Ko ana iya hango abin da zai auku a gaba?

Daga Sharon Weinberger

22 ga Fabrairun 2012

Asalin hoton, Getty Images

Peter Gloor bai mallaki mulmulallen gilashin duba (crystal ball). Baya ramlin ganyen shayi, inda zanen layukan hannunka ke ikrarin yin magana da matuna "daga wani bangare."

Duk da haka masu binciken kimiyya a Cibiyar Fasahar kere-kere ta Massachusetts (MIT) sun yi ikirarin iya gane abin da zai faru nan gaba.

Dauki misalin yadda jam'iyyar Republican ke kokarin tsayar da dan takarar zabe.

A shekarar da ta gabata, inda kuri'un Newt Gingrich suka yi ta hauhawa, inda wasu masana suka yi kyakkyawan zaton shi zai doke abokin karawarsa Mitt Romney. Amma Gloor ya yi has ashen cewa ba zai ci ba.

Gaskiya ta tabbata cewa ce ce-ku cen da ake ta yi a Twitter alamun sun nuna yadda tsohon Shugaban majalisa ke samun galaba, amma masu nazarin bayanan da aka tace a shafin Wikipedia, Gloor ya yi hasashen cewa Romney zai doke shi.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ta tabbata Gloor ya canki gaskiyamai cin daidai: Romney ya kayar da Gingrich da wawakeken gibi da daddare.

Tabbas akwai yiwuwar ka ce hasashen sa cankar sa'a ce kawai. Sai dai Gloor ya ce hasashensa ya sha tabbata tsawon lokaci akai-akai. A wasu lokutan ma.

Yadda yake nazarin al'amura (dalla-dalla) kan taimaka wajen fitar da sakamakon zaben ind ajin ra'ayin jama'a ya gaza.

Alal misali, a shekarar 2009 an kada kuri'ar hana ginin hasumiyar masallatai a kasar Switzerland. Kuri'ar jin ra'ayouin jama'a ta yi kuskure nuni da cewa mutane za su ki amincewa da matakin (da za a dauka), yayin da bibiyar kadin al'amura na Gloor ta hanyar nazarin shafukan sadarwar sada zumunta (na intanet) ya yi hasashe daidai, inda ya canki cewa za a tabbatar da matakin.

"Mutanen sun yi wa masu tattara kuri'un jin ra'ayin karya, saboda ba sa so a dauke su masu nuna wariya, inji Gloor.

Tsarin bincikensa ya bunkasa a jerin nau'ukan aikin kimiyya, wanda ake yi wa lakabi da nazarin hangen abin da zai auku gaba.

Wani fanni ne da ke daukar hankalin kowane mutum kama daga kan hamshakan masu shiryawa da kasuwancin fina-finai, wadanda ke kokarin gano fina-finan da za su shahara a wajen jiga-jigan jan rangamar harkar, da wadanda ke son cikakkun bayanai game da hannayen jari su ke samun nasara.

Su kuwa wadanda ke sha'awar harkokin siyasa, sukan yi amfani da wannan dabarar ne wajen hasashen gano wanda zai lashe zaben da ke karatowa.

'Binciken dimbin al'amura"

Bibiyar kadin al'amuran bayanan da ke tattare a bainar jama'a don gano abin da zai auku nan gaba ba sabon al'amari ba ne, amma yunkurin da aka yi ta yi a baya sun mayar da hankali ne kacokam kan labaran kafafen yada labarai.

Gabanin fara yakin duniya na biyu, Gwamnatocin Amurka da Birtaniya sun yi ta bibiyar kafafen yada labaran duniya don gano musababbin tashe-tashen hankulan, sannan a lokacin yakin cacar baki, Gwamnatin Amurka ta dauki nauyin malaman jami'a don su bullo da dabnarun lissafi da za a rika amfani da su wajen bibiyar rahotanni kafafen yada labarai don gano matakan da Tarayyar Sobiyat ka iya dauka (abubuwan da za ta aiwatar a gaba).

Shekaru goman da suka gabata kafafen shafukan sada zumunta irin su facebook da Twitter sun bullo da makwararar labaran duniya. Kaleve Leetaru, masanin kimiyya kwamfuta a Jami'ar Illinois ya kwatanta shafukan sada zumuntar da wani abu kamar "kafar shiga mutane" saboda dimbin bayanan da suke tattare a wurin.

"Akwai biliyoyin al'amura da aka baza a Facebook kullum tare da aikewa da sakoni miliyan 200 a twitter," in ji shi.

"Daya daga cikin abin da na fi yin nuni da shi yanzu, shgi ne kowace rana ana kara samun dimbin kalmomi da ake bazawa a twitter fiye da abin da ake wallafawa a shafun jaridar New York times tsawon shekaru 60 da suka gabata.

Asalin hoton, Getty Images

Dabarar dai ita ce a fahimci abin da bayanan ke nufi shi ne muhimmin al'amari a darussan

Misali Gloor ya ce Twitter na da matukar alfanu wajen gano dabi'ar da ke da tasirin kan dimbin al'umma. Abin la'akari wajen kallon sabon fim, alal misali, abin da cinbcirindon mutane suka ce na da tasiri kan al'umma; yana da kyau ko fim din ya yi muni?

Wani abu ne da gano shi aka dora shi bisa gwajin masana kimiyyar kwamfuta hsinchun Chen na Jami'ar Arizona.

Chen da gungun abokan aikinsa sun yi nazarin dimbin bayanai daga daruruwan fina-finan Hollywood, inda suka yi kokari gano dangantakar da ke tsakanin sayar da tiki ta shafukan sada zumunta. Tsarin ya yi matukar "kyau," kamar yadda Chen ya yi nuni.Dakin bincikensa ya yi nasarar gano cewa fim din Mel Gibson the Beaver kan wani mutum da yake magana ta hannun dan kwikwiyo zai nasa bam; haka shi ma na Jim Carey mai taken Mista Popper Penguins. Babu wanda aka kada wa kuri'a a shafukan zumunta na intanet, a cewar Chen.

Darasin da aka koya daga bin kadin al'amuran shafukan zumunta na intanet kan bayanan da aka tara kan fina-finai shi ne ba a damu ba kan kowane ne ya zama tauraro, ko nawa aka kashe wajen shirya fim, ko ma wane irin kyau fim din ke da shi; abin la'akari kawai shi ne abin da mutane ke fada a kansa a shafukan intanet.

"Masana'antar fina-finai ta tumbatsa," a cewar Chen , "ba abin da ta kunsa ba."

Duk da cewa cincirindon da aka na da tasiri mai kyau kan fina-finai, amma in aka dauki irin wannan salon aka dora ma'auninsa kan harkokin siyasa al'amura za su rincave. Sabanin haka, masu bincike kamata ya yi su duba mabambantan bayanai da aka tattara.

A nan ne "dimbin al'amura" suka shigo, a cewar Gloor. Dimbin al'amura wani gungun kwararru ne da ba su da matsala, tamkar wadanda suke suke gyaran kundin bayanai na Wikipedia.

"Akwai dimbin masu ta'ammali da kundin Wikipedia, amma dubu biyu ko uku ne suke yin mafi yawan aikin," in ji shi. "Mu kan tarairayi wasu, don gano yadda ake girmama su, su wane ne ke gyara wani abu."

Dangane da zabubbukan fitar da gwani na Republican, bibiyar kadin al'amuran nazarin Gloor a Disamba ta yi nuni da cewa kodayake talakawa a shafin Twitter sun nuna cewa Gingrich ne zai yi nasarar lashe zaben, inda dimbin bayanan Wikipedia ma na nuni da cewa Romney ne ke kan gaba.

Asalin hoton, Getty Images