Yadda kalamanka ke cutar da dabi’arka a boye

Masu sakin jiki irin su Abraham Lincoln an fi jin muryarsu da yawan hira fiye da mu (Credit: Getty Images)

Asalin hoton, Credit: Getty Images)

Bayanan hoto,

Masu sakin jiki irin su Abraham Lincoln an fi jin muryarsu da yawan hira fiye da mu

Idan ka saurari tattaunawa a cikin bas, ko kana jin za ka iya tantance kimar mutuntakar mutanen da ke hira bisa la'akari da kalmomin da suka yi amfani da taken batun da suke tattauna a kai?

Ya za ka ji idan na nusar da kai wani gajeren labari? Ko za ka iya gano wani abu game halayyar marubucin da harshensa?

Akai, akai a kan tunantar da mu "yi takatsantsan wajen zaben kalmominku" sai dai al'amura na nuni da cewa kalmomin a kashin kansu na iya bankado al'amura da dama fiye da abin da muke kokarin furtawa.

Akwai dumbin hujjoji da ke nuni da cewa mutuntakarmu rubutacciya ce, tambarin adabi ne, a harshen da muke amfani da shi, kama daga kan sakonnin Twitter da muke aikewa da su zuwa kan zaben adireshin i-mail.

Ba za a ce an kebe daukacin al'amuran da aka gano na da ban mamaki ba. Masu haba-haba da jama'a (sakin jiki) sun fi surutu rututu fiye da tsararakinsu masu shiru-shiru.

Su kan yi magana cikin sauri. Mata masu sakin jiki (da mutane), amma ban da maza sun zama cikin taron mutane suna tattaunawa, yayin da maza masu dari-dari da mutane (amma ban da mata)su kan shafe tsawon lokacin suna zancen zuci (maganar kansu da kansu).

Sai dai masu dari-dari da masu sakin jiki (da jama'a) suna amfani da kalaman harshe mabambanta.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Shekaru kadan da suka wuce, wani gungun masu bincike karkashin jagorancin Camiel Beukeboon na Jami'ar VU da ke Amsterdam, suka gana da mutane 40 da suka aikin sa-kai, inda aka umarce su su dubi hotunan mutane mabambanta a yanayin zamantakewa, sannan su bayyana abin da ke faruwa da karfi.

Sun gano cewa harshen masu sakin jiki ya fi zama hasashe kuma "sakaka," yayin da masu dari-dari ke da tsayayyar Magana. A iya cewa, masu dari-dari sun fi nuna al'amari kai tsaye.

Masu sakin jiki sun ce: "Wannan makalar ta yi kyau matuka."

Masu dari-dari sun ce: "Wannan makala ta yi matukar ilimantarwa."

Bisa la'akar da wannan, sauran binciken ya gano cewa masu dari-dari sun amfani da manuniya, wanda a bayani take nufin wani abu ko taro. Sannan sun yin takatsantsan a kalaman harshensu; wato ana nufin yiwuwa ko akasin hakan, kuma suna yawan kimanta yawan al'amura, kamar wanda ke nuni da tabbacin lambobi.

Masu sakin jiki sun ce: "Mu nemi abinci"

Masu dari-dari sun ce: "Ta yiwu mu je ko mun samu makwalshen nama da biredi."

Daukacin al'amuran na nuni da alkiblar tunani.

Mafi yawan masu sakin jiki na jin dadin kazar-kazar din rayuwa, ta yadda ake ganin za su iya zama mashaya, su kwana ko'ina, tare da yin kasada fiye da masu dari-dari; a ko wanne lokaci suka bude bakinsu, to a shirye masu sakin jiki suke da yin kasada ba tare da la'akari da tabbacin daidai ba, kai tsaye za su furta abin da suke son fadi.

Dangantakar da ke tsakanin kimar mutuntaka da kalaman harshe ta kan fadada zuwa kalmomin da aka rubuta.

Lokacin da Jacob Hirsh da Jordan Peterson na jami'ar Toronto suka umarci dalibai su rubuta abubuwan da suka koya a baya da mnufofin da suke son cimmawa nan gaba, sai suka gano cewa wadanda kimarsu ta nuna masu sakin jiki ne sun fi amfani da kalmomin da ke nuni da alaka, wadanda suka bayar da ma'ana a wajen masu bincike cewa, masu skain jiki suna "da kazar-kazar wajen hulda."

Asalin hoton, (Credit: Wikimedia Commons/Eric Magnan)

Bayanan hoto,

Wadanda ke bayyana sirrinsu sun fi kasancewa masu amfani da Kalmar "tawada"

Sai dai wannan ba yana nufin kwatanceceniya ce tsakanin masu sakin jiki da masu dari-dari ba.

Kalaman harshensu sun nuna irin kimar mutuntakrsu, kan al'amuran da suka shafi bude cikinsu (suna da walwalar amfani da kalmomi kan al'amurn da suka shafi alkiblar tunani), yadda damuwarsu take (matukar damuwa mai yawan haifar da bacin rai) da yadda suke takatsantsan (dalibai masu kwazo na yawan amfani da kalmomin cimma nasara).

Mai damuwa cewa ya yi: "Na dugunzuma cikin bacin rai."

Mai bayyana sirrinsa cewa ya yi: "Kana kawai bukatar a ji ka ne."

Mai takatsantsan cewa ya yi: "Za mu yi aiki kan lamarin."

Kimar mutuntaka na haskawa ne a wajen rubutun kirkira.

A shekarar 2010, wani gungun Jamusawa masanan tantance tasirin kwakwalwa kan dabi'u suka bai wa dalibai fiye da 100 kalmomi biyar ("hadarin jirgin sama," 'Yar aiki" "Rugugin wuta," tsakiyar karni," da "katafaren shago") sai aka bukaci su rubuta gajeren labara da zai hado daukacin kalmomin.

A wannan karon masu bayyana sirri sun kirkiro labarai, yayin da masu sassauci suka rubuta labarai masu nuni da abokanta/kawancen huldar jama'a.

Saura da me, da aka nuna wa sauran gungun daliban labaran, aka bukaci su yanke matsaya kan dabi'un marubutan sun yi managarcin aiki, inda a kalla suka tabbatar da masu bayyana sirrinsu da masu kyawun hali.

Mafi yawan binciken ya bibi kalmomin harshen da muke amfani da su a kebe. Sai dai kuma me yake faruwa lokacin da muke tattaunawa?

Daya daga cikin binciken ya gano cewa idan ka tara dimbin masu dari-dari a daki guda, za su karke ne da tattaunawa kan yadda za a shawo kan wata matsala (ina neman wani dakin domin abokan zamana suna yi mini harigido").

In an kwatanta da lokacin da masu sakin jiki ke tattaunawa da juna sukan bibiyin kadin al'amura da dama, inda sukan nuna dimdin "annashuwar magana" kamar "ina son jijjiga jikin gudu-gudu" da "Steinbeck na da ban mamaki."

Wannan dai ya dace da abin da mafi yawna mutane suka sani tuni: a rayuwa masu sakin jiki sun fi mayar da hankali kan jin dadin rayuwa.

Asalin hoton, (Credit: iStock)

Bayanan hoto,

Kuma masu sakin jiki akwai yiwuwar su fi amfani da Kalmar "sha"

Tabbas a 'yan kwanakin nan mu kan sarayar da kwanakinmu wajen aikewa da sakonnin i-mail da sakonnin shafin sadarwa da baza bayanai a shafin twitter.

Ko ka san cewa muna kaskantar da kimar mutuntakarmu a wadannan shafukan sada zumuntar intanet.

A wajen nazarin bayanan shafuka 700 wadanda ke kunshe da dubban daruruwan kalmomi, masu bincike a Jami'ar Texas da ke Austin sun gano cewa kalmomin da mutane ke amfani da su sun yi daidai da yadda suke bayyana kimar mutuntakarsu; misali, wadanda suke ganin suna da kyawun hali suna amfani da kalmomin da ke nuni da rantsuwa kadan.

Da gungun masu binciken suka ci gaba, har ta wajen bibiyar dabi'un mutane dangane da amfani da wasu kebantatttun kalmomi.

Dimbin bayanai kan "masu bayyana sirri" na nuni da cewa sun fi kwatanta amfani da Kalmar "tawada" sannan an yi hasashe mai karfi cewa masu sakin jiki sun yiwuwar amfani da kalmar "sha".

Asalin hoton, Chelsea Guglielmino

Bayanan hoto,

Masu dari-dari kamar Sarauniya RuPaul (wadda ya ce yana badda kama ne tamkar mai sakin jiki) sai yake kokarin yin magana tsayayya

Kwatankwacin irin wannan labarin ya bayyana a Twitter.

Sauran binciken ya gano cewa masu skain jiki sukan yi nuni da sosuwar zuciya na gaskiya da huldar abota a kai-akai, yayin da masu tsananin damuwa (ko ratsin natsuwa) suka fi amfani da wakilin sunan mutum na farko tilo, kamar "Ni" "Kaina" Na karshen ya gano cewa wadanda suka damfaru da rashin natsuwa sun fi amfani da kalmomi cikin 'yanci. Da nuna isa.

Masu sakin jiki sun ce: "Muna cikin farin ciki!" Masudamuwa sun ce: "Ina jin dadin wannan lokacin" cikin 'yanci da isa.

Abin mamakin shi ne, wadannan mutane masu kimar mutuntaka da aka auna sun yi daidai, kuma binciken dai ya gano cewa wadanda suka yi aikin sa-kai sun samu nasarar tantance kimar mutuntakar bako yadda mai damuwa da mai kyawun hali suke t ahanyar karanta sakonninsu na Twitter.

A gaskiya alamu sun nuna ba za mu iya kokarin bibiyar kimar mutumtakar mutanen da muka hadu da su ta hanyar la'akari da kalmomin da harshensu ke furtawa.

Muna yi mutane hukunci akai-akai bisa la'akari da tambarin sakonsa na kafofin sadarwa. Wadanda ke da lambobi da dama a adireshin i-mail dinsu, misali ana ganinsu a matsayin wadanda ba su da kula ko takatsantsan.

Yayayin da muke ganin masu barkwanci a adireshinsu sun fi kasancewa masu sakin jiki (kodayake wannan ba gaskiya ba ne).

Manufar bayyana muhimmin lamarin a kanmu duk lokacin da muka yi magana, ko rubutu ko sakon Twitter damuwar kadan ce musamman idan gaba daya kafi son boiye sirrin dabi'arka a kashin kanka.

Sai dai an samu damar sauya yadda wasu ke kallonka.

A wani yanayin, kamar wajen ganawar daukar aiki ko farkon haduwar masoya, akwai yiwuwar mutrum ya gwada kyakkyawar dabi'a da mutuntaka, ta hanyar sauya kalaman harshenka.

Idan ka yi haka kuwa zan iya hasashen cewa kimar mutuntakarka akwai tasirin salon Machiavelli (salon juya tunanin masu mulki ga al'umma).

Ina ganin zai fi kyau in dakata da rubutu yanzu kafin ka gano irin dabi'ata