da shi garin da suke zaune, cike da fatan ganin al'amuran da ya saba da su ko za su dawo masa da tunaninsa.

Ita ta rika karbo masa abincin rana domin bai ma san abin da yake so ba. Ya kasa tunani kwana 10 da suka gabata na hutunsu, duk da cewa wasu al'amuran sun shaf ganawa da wasu 'yan uwa a karo na farko.

Can tsakar rana sai ya fara warwarewa, al'amarin da ke nuni da cewa ya shirya yin tattakin da suka tattauna yinsa kafin wannan rana, wato dai ya fara tuna al'amura. Cikin sa'a guda ya dawo garas yadda yake - komai ya yi daidai ba ya ga mantuwar sa'a shidan da ya yi, al'amuran da har zuwa yau ba su dawo ba.

Da komawarsa gida Birtaniya sai ya ziyarci likitansa, wanda ya fada masa cewa ya ratsa bagiren duniyar mantuwa, wani lamari da ya saba shafar mutanen da shekarunsu suka dara 50 (kamar Paul).

Sashen kula da hadurra da kulawar gaugawa a asibiti na ganin mutum biyu zuwa uku wadanda suka auka cikin matsalar a ko wanne wata.

Lokacin aukuwar lamarin, mutane na sane da yadda ake tuki da tafiya, amma a matsala irin ta Paul ba za su iya tuna abubuwan da suka kasance suna yi a kwanakin da suka gabata ba.

Yawan maimaita tambayar wasu, kamar yadda Paul ya yi a gabar teku, nan ne jigon warware matsalar.

Sashen kula da hadurra da kulawar gaugawa a asibiti na ganin mutum biyu zuwa uku wadanda suka auka cikin matsalar a ko wanne wata.

Har yanzu musababbin matsalar bai bayyana ba.

Da farko likitoci na tsammanin irin wannan farmakin alama ce ta farfadiya ko rabin ciwon kai, ko ta yiwu an dan samu sandarewar gabban jiki.

A halin yanzu an tabbatar lamarin ba shi da alaka da sauran matsalolin rashin lafiya.

An yi hasshen cewa dunkulen sashen kwakwalwa da ke sarrafa tunani ne ke da alhakin tattara bayanai na tsawon lokaci, don haka ake ganin shi ne jigon shawo kan matsalar.

Hakkin mallakar hoto (Credit: iStock)
Image caption Illar matsalar na iya yin muni har ta kai ga mutane sun manta da kansu

Adam Zeman, Farfesan massarafar tunani da matsalolin kwakwalwa a Makarantar horar da Likitoci a Jami'ar Exeter ya yi nunmi da cewa: "abin da ake tsammanin yana faruwa shi ne masarrafar tunani (hippocampi) ke kullewa na wucin gadi.

Abin da ya faru ga Paul fitacce ne. Za ka manta abin da ya faru makonni da suka wuce, kuma ba za ka iya tuna sababbin al'amura lokacin da matsalar ke ci gaba ba.

Nazarin hoton kwakwalwa ya inganta wannan mahangar, inda aka gano matsalolin wucin gadi tattare da masarrafar tunani yayin aukuwar matsalar.

Mutanen da suka saba fama da yawan ciwon kai su suka fi yawan fama da matsalar.

Da ka bibiyi kadin al'amuran daidaikun mata 142, wadanda suka ratsa bagiren duniyar mantuwa, likitocin Faransa sun gano cewa, irin wadanan matsalolin dugunzumar damuwa ke haifar da su, al'amuran da suka hada da takaddamar muhawara, yayin da maza kuwa sun fi samun nasu ne lokacin da suke fama da matsin lamba ko nutso a ruwan sanyi.

Mutanen da suka saba fama da yawan ciwon kai su suka fi yawan fama da matsalar.

Hakkin mallakar hoto (Credit: iStock)
Image caption Cutar na nufin mutane na iya mantuwar sa'o'i ko kwanakin rayuwarsu har abada

Akai-akai, mutanen da ke fama da matsalar na da bambancin yanayin da ake kira ratsa bagiren farfadiyar mantuwa, wanda ake dauka cewa shi ne ratsa bagiren duniyar mantuwa, amma irin wannan farfadiyar.

Lamura ne na wucin gadi da ke faruwa akai-akai, da zarar an tayar da mutum daga barci.

Zeman ya ce a mafi yawan lokuta warware matsalar cutar na da sauki: "Idan ka ga wani bayan aukuwar lamarin, kuma suka bayar da bayani irin na Paul, to babu tababa a ciki.

"Idan ka hadu da su a tsakiyar aukuwar lamarin, to sha'anin na da matukar wahala, don haka sai ka yi tunanin farmakin wasu matsalolin da suka hada da sandarewa ko shanyewar gabobin jiki da farfadiya ko rudanin mantuwa."

Babban bambancin da ke tattare da rudanin mantuwa shi ne majiyyatan ba sa iya tuna kansu, amma za su iya tuna sababbin al'amura.

Kyakkyawan batu game da matsalar ratsa bagiren duniyar mantuwa shi ne, lamari ne da ke faruwa a rudanin kwatsam ba tare da nuna alamar wasu cutttuka ba.

Sai dai kaso kadan ne daga cikin wadanda suka yi fama da yanayin za su sake kwata makamancinsa. Amma idan ya faru gareka, tabbas zai iya zama lamari mai tsananin firgitarwa.

Paul ya yi fatan ka da lamarin ya sake aukuwa har abada. Sai dai idan ya auku, to Kirsty na da masaniya kan ko mene ne.