Mene ne alamun abin da zai auku a gaba?

An fara wallafa wannan maƙala a watan Satumban 2017

Mene ne alamun abin da zai auku a gaba?

Asalin hoton, Getty Images

Duk da cewa wadanda ke amfani da dabarun gano abin da zai auku dimbin bayanan da ke tattare a shafukan sadarwar intanet na da muhimmanci, sukan yi takatsantsan kan kimar tasirinta wajen aiki kan daukacin fannoni.

Wasu al'amuran ba za a iya gano ta hanyar amfani da shafukan sadarwar zumunta a intanet, wadanda mutane ba sa maganarsu a shafukan intanet. "Ta yiwu ba za mu iya gano laifukan da aka aikata ba," inji Gloor. "Ba za su tattauna kansu a bainar jama'a ba."

Leetaru ya yi matukar damuwa da yawan dogaro da shafukan sadarwar intanet don gano abubuwan da za su faru, inda ya yi ta kai-kawo kan al'amura da dama wadanda yanayin su ke nuni da cewa sunfa faruwa a bainar jama'a, kamar zanga-zanga, suna tattare da boyayyen al'amari a bagarensu.

"Idan ka dubi tarzomar Birtaniya (a shekarar 2011), abu na farko da kowa ke cewa (a duba) Facebook da Twittter. Amma da aka ci gaba da dubawa, sai aka fahimci cewa hakikanin wadanda suka tayar da tarzomar tsararraki ne masu masu musayar sakonni ta Blackberry."

Duk da cewa Leetaru na cikin masu hasashebn hango abubuwan da ke faruwa a shafukan sadarwar intanet dangane da huldar al'umma da harkokin siyasa, inda aikinsa na kwanan nan ya himmatu kacokam wajen fuskantar bibiyar bayanan da aka tattara ta kafofin yada labarai na al'ada da aka saba da su, wadanda suka hada nazarin rahotannin labaran baya, wadanda ya ce sun gano wajen buyar Osama bin Laden a cikin da'irar mil 125 (ko kilomita 200).

Shafukan sadarwar intanet, duk da suna samar da dimbin bayanai, ba lallai ne su bayar da bayanai masu tushe ba, ko managartan bayanai. "Daukacin ayyukan da ke fitowa daga shafukan intanet na nuni da cewa wuri ne na kwakwazo," in ji Leetaru. "Wani al'amari ya faru kuma kafar sadarwar intanet ta kawo rahoto a kansa."

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Alal misali tashin hankalin da ya biyo bayan zaben Kenya shekaru da dama da suka wuce, Leetaru ya yi nuni da cewa mafi yawan sakonni kafafen sadarawar intanet na sada zumunta sakonin da ke fitowa daga kasar ba lallai rahotani ba ne masu tushe (ko makama) kan al'amarin da mutane suka gani, amma sabanin haka mutane kan aike da sakon twitter ko su watsa labarai daga rahotanni kafafen yada labarai.

"Don haka wannan ba yana nufin cewa suna kawo rahoton cewa sun ga tanki na gungurawa a kan titi ba, suna kawai amfani da shi kusan kodayaushe don baza bayanai akan lokaci," a cewarsa.

A jerin cukurkudaddun al'amura da dama, masu bincike kan hada bayanan shafukan intanet da rahotanni labarai da sauran bayanan da ke tattare a bainar jama'a don taimaka wa hasashensu na gano al'amuran da za su auku.

Alal misali, Kamfanin hadin gwiwar Sweden da Amurka mai tattara bayanan abin da zai auku nan gaba, da a yanzu yake a Cambridge, Massachusetts yana zakulo daruruwan dubban bayanai daga kana bin da gwamnati ke tattarawa zuwa kan shafukan sadarwar intanet, don gano alamun abin da zai auku nan gaba.

A cewar Christopher Ahlberg, shugaban kamfanin masarrafar kwamfutar da kamfanin ke amfani da ita ga bunkasa cikin shekara goma wajen bibiyar ayyukan da suka gabata.

Shi da abokan aikinsa sun damfaru da son gano dabarun tsara bayanai bisa la'akari da lokacin aukuwarsu, inda suke bai wa mutane damar yin bincike a Google kan al'amuran da za su faru nan gaba.

"Kafafen sadarwa cike suke da irin wadanan al'amura na gaskiya kana bin da zai faru nan gaba," kamar yadda Ahlberg ya yi nuni.

"Don haka abin da za mu tambayi kawunanmu shi ne ke za mu iya samar da na'urar da za mu yi amfani da ita da wasa kawai mu kirata DVR (Mai tattara bayanan muryar da aka furta) kan kowane al'amari da aka yi magana a kai ko aka rubuta game da abin da zai faru a gaba, sannan mu tsara bayanan da kyau cikin tsari a matattarar adana su, ta yadda za mu rika amfani da ita cikin sauki?"

Kamfanin ya yi kwatankwwacin hakan, kuma ayau ya yi masarrafar tattara bayanai kana bin da zai auku, wanda ake amfani da shi a tsakanin kamfanoni masu zaman kansu da abokan huldar gwamnati da ke da bukatar bibiyar kadin bayanan hasashen abin da ka iya aukuwa nan gaba.

Daya daga cikin misalan bayanan da aka tattara kan al'amuran da ka iya faruwa a gaba za a iya amfani da su, a cewar Ahlberg, ta yiwu a dogara da su wajen bibiyar hawa da faduwar hannayen jarin kamfanonin harhada magunguna.

Mai nazarin zai dubi wani kwanan wata, tare da bayanan da aka tattara kan abin da ka iya faruwa a gaba, inda za a nuna masa daukacin bayanan da aka tattara daga jama'a kan al'amuran da ka iya aukuwa a wannan ranar, wanda suka hada da nazarin Hukumar tantance nagartar abinci da magani ta Amurka (FDA), wajen fito da sabon magani ko karewar ikon mallakar fasahar sarrafa magani.

Asalin hoton, Getty Images

Daukacin wadannan bayanai na tattare da muhimman alamu ga masana. Kuma za su iya zama sharer fage wajen nazarin bin kadin abin da zai auku gaba: zaben hannayen jarin da farashinsu ke dagawa.

Sai dai Ahlber da sauran masu bincike sun dauki wannan a matsayin hanya mai nisan kaiwa ga manufa. "A wasu lokutan ina ganin mutane na son a yi musu duban siddabaru," inji Ahlberg. "Wannan bai dace da hakikanin al'amarin ba."

Yawan bayanai

Wasu sun yarda cewa har yanzu nan ne wajen rudanin. Gloor, wanda ya saba amfani da dabararsa wajen shammatar kasuwanni, zuwa yanzu nasararsa ta takaita a wani bajiri. Sai dai irin wannan aikin (nasa) ya fitar da wani sakamako mai ban mamaki: dabarun aikin na bayar da damar maye gurbin hada-hadar hanayen jari. "Muna da masu rike kambi da masu rike kambi duk sun tabbata gaskiya ne," inji shi. "Suna Magana akan sabon ci gaban da aka samu wanda ya yi daidai da sabon makamashi."

Chen ya yarda cewa kasuwannin hada-hadar kudi sun fi wuyar hasashe fiye da fina-fionai. "Lamarin babu sauki wajen hasashen yadda za ta kaya a hada-hadar hannun jari; Za ka iya gano yadda al'amura al'mura ke kara-kaina, yawan abin da ya hauhawa da tumbatsa," inji shi. "Sakamakon babbar martaba ce (kwatankwacin tambarin Holy Grail)."

Idan irin wannan tsarin nazarin ba zai yiwu a kodayaushe ya yi hasashe mai tabbaci kai tsaye, to kimarsa akwai bin kadi don gano al'amuran da za su iya faruwa yana kara samun karbuwa a wajen gwamnatin Amurka. Bayanan da aka tattara kan makomar al'amura, wadanda fasahjar kere-kere za ta iya binciko su a shafukan intanet don hasashen abin da ka iya haifar da zanga-zangar siyasa, wadda ta hada da mamayar kasuwar hannayen jarin Amurka ta 'Wall street' ko shawo kan miyagun ayyuka. Wadanda suka hada da farmakin kutse a shafukan sadarwar intanet, al'amari ne da tuni ake nazarinsa wajen jami'an tsaron kasa. Dabarar In-Q-Tel kamfanin hada-hadar hannayen jari da Hukumar Leken asirin Amurka ta CIA ta kafa ya zuba jari a kamfanin.

A gaskiya masu bin kadin ayyukan sirri muradinsu game da bin kadin abin da ka iya aukuwa a gaba, musamman bisa la'akari da kafafen sadarwar zumuntar intanet, yana kara kasura a 'yan shekarun da suka gabata, musamman bisa la'akari da kakar zanga-zangar juyin-juya halin Larabawa, wadanda ake ganin akwai dan tasirin kafafen sadarwar zumuntar intanet wajen ruruta wutar rikicin. A bara, binciken manyan ayyukan sirri na Iarpa, wani tsarin bincike da bunkasa ayyuka, wani reshe na Hukumar Asirin Amurka, ya kaddamar da aikin da ya yi wa lakabin manuniyar bayanai (Open Source Indicator) da aka tsara don binciko bayanai a shafukan sadarwar zumuntar intanet da sauran bayanan da ke bainar jama'a da za a yi amfani da su wajen gano abin da ka iya faruwa a gaba.

Hedkwatar tsaron Amurka ta 'Pentagon' ta kaddamar da dimbin dabarun hasashen bin kadin gano ayyuka a 'yan shekarun nan, tare da tabbacin gane dabi'ar mai kunar bakin wake. Mark Maybury babban masanin kimiyya a rundunar sojan saman Amurka ya kwatanta tsarin tatttara bayanai kan mutane kan ko daga shafukan intanet da labaran kasashen waje ko wani wurin daban a matsayin wani abu mai kama da hotunan bayanan da na'urori masu sarrafa kansu suka tara lokacin da suka yi shawagi a sararin samaniyar Afghanistan. Sai dai sabanin bayanai kan bama-bamai, yana tattara bayanai ne kan dabi'un mutane.

"A managarciyar dabarar kasa, za ka so yin abubuwa irin wadanda za su gano rugujewar kasa," a cewar Maybury wanda ya tsara dabarar aikin bin kadin al'amura ga rundunar sojan sama. "Managartan tsare-tsaren da za su bayar da damar gano al'amuran da suka shafi fasakwauri ta ruwa, safarar mutane da fataucin miyagun kwayoyi."

Har yanzu abin tambaya shi ne kawai ko al'umma na da masaniya cewa sakonninsu na twitter da facebook da Wikipedia masana a jami'o'i da kamfanoni masu zaman kansu da Hedkwatar tsaron Amurka ta Pentagon da Hukumar Leken asiri ta CIA na bibiyarsu. A wannan zamanin mutane ba su cika yin tunani kana bin da suke aikewa ta twitter game da tsarin abincin darensu ko baza ra'ayinsu na siyasa ko karin bayani game da zanga-zangar da ake yi a kan titi.

Hatta mutane da ke kauce wa ta'ammali da Twitter da Facebook suna tiamakawa wajen samar da bayanai ta hanyoyin da ba su snai ba: nazarin bibiyar kimanta martabar kayayyaki a shafin Amazon, ko yin sharhi a shafukan labarai ko wani abu mai saukin bincikowa a wayarsu ta alfarma da za a iya tattarawa a yi nazarinsa.

Mutane sun dugunzuma cikin damuwa kan dimbnin bayanai," a cewar Mark Abdollahian, masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Claremont, wanda ya yi aiki da kamfani mai zaman kansa don fitar da dabarun hasashen gano abin da ka iya aukuwa. Ba wai shafukan sada zumuntar intanet kadai ba; Abdollahian ya yi nuni da cewa: wayar zamani tai Phone da sabon tsarinta na sarrafa murya da ya shaahra Siri Voice Application, wanda ke aikewa da byanai ga kamfanin Apple, inda ake bibiyar kadinsa tare da sauran bayanai.

Daukacin wadannan bayanan, ko da daga shafukan zumuntar intanet ko wayoyin hannu na alfarma aka binciko su, wani zai bibiyi kadinsu saboda wata manufa, ko gano yiwuwar zanga-zangar siyasa ko hawa da saukar farashin hannayen jari ko ma kawai ya gano gidan sayar da abincin da kake kokarin ganowa.

"Tambayoyinku kan lamarin za su kara wa mai nazari gogewa. Mene ne mutane ke yi da bayanai? Inji Abdollahian. "Wannan ita ce tambayar da daukacinmu ke soin bijiro da ita.