Yadda nau'ikan hatsin noma ke da tasiri a tunanin al'umma

Lamarin da ke kan gaba

Asalin hoton, Getty Images

Maraba da zuwa duniyar mutane. Mutane na daban ne bisa la'akari da iya zamansu a muhallinsu ta yadda za su samu damar gina tushen rayuwa tun daga turakun Arewaci zuwa Hamadar Sahara.

Wannan makalar ita ce ta farko kan Duniyar Mutane, a wani jerin makalun BBC da ke bayanin hangen makomar gaba ta hanyar amfani da dabarun kimiyyar zamani don bin kadin mabambantan al'amuranmu.

Lamarin da ke kan gaba

Ka dauki Amurka a matsayin al'ummar da ke zaune a daidaiku a daukacin kasashen yammacin Turai.

Masana tarihi irin su Frederick Jackson Turner tuni suka yi takaddama kan cewa fadada a kutsawar cikin Yammacin Turai da aka fara yi shi ya tabbatar da bunkasar ruhin cin gashin kai, ta yadda kowane karonbatta da yaki da wasu suka fafata sun yi ne don tsiran kansu.

Bisa la'akar da wannan mahanga, binciken baya-bayan nan kan tsarin tunani ya yi nuni da cewa jihohin da ke gabar gaba-gaba (irin su Montana) sun kasancewa masu zamantakewar daidaikun al'umma.

Don tabbatar da "mahangar zamantakewar sa-kai," sai masanan da ke tantance tasirin kwakwalwa kan dabi'u suka yi nazari karo na biyu kan cin gashin kai, a matsayin binciken da ya ci karo da wancan (na farko).

Masana aikin gona 'yan Amurka irin su William S Clark su suka taimaka wajen zaunar da al'ummar Hokkaido. "Yara a kara kwazo" al'amarin da ke nuni da tarbiyyar tunanin da da ta kawo zuwa yau

Wannan dalilin ne ya sanya Hokkaido ke da ban sha'awa. Tamkar mafi yawan kasashen Gashin Asiya, Japan gaba dayanta jama'arta sun zama a tattare, tqre da yin tunani irin na al'umma dungurungum.

Duk da haka yawan yin kaura zuwa yankin arewaci ya kawata yadda ake rige-rigen komawa Arewacin Amurka; gwamnatin Sarki Meiji ta dauki masana aikin gona 'yan Amurka, irin su Horace Capron don su taimaka wajen noma kasar.

Idan mahangar tarewar sa-kai ta yi daidai, to wadanda suka fara tarewa a wurin da tuni sun yi noma mai yawa a Hokkaido na kashin kansu, in an kwatanta da sauran kasar.

Asalin hoton, Sean Pavone / Alamy Stock Photo

Bayanan hoto,

Hokkaido ta fita daga tsohon tarihinta na karkarar kan iyaka, amma dai mazaunanta na damfare da wasu dabi'u na daban

Tabbas Shinobu Kitayama na Jami'ar Michigan ya gano cewa mutanen Hokkaido suna bayar da fifikon muhimmanci kan cin gashin kai da nasara ta kashin kai da damfaruwa da alfahari fiye da sauran Japanawan da suke sauran tsibiran, kuma ba su damu da ra'ayin sauran ba.

Mutanen da aka bibiyin kadin lamarinsu an kuma an bukaci su yi gwajin tunanin zamantakewa, inda aka ce su tattauna kan 'yan wasan kwallon ragar baseball masu amfani da kwayoyin sanya kuzari.

Japanawan da ke sauran tsibiran sun fi kasancewa masu la'akari da tursasar son smaun nasara, su kuwa Japanawan Hokkaido masu daidaikun al'umma, sun fi kusa da tsarin rayuwar Amurkawa a amsoshinsu.

Mahangar kwayar cuta

Wata mahangar da ta ci karo da bijirowar basira ita ce kwatanta naui'ukan trunanin na bijirowa tamkar kamun kwayoyin cuta.

A shekarar 2008, Corey Fincher (na Jami'ar Warwick) da abokan aikinsa sun yi nazarin bayan da aka tattara kan annobar da ta far wa duniya, inda suka raba sassa tsakanin zamantakewar daidaikun al'umma da wadanda suke a tare, inda suka duba alakarsu da yadda cututtuka ke yaduwa; wadanda suke a tare sun fi kamuwa da cuta, sanan wadanda suke a daidaiku ba su cika kamuwa ba.

Wannan 'yar bibiyar dabara da aka bi ta yi nuni da cewa zaman tare ya fi daidaita al'umma a dabi'u da girmama sauran, yana kuma iya sanya mutane su farga wajen kauce wa dabi'un da ka iya yada cututtuka.

Lamarin da wuya a ce alakar zahiri da ta bayyana ba wasu dalilai suika haifar da ita ba, wadanda suka hada yawan dukiyar al'ummar kasam, amma gwaje-gwajen dakunan bincike sun fito da wata mahangar wato lokacin da masana kwakwalwa suka cusa wa mutane tsoron cututtuka, inda sukan karke da tunanin al'umma gaba daya, kan al'amuran da suka hada da daidaito a hade game da dabi'un al'umma a dunkule.

Sai dai ta yiwu muhimmin abin mamaki a wannan mahangar ya fito ne daga gona. Thomas Talhelm na Jami'ar Chicago bad a dadewa ba ya bibiyi kadin lamarin mabambantan gundumomi 28 a kasar Sin, inda ya gano cewa alkiblar tunanin ta tasirantu da noman da ake yi a yankin.

Talhelm ya ce yanayin da ya samu kansa a kasarsa ta zaburar da shi yin aikin. Lokacin da ya kai ziyara Arewacin Beijing ya gano cewa baki sun fi hadin kai. "Idan ina cin abinci ni kadai mutane kan zo su yi mini magana" Sabanin yadda wadanda ke zaune a birnin Kudanci na Guangzhou ke dari-dari da tsoron yin wani abu ba daidai ba.

Girmama wasu da suke yi na nuni da alamun tunanin zaman tare, don haka Talhelm ya far amamakin da tunanin banbkado al'amuran da ke tattare da nau'ukan dabi'u biyun. Bambance-bambance ba su da alaka da yawan dukiya ko ci gaban zamani, amma ya lura da daya bambancin bai rasa nasaba irin hatsin da ake nomawa a yankin; shinkafa ta fi yawa a Kudanci, inda alkama ta fi yawa a Arewaci. "Kogin Yangtze ya raba su," a cewar Talhelm.

Noman shinkafa na matukar bukatar hadin kai: aiki ne mai wahalar gaske da ke bukatar tsare-tsaren ayyukan noman rani da zai karade gona daban-daban. Shi kuwa noman alkama in an kwatanta rabin kwatankwacin irinj wannan aikin yake bukata, kuma ya dogara kacokam kan ruwan sama fiye da na noman rani, al'amarin da ke nuni da cewa ba sai makwafta sun taimaka wa juna ba, za su iya fuskantar noman hatsinsu kawai.

Asalin hoton, STRINGER

Bayanan hoto,

In an kwatanta da sauran nau'ukanj aikin gona, noman shinkafa na matukar buatar tallafin juna a cikin al'umma, tare da ban ruwan rani da zai kewaye dimbin gonaki

Amurkawa sun fara tattaruwa da yawa.

Ko wadanan bambance-bambancen na nuni da tunanin zaman tare ko killacewar daidaiku a cikin al'umma?

Aiki tare da masan a kimiyya a kasar Sin, Talhelm ya bibiyi kadin lamarin dalaibai 1,000 a sassan da ake noman shinkafa da na alkama, ta hanyar gwajin dacen daidaito da tunanin al'umma dungurungum.

Sannan sun bukaci mutane su zana wani fasali da ke nuni da dangantakarsu da abokansu da abokan hulda; mutanen da ke zama a daidaikunsu sun fara tattaruwa fiye da abokansu da ke zaman tare da ke kokarin ganin kowa ya zauna a wuri iri guda. "Amurkawa sun fara tattaruwa da yawa," in ji Talhelm.

Tabbas mutanen da ke zaune a yankunan da ake noman alkama sun fi zama daidaikunsu, yayin da mutanen da ke yankunan da ake noman shinkafa sun fi taruwa wuri gida, su yi tunanin al'umma gaba dayanta kacokam.

Wannan ya kasance gaskiya a kan iyakokin mabambantan yankunan. ""A nan mutanen da ke yankunan karkarar kusa, amma daya na noman shinkafa, dayan kuwa alkama, kuma har yanzu ana samun bambance-bambance a tsakaninsu."

Tuni ya yi gwajin wannan hasashe nasa a Indiya, al'amarin da ya nuna karara bambancin da ke tsakanin yankunan da ake noman alkama da na shinkafa, inda aka samu sakamako iri daya.

Kusan daukacin mutanen da ya tuntuba ba aikin noma suke yi kai tsaye, tabbas tarihin al'adun yankunsansu har yanzu suna da tasirin juya akalar alkiblar tunaninsu. "Akwai tujiyar da ake samu a cikin al'ada."

Asalin hoton, Mike Kemp

Lura da mahangar tunani

Yana da muhimmanci a jadadda cewa wadannan al;'amura da suka bayyana karara sun karade dimbin mutane; akwai mataki-maki ga kowace al'umma da aka yi nazarinta.

"Manufar da ke nuni da cewa baka ce ko fara tun daga tushen nazarin al'ummar ba zai yi tasiri ba," a cewar Delwar Hussain, wani mai nazarin harkokin dan Adam a Jami'ar Edinbirgh, wanda ya yi aiki tare da Mesoudi wajen bibiyar kadin lamarin 'yan asalin Bangladesh da ke zaune a Birtaniya.

Hussaini ya yi nuni da cewa akwai dimbin alakar tarihi tsakanin qasashen Gabashi da Yammaci da ke nuni da cewa wasu mutane na bin bagiren daukacin nau'ukan tunanin biyu, inda ake ganin al'amuran da suka shafi shekaru da matakin rayuka suna da tasiri kan hakan.

"Tun bayan da Hernrich ya wallafa makalar bincikensa kan 'ban mamakin' son rai, tare da cewa amsar da ya samu mai nagarta ce.

Ya yi matukar gamsuwa da jin cewa sauran masu binciken irin su Talhelm sun fara gudanar da babban aiki a wajen kokarin fahimtar mahangar tunane-tunane mabambanta.

"Ko kana son bayanin kan mahanga da ke nuni da dalilin da al'ummomi mabambanta na da tsarin tunani daban-daban.

Duk da kyakkyawar manufa da ake da ita , ci gaban bincike ya samu tsaiko.

Domin lokaci da kudi na da alfanu wajen tabbatar da nau'ukan tunani a daukacin fadin duniya, inda mafi yawan binciken har yanzu ke bin kadin lamuran mutane masu ban mamaki sabanin manyan bambance-bambance da ke tsakaninsu.

"Mun samu daidaito kan rashin lafiya. Abin tambaya shi ne ina za a samu mafita"