Ya dace ma'aikaci ya rika duba Intanet yayin aiki?

Sabanin a ce an saci kayan kamfani, ta hanyar biibiyar shafukan sadarwar intanet lokacin aiki, ma'aikata na satar sarayar da lokutan kamfani (na aiki don biyan bukatar kansu) Hakkin mallakar hoto Getty Images

Daga Emily Lowe-Calverley da Rachel Grieve

20 ga Agustan 2017

Duba shafukan ciniki a Intanet ko wuraren shakatawar hutu a shafukan Facebook: idan ka dakatar da aiki don bibiyar shafukan Intanet a kashin kanka za ka kasance abin zargin 'bibiyar shafukan sadarwa a lokacin da kake bakin aiki.'

Dube-dube a Intanet lokacin aiki wata dabarar zamani ce da ke kawo tarnaki a wajen aiki.

Sabanin satar kayan kamfani, wajen aiki na zamani da ke tattare da na'urorin sadarwa cikin sauki ma'aikata ke samu damar sarayar da lokutan aiki.

Dube-duben Intanet a lokacin aiki ba ya tattare da mummunar manufa, amma ba a kodayaushe ba.

Domin a gaskiya, a bincikenmu, mun gano cewa, bibiyar shafukan Intanet a lokacin aiki na tattare da "mummunar" dabi'ar, ta hanyar boyewa yadda ba za a gane ba.

Wane ne ake da tabbacin zai bibiyi shafukan sadarwar Intanet lokacin aiki, kuma bisa wane dalili?

Amfani da dama

Muna da ma'aikata 273 wadanda aka sakaya sunayensu a wani bincike da aka gudanar a shafukan Intanet kan yadda ake sarayar da lokutan aiki don bibiyar shafukan wajen biyan bukatar kashin kai da ta zama "mummunar" dabi'ar kowane mataki a kullum.

Irin wadannan dabi'u ana ganinsu tamfar keta haddin zamantakew a ne, na munan dabaru rubi uku, wato mugunta da kwasar garabasar son-rai da danniyar juya akalar al'amura (siddabarun Machiaveli) da jiji da kai, nau'ukan dabi'un da ake samu a rukunin al'umma.

Muna sa ran cewa saboda fafutikarsu ta son kwasar garabasa su tauye wasu, in an kwatanta da hakkoki da daidaikun masu munanan dabaru suke da tabbacin suna bibiyar shafukan ntanet don biyan bukatar kashin kansu a lokacin aiki.

Mun yi nazarin yadda mutane ke jin cewa sun sha (wajen aikata son ransu) a wajen aiki ba tare da an kama su ba (iya yaudarasu).

Babu mamaki jin cewa jiji da kan da ke tattare da wadannan munanan dabi'u uku, irin wadannan mutane na jin cewa za su iya shammatar sauran.

A jerin wadanda aka bibiyi kadin lamarinsu.

Mun gano cewa rudanin kwakwalwa da danniyar juya akalar al'umma a salon 'Machiavelli' (dabarun mulkin jama'a) da fifita kai na da alaka da dabi'ar bibiyar shafukan intanet a lokacin aiki, ta hanyar yausdara.

A wani yanayi munanan dabi'un uku (rudanin kwakwalwa da danniyar juya akalar al'umma a salon 'Machiavelli' da fifita kai) na bayar da cikakken tabbacin cewa mutum ya sha (tsira ba tare da an kama shi/ita da laifi ba), al'amarin da ke sanyawa a karke da dube-duben intanet don biyan bukatun kashin kai a lokacin da ake bakin aiki.

Abubuwan da muka gano na nuni da cewa daidaikun mutane da ke fama da rudanin kwakwalwa kan aikata dabi'un bibiyr shafukan Intanet don biyan bukatun kashin kansu a lokacin aiki ba tare da la'akari da cewa suna yaudara ba.

Wannan lamari daidai yake a kan mai fama da matsalar rudanin kwakwalwa:mutumin da rikicin kwakwalwarsa ya tsananta ba ya jin kunya ballanta dar-dar din ya aikata laifi, tga yiwu ma bai damu ba, koda an kama shi (da laifi).

Idan masu kamfani na son rage bibiyar shafukan intanet lokacin aiki, dabarun shawo kan lamarin shi ne a gano yadda ma'aikata ke yin yaudara na da muhimmanci.

Ana bukatar karin bincike bisa la'akari da cewa bincikenmu rahoton kashin kai ne da ya yi wa mata alfarma, ammma sakamakon ya bijiro da tambayoyi masu kayatarwa game da wuraren aiki, tattare da irin dabarar da suke da ita wajen shawo kan irin wannan dabi'a.

Ko shugabannni za su damu?

Illolin da ke tatttare da bibiyar shafukan Intanet lokacin aiki sun hada da dauke hankalin ma'aikaci daga aikinsa zuwa munanan abubuwan da za su iya haifar wa kamfani asarar dukiya ko rashin tsaro (alal misali, lakakin aikin alakar kwamfutoci ko kwayoyin cutar bayiros da ke cutar kwamfuta).

Bincikenmu na nuni da cewa idan kamfanoni na son shawo kan bibiyarr shafukan intanet da ma'aikata ke yi lokaccin aiki, ana iya bullo da dabarar bin kadin aiki keke-da-keke, ta yadda in an kama wani zai zama darasi ga wasu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Za a iya sanar da ma'aikata cewa daukacin al'amuran da suke gudana a shafukan intanet za a rika lura da su, amma sa'ido na tattare da hadarin shiga kebabbiyar rayuwar ma'aikaci ta sirri, tare da haifar da yanayin aiki mara dadi.

Kyakkyawan al'amari game da bibiyar shafukan intanet lokacin aiki ba daukacinsa ba ne mummunar dabi'a a wajen aiki.

Duba shafukan intanet na da kyakkyawan tasiri dangane da abin da ke sosa zukatan ma'aikata, inda suke samun damar kawar da damuwa.

Kuma takan kara musu kuzarin aiki bisa wasu dalilai, ta hanyar samar wa ma'aikatan tsaikon hutun wucin gadi, inda da sun dawo bakin aikinsu sai su mayar da hankali kan abin da ke gabansu.

Katafaren likon alakar na'urorrin kwamfuta matsala ce.

Yayin da ma'aikata ke fakewa da aiki su bibiyin shafukan intanet, su ma aikin kan keta hadddin rayuwarsiu ta kashin kansu.

Likon alakar na'urori ke bayar da damar aiki sa'o'i 24 a mako.

Wani bincike ya yi nuni da cewa ma'aikatan da kamfani ya ba su wayar salula alfarma sukan ji cewa kodayaushe ana tare da su ddon haka suke jajircewa a wajen aiki.

A wajen wasu ma'aikatan, wannan lamari ne tattare da alfanu da akasinsa.

Fahimcewa za a "tuntubeka ko kiraka a kai- a kai" kan sanya a jibga wa ma'aikaci dimbin aiki.

Sai dai, likon alaka na iya haifar da gajiyawar ko kashe karsashin kwazon ma'aikata.

Yin aiki daga gida na bai wa ma'aikaci damar samun gamsuwa da natsuwar aiki.

Ma'aikata sun saba fafutikar "daidaita aiki da harkokin rayuwa," amma a wajen wasu mutanen wannan hanyar a yanzu kafarta ta dusashe.

Duba Intanet a lokacin aiki da sarrafa na'urori da ma'aikata ke yi na da alaka guda.

Mutane na yin aikin kashin kansu ne a shafukan Intanet lokacin da suke wajen aiki, sannan suna gudanar da ayyukansu lokacin da suke gida.

Ana son sabuwar mahangar 'daidaito'?

Wasu nau'ukan nazarin na nuni da cewa fasahar lakabin sunan ta fito ne da tsarin da yanzu zai bai wa ma'aikata damar neman "daidaito tsakanin aiki da harkokin rayuwa," inda ma'aikaci zai sarayar da dimbin lokaci ga aiki da harkokin rayuwa, ta yadda zai dauki kowane da muhimmanci.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yayin da ma'aikata ke bibiyar shafukan intanet don bukatar kansu a lokacin aiki, to aikinsu ma na shiga cikin harkokin rayuwarsu

Alal misali, ta yiwu ka amsa kiran waya daga wajen aiki yayin da kake kallon gasar wasan kwallon danka, amma kakan yi tsallen badaken baza hotunan kyaututtukan murnar bikin zagayowar ranar haihuwar babban abokinka.

Jigon lamarin dai na nuni da cewa ma'aikaci na jin cewa zai iya tarairayar ayyukan da ake matukar bukatarsu.

Bayanin binciken da aka gudanar na nuni da cewa aiki daga gida ya fi dadi da samun gamsuwa a tsanake.

Binciken dai ya bayyana cewa, 'wadanda ke damar yin aikin kashin kansu lokacin da suke bakin aiki, ba za su samu tarnakin karon-batta tsakanin lokacin aiki da hidimar iyali ba.

Sai dai wadannan aka ba su damar yin aikin kashin kansu daga gida lokacin da suke bakin aiki, suna da isasshen lokacin aiki da hidimar iyali.

Bincikenmu ya nuna cewa yadda ma'aikata ke fakewa da damar wurin aikinsu (su yi aikin kashin kansu) wani yanki ne na bibiyar shafukan Intanet sabanin aikin da aka dauki mutum ya yi.

Amma nau'uka biyu ne: shugabannin kamfanoni na bukatar su yi tunani kan ko amfana da dimbin ma'aikatansu.

Asalin wannan makala ta fito ne a kafar sadarwa ta"The Conversation," (tattaunawa), san nan an sake wallafata karkashin izinin lasisin dokar kirkirar ayyuka (ko rubuce-rubuce).

Labarai masu alaka