Bambancin tunanin al'umma a Gabashi da Yammacin duniya

Hokkaido

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin da Horace Capron ya fara kutsawa Hokkaido a shekarar 1871, ya duba duk wata alama da za ta nuna an taba rayuwa a kan manya-manyan falalen tsaunuka, ga dazuka da duwatsu masu ban tsoro.

"Wannan wuri mai kyakkyawan yanayi da ban sha'awa ya mutu murus," kamar yadda ya rubuta daga bisani. "Ko karar fadowar ganyen bishiya bai ji ba, balle kukan tsuntsu ko wani rayayyen abu."

Yana jin cewa wuri ne da ba za a kimanta lokacinsa (zamaninsa) kai tsaye kafin tantance tarihi ba.

"Ta yaya lamarin ke cike da ban mamaki cewa wannan kayatacciyar kasa mai dimbin arziki, mallakin tsohuwar kasa mafi yawan al'umma a kasashen duniya… za ta kasance tsawon zamani fayau tamkar ba a taba zama ba, kusan a ce ba a san da ita ba, kamar hamadar Afirka," in ji shi.

Wannan kan iyakar kasar Japan ce, kuma kwatankwacin "Yamutsin Yammaci" irin na Amurka. Can cikin Arewacin tsibiran Japan Hokkaido ta kasance a kungurmin daji mai nisa, inda teku ya tumbatsa ya shata iyakarta daga Honshu.

Mafiyan da kan bugi kirji su yi kasadar shiga su tsallaka sai sun jure wa matsanancin sanyi da rugugin aman wutar tsauni da miyagun namun daji. Don haka Gwamnatin Japan ta kyale wurin dungurungum ga 'yan asalin wajen kabilun mutanen Ainu, wadanda ke rayuwa ta hanyar farauta da su.

Lamarin ya sauka a tsakiyar karni na 19. Jin tsoron farmaki da mamayar Rashawa, sai Gwamnatin Japan ta sake mallake Arewacin kasarta, inda ta tura mayakan gargajiya na Samurai suka tare da Hokkaido.

Ba dadewa ba wasu suka biyo su, inda aka bude gonaki da tashoshin jiragen ruwa da hanyoyin ababen hawa da titunan jirgin kasa aka bunkasa su, suka karade daukacin tsibirin.

Masana harkokin noma irin su Capron an jawo don su bai wa sababbin mazaunan yankin shawara kan yadda ya dace su yi noma a wurin, ta yadda cikin shekara 70 al'ummar wurin ta tumbatsa daga dubbai kadan zuwa fiye da miliyan biyu.

Da aka shiga sabon karni, adadin ya nunnunka zuwa miliyan shida.

Asalin hoton, Credit: Getty Images)

Bayanan hoto,

Kafin sarki Meiji ya tura mutane su cika tsibirin, asalion mutanen da ke zaune a Hokkaido kabilar Ainu ne

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kafin sarki Meiji ya tura mutane su cika tsibirin, asalin mutanen da ke zaune a Hokkaido kabilar Ainu ne. Ta yiwu irin tsirran da kakannionmu (magabatanmu) suka shuka ke juya akalar tunaninmu.

Mazaunan Hokkaido kadan ne a yau suka taba tunanin mamayar kungurmin daji a kashin kansu.

Duk da haka masana tasirin kwakwalwa kan dabi'u sun gano cewa ruhin kan iyaka na nan damfare a tunaninsu, yadda suke ji da hankalinsu in an kwatanta da mazaunan Honshu wadda kawai ba ta wuce nisan kilomita 54 (mil 33) daga wurin.

Sukan killace kansu, suna masu alfahari da nasararsu, masu matukar burin bunkasar ci gaban kashin kansu, kuma ba su cika gwamuwa da mutanen da ke kewaye da su ba.

A gaskiya, idan ana kwatanta kasashe, yanayin wadannan mutane ya fi kusa da na Amurkawa fiye da sauran mutanen Japan.

Labarin Hokkaido daya ne daga jerin binciken da aka gudanar na bibiyar yadda zamantakewaar al'umma a muhallinsu ke juya akalar alkiblar tunaninsu.

Daga nazari mai fadi kan bambance-bambancen da ke tsakanin Gabashi da Yammaci, don saukaka bambancin jihohin Amurka, al'amura na bayyana karara cewa tarihi da yanki da al'ada na iya sauya yadda muke tunani, kuma hanyoyi mafi ban mamaki har sun karade mahangar fahimtarmu.

Za a iya juya akalar alkiblar tunaninmu sanadiyyar irin tsiron hatsin da magabatanmu suka shuka a gona, kuma kogi guda na iya gindaya iyakoki tsakanin tsarin rayuwar mabambantan al'ummomi masu tunani daban-daban.

A duk inda muke zaune, al'amuran da ke farkar da mu za su iya taimakawa wajen tursasa karfin tasirin fahimtar tunaninmu da kyau.

Tunani na "daban"

A da masana kimiyya ba sa la'akari da bambancin tunanin al'ummar duniya. Cikin shekarar 2010 tasirin makalar da ta bayyana a mujallar fannonin Kimiyyar Tantance Tasirin Dabi'u da aikin Kwakwalwa ta ruwaito cewa mafi yawan darussan nazarin kwakwalwa duk na "Yammacin Turai ne cike da ilimi da bunkasar masana'antu da arziki da dimokuradiyya," ko "mai ban mamaki kadan.

Kusan kashi 70 cikin 100 na Amurkawa, wadanda mafi yawansu dalibai ne da ke karatun digiri da ke sa ran samun kudin kashewa ko makin darasin aji ta hanyar sarayar da lokacinsu wajen shiga wadannan gwaje-gwajen.

Abin da kawai za a iya kaddarawa shi ne wadannan rukunin mutane za su iya wakiltar hakikanin lamarin yanayin dan Adam cewa daukacin mutane daya suke.

Idan har hakan gaskiya ne son ran Yammacin Turai ba shi da wani muhimmanci. Duk da haka dan binciken da aka gudanar wanda ya yi nazarin al'adun wasu mutane zai nuna cewa wannan ba matsala ba ce.

"Mutanen Yammacin Turai musamman Amurkawa su ne a karshen karkasuwa," a cewar Joseph Henrich na Jami'ar British Columbia, daya daga cikin marubutan binciken.

Asalin hoton, (Credit: Alamy)

Bayanan hoto,

Yawan al'ummar Hokkaido ya habbaka daga dubbai zuwa miliyan shida adadin mazaunan a yau

Wasu muhimman bambance-bambancen da ke tattare da "daidaitar daidaiku" da "tattaruwa," ta yadda ko ka dauki kanka a matsayin mai cin gashin kai da ya tsayu a kashin kansa.

Komai tarewa da haduwa da sauran jama'ar da ke kewaye da kai, inda kake fifita taruwa kan kadaitaka.

Daukacin al'amuran za a ce akwai da dama da suka kebanta - mutanen Yammaci sun fi zama su kadai, inda mutanen kasashen Asiya irin su Indiya da Japan da Sin suka fi zama a tare cikin jama'a.

Da aka tambayi Farfesoshin Amurka kan cancantarsu, kashi 94 cikin 100 sun yi ikirarin cewa "sun fi matsakaita' wata alama da ke nuni da kamba kai.

Al'amura da dama, sakamakon a bayyane yake kamar yadda kuke zata. Idan aka yi tambaya kan dabi'u da halaye, mutanen da suka kadaita kansu a al'ummar Yammacin Turai sukan kimanta nasarar kansu a kan abin da rukuninsu ya cimmawa, al'amarin da ke nuni da kambama kai da neman farin ciki a kashin kan mutum.

Sai dai wannan zakuwar nuna kimar kai tana bayyana ne a inda ake da kwarin gwiwa fiye da kima, inda gwaje-gwaje da dama suka nuna mutane na daban da suka shiga jerin wadanda aka bibiyi kadin lamarinsu akwai yiwuwar su fi kimanta matsayinsu.

Damfaruwa da son kanbama kai kusan a iya cewa babu ita a daukacin binciken da aka gudanar a daukacin fadin Gabashin Asiya; a gaskiya ma a wasu nau'ukan wadanda aka bibiyi kadin lamarinsu sun ma fi damfaruwa da kaskantar da kimarsu fiye da daga darajar kansu.

Mutanen da al'ummarsu ke zaune a matsayin daidaiku su kan bayar da muhimmancin zabin abin da suke so a kashin kansu cikin 'yanci.

Asalin hoton, (Credit: Getty Images)

Bayanan hoto,

Tunanin al'umma dungurungum ya kanainaye Falsafar (mahangar tunani) da al'adun Gabashi

Muhimmin abu shi ne tarbiyyarmu na iya kai wa kan muhimman al'amuran tunani da ake bi na hankali.

Mutanen da al'ummarsu take a tare (wuri guda) sun yi tunani na gaba daya, ta yadda tunaninsu zai bijiro da dabarun shawo kan matsaloli, inda suke mayar da hankali kan dangantakarsu da yanayin da ya faru, yayin da mutanen da ke zama kebe su kadai sun fi mayar da hankali kan daidaikun al'amura, inda suke la'akari da cewa yanayi na nan yadda yake babu sauyi.

Misali a saukake shi ne, ka kaddara cewa ka ga hoton wani dogo yana cutar da dan karami. Ba tare da neman wani bayani ba, mutanen Yammacin Turai za su dauka kawai wannan wani muhimmin al'amari da dabi'ar babban mutum da ba ta sauyawa; ta yiwu mugun mutum ne.

"Sai dai in tunanin al'umma gaba daya kake yi za ka yi tunanin cewa akwai wani abu a tsakanin mutanen, ko ta yiwu babban mutumin maigidansa ne ko mahaifinsa," a cewar Henrich.

Irin tarbiyyar zamantakewarka na iya sauya yadda kake kallon al'amura.

Kuma irin wannan tunanin na iya fadada zuwa kan yadda muke rarrabe abubuwa marasa rai gida-gida.

Ka kaddara an ce ka kawo sunayen abubuwa biyu masu alaka da juna a jerin kalmomin da suka hada da 'jirgin kasa da bas da titin tarragon jirgi."

Me za ka ce kan hakan? Wannan dai an santa a matsayin "gwajin dacen daidaito," tun da sun danganta ne kan alaka tsakanin abubuwa biyu kuma daya na da muhimmanci ga aikinn wani.

Za ta iya sauya yadda kake kallon al'amura. Wani binciken yadda ido ke gani da Richard Nisbvett na Jami'ar Michigan ya gudanar ya gano cewa wadanda aka bibiyin kadin lamarinsu daga Gabashin Asiya suna iya shafe tsawon lokaci suna kallon gefen zane , inda suke nazarin yanayi.

Yayin da mutanen Amurka kuwa za su iya shafe tsawon lokaci suna nazari abin da hoton ke nufi. Abin sha'awa shi ne bambanci kuma zai iya bayyana a zane-zanen yara daga Japan da Canada, inda yake nuni da cewa mabambanta hanyoyin fuskantar al'amura suna bayyana tun a kananan shekaru.

Idan muka tarairayi mafuskantar da muka mayar da hankali a kai, wannan tsukukun ko bambancin kai tsaye kacokam zai tabbatar abin da muke iya tunawa kan wani lamari da ya auku wata rana.

"Idan kanmu muke gani, to muna fuskantar wani abu daban, don haka muna cikin duniya daban-daban," in ji Henrich.

Asalin hoton, Mike Kemp

Babu wani abu da ya raba mabambantan al'adu biyu kai tsaye game yadda ake tunani, kuma mutanen da suka yi kaura daga al'ummomin za su iya sajewa da nau'ukan tsarin tunane-tunanen.

Ko da yake wasu mutanen na ikirarin cewa tarbiyyar zamantakewarmu tana nan damfare a kwayoyin halittarmu, har zuwa yau hujja na nuni da cewa ana koyo ne daga wasu.

Alex Mesoudi na Jami'ar Exeter ba da dadewa ba ya yi nazarin tsarin tunanin Iyalai 'yan Bangladesh mazaunan Gabashin Landan. Ya gano cewa a amtakin farko, 'ya'yan wadanda suka yi kaura zuwa kasar sun fara daukar dabi'un cin gashin kai na daidaiku a bayyane, sun kuma daina yin tunanin al'umma dungurungum.

Yadda suke amfani da kafafen yada labara ya fi zama babbar manuniya kan sauyin da aka samu. "Ya fi zama muhimmi fiye da koyarwar makaranta in ana bayanin sauyin."

Shin ya aka yi ma mabambanta tsare-tsaren tunani suka bijiro tun farko?

Lamarin da yake karara kawai suna tafiya ne kan doron falsafar (alkliblar tunani) da ta kankane, wadda tasirinta ya bayyana a kowane yanki tsawon zamani.

Nisbett ya yi nuni da cewa masana Falsafa a Yammacin Turtai na jadadda muhimmancin 'yanci da cin gashin kai, inda su kuma a al'adun mutanen Gabashi irin su Tao ko al'adar mutanen kasar Sin da suka mayar da hankali kacokam kan hadin kai.

Falsafar Confucius (na Sin) alal misali ya jadadda "nauyin da ya rataya kan sarki da talakawansa, na iyaye a kan 'ya'yansu, na miji a kan matarsa, tsofaffin akan matashin dan uwansa da kuma tsakanin aboki da aboki."

Wadannan mabambanta fuskokin hangen duniya na damfare a adabin al'ada da tsarin iliminta da harkokin siyasa, don haka ta yiwu a dan yi mamakin cewa wadannan al'amura sun zama jiki, inda suke yi tsirin tarairayar muhiumman al'amuran daake tunani a akai.