Yadda mutane ke shirya wa kansu jana'iza

jJana'izar da mutum ke shiryawa kansa Hakkin mallakar hoto Sian Butcher

Shirya jana'izar 'bogi' zai taimaka wajen samun sabuwar mahangar fahimtar rayuwa, ta yadda tunkarar mutuwa da ba za a iya kauce mata ba, musamman ga wadanda ke fama da cutar da ka iya kawo karshen rayuwarsu, na bai wa mutane damar yin ban kwana da masu kaunarsu.

Ooho, sannan ta yiwu kawai mutum ya saurari kyawawan bayanan da mutane za su ce game da kai bayan ranka/ki. Kuma a cewar wanda ya yi jana'izar kansa wannan al'ada ce da ke kara samun karbuwa a Birtaniya.

Yi wa kai jana'iza duk da cewa mutum na nan a raye (a jana'izar da jigon shirin na nan a raye) tuni ake gudanar da shi a Koriya ta Kudu da kuma kasar Japan (inda ake yi wa al'adar lakabin da seizenso).

Ko shirya irin wadannan bukukuwan alama ce ta kauce wa mutuwa wadda ta zamo abin kunya?

Idan haka ne kuwa, lamarin na iya kasancewa da alfanu wajen inganta lafiyar tunanin kwakwalwarmu - wani bincike da aka gudanar a 2009 wanda ya gano cewa tunanin mutuwa na tsawon mintuna biyar a rana, har zuwa mako guda, na rage kaifin tunanin dugunzumar damuwa.

Bunkasar jana'izar da rayayyu ke shirya wa kansu na matukar baranazar kawar da al'adar zaman makoki.

Mutane na kauce wa bukukuwan addini na al'ada da aka saba da su don yin shirin bukukuwan jana'iza na lumana.

Bunkasar ire-iren jana'izar da rayayyun mutane ke shirya wa kansu ya kasance wani babban abin mamaki a al'adar zaman makoki.

Mutane suna kauce wa daga bukukuwan addini na al'ada da ake yi wa mamaci ta wajen aikata wasu nau'ukan kamar jana'zar lumana, inda wasu wuraren shirya jana'izar ke amfani da makarar da za ta yi rugu-rugu ko gara ta cinyeta.

Farkon wannan shekarar, wani tauraron fina-finan Hollywood Luke Perry an binne shi sanye da suturar "hular barawo".

Wani sabon salon sanya likkafani ne da ake yi da kadar auduga da nau'ukan tsirran hular barawo wanda masu yin sa suka yi ikirarin cewa zai iya "rage kaifin rubewar jiki da za ta gurbata muhalli da kona gawa."

Za ka/ki iya hayar "mai haifar da rudani a jana'iza" mutumin da ake biya don isar da sakonni daga mamaci (wasu lokutan na daukar fansa, kamar fada wa mutane su bar wurin, a wasu lokutan kuwa barkwanci ne ko nuna kauna).

Hakkin mallakar hoto Sian Butcher

Wannan shi ne kwatankwacin tsaurara dokokin da ke tattare da mutuwa da jana'iza wadanda musamman suka kasance masu tsaurin gaske a zamanin Sarauniya Victoria.

Da can, al'adun sun hada ganin masu makoki sanye da bakaken kaya na wani tsawon lokaci, gwargwadon dangantakarsu da mutumin - wadanda abokan zamansu suka mutu (mace ce ko mijin ne).

Alal misali, ana sa ran ganin sun kasance sanye da irin wadannan tufafin tsawon shekaru biyu - su kuma rage shiga ruguntsimin tarurrukan hada-hadar harkokin zamantakewar al'umma na tsawon shekara.

Mafi yawan lokuta ana son masu zaman makoki su ajiye gashin mamaci da aka datso, ko su kasance sanye da wani nau'in kayan ado na musamman don zaman makokin.

David Williamson, wani kwararren mai tarairayar ruhi da ke cibiyar kula da lafiya ta St Leonards Hospice a York, na shirin bullo da jana'izar rayayyu a matsayin hidimar tarairayar majinyatan da ake kula da su daga bisani cikin wannan shekarar.

"Na samu izini daga Majami'ar Ingila don haka na dade ina yin jana'iza sama da shekara 30," a cewarsa.

"A kodayaushe na kan cika da mamaki jin irin kalaman da abokai da 'yan uwa ke yi game da mamata, kuma na kan tambaye su, "Ko kun taba furta irin hakan ga mutanen lokacin da suke raye?

Kuma tabbas suna yawan amsa mini da cewa a'a. Don haka na kan cika da mamakin kan cewa ko akwai wani salon da ya fi dacewa mu bayyana tunaninmu da yadda muke ji game da mutanen lokacin da suke raye?

Ya gano cewa a al'adar Birtaniya, inda a gargajiyance a kan kame kai lokacin sosuwar zukata, shi ya sa jana'izar rayayyu za ta iya "'yantar da mutane su kawar da abin da ke sosa musu zukata ba tare da sun wulakanta ko su kasance cikin rashin jin dadi ko a hargitse."

Georgia Martin, mai shekara 28, ta fara aikin sa-kai na shirya wa rayayyu jana'iza, bayan zuciyarta ta sosu a wajen jana'izar kakanta.

"Na tuna yadda na ga abokansa a wajen tare da tunanin bakin ciki," zai so ganin daukacin wadannan mutanen. Shin mene ne ba ya hana mu shirya irin wannan ba lokacin da yake raye?

Shekara guda daga bisani, ta shirya nau'ukan jana'izar rayayyu sau shida kuma ta ce yayin da kowace an bambanta salon aiwatar da ita, inda take ganin sun taimaka wa daukacin masu mutuwar da iyalansu suka amince da hakan.

A ganinta, suna da wata kima da ta fi jana'izar al'ada da aka saba yi, tunda babban bako a wajen jana'izar, tabbas mamacin ne.

Zayyanar mutum jingine da tulluwar dutsen bayanan kabarinsa Sian Butcher

"Yayin da kowa ke halartar jana'izarka bayan ka/kin mutu, a hakikanin gaskiya ba ka/kya nan a wurin ballantana ka ji daukacin al'amura/abubuwan kauna da suke so a tare da kai/ke," Georgia ta ce "Sannan lamarin na ba ka/ki damar gaya wa mutane cewa, yayi kyau a ci gaba bayan na mutu."

A wajen wasu kuwa, shirya jana'izar rayayyu ga masu fama da cutar da ke saurin kisa ga mutanen da suke kauna, na ganin mutum zai samu damar muhimman al'amuran lokacin da yake cikin mawuyacin hali.

A shekarar 2016, Tom Honeywell, mai shekara 24 ya taimaka wajen shirya jana'izar rayayyu ga kakansa, wanda bayan an sanar da shi cewa wata guda ya rage masa kawai na rayuwa, ya jajirce kan cewa yana son gudanar da biki tare da abokansa.

Kimanin mutane 80 suka halarci bikin da aka gudanar a Plymouth. Akwai mai daukar hoto, inda ya yi hotuna da masu tarairayarsa gwanin ban sha'awa a kan dandamali inda mutane suka mike tsaye don girmamawa.

Tom ya ce: "Ina jin cewa sai mutum mai dakakkiyar zuciya zai iya shirya wa kansa jana'iza alhali yana raye. Ka san bikin da ka/kike gudanarwa; kasan cewa kai mai mutuwa ne.

Yayin da shirin ke taimaka wa "mai mutuwar" ya gana da abokansa a karo na karshe, kuma lamarin na da matukar damuwa da kai-kawo a tunanin jin cewa mene ne dalilin da ya sa ka kasance a wurin gaba daya ma.

"Rana ce mai sosa zuciya," a cewar Tom, " ta kasance harbutsai yin bikin mutuwa bayan yana nan a raye. Yana bayar da tabbas gaskiyar lamarin cewa mutuwa gaskiya ce. Amma dai fatansa ne, kuna za ku iya sanin cewa ya ji dadin lamarin. Yanayin farin ciki ne."

Yayin da mafi yawan mutane ke yi wa kansu jana'izar rayayyu saboda sun kamu da cutar mai saurin halakarwa, wasu kuwa suna yi ne saboda kawai su yi wani abu bambarakwai na daban (a rayuwarsu).

Michael Hebbm, wanda ya kafa kungiyar Death Over Dinner - Tattaunawar Mutuwa a wajen cin abinci (kungiyar da ke karfafa gwiwar mutane su rika taron cin abinci don tattaunawa kan mutuwa), inda suka taba yin taro a Seattle don murnar zagayowar ranar haihuwarsa shekara 40.

Shi da budurwarsa da suka dade tare sun ranba gari makonni kadan kawai kafin a gudanar da lamarin. Don ba ya son kasancewa shi kadai, sai ya aike da sakonnin email ga abokansa 50 yana gayyatarsu su zo bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Nan take arba'in suka ba shi amsar cewa za su halarci bikin, kuma daga cikinsu, akwai wadanda suka yanke matsayar ingiza keyar abokinsu - da ya shahara da sunan "Malam Mutuwa - Mista Death" - Jana'izar rayayyen mutum.

Lamarin kan fara ne kamar wasan kwaikwayo, amma daga bisani sai kawai ya rikide ya zamo kamar na gasken gaske: daga nan lamarin ya tashi daga wasa sun yi shiri tsaf, inda Michael ya kasance sanye da fararen tufafi, tamkar dai yadda ake lullube mamaci da likkafani a akwatin gawa ko makarar da ke bude, inda zai kasance a kwance na tsawon sa'o'i uku.

Hakkin mallakar hoto Sian Butcher

Sai masu daukar gawa su dago ka, a kai ka wani daki mai duhu, a kunna kyandir.

"Hucin numfashinsu ya yi warin giyar whiskey," a cewar Michael daya daga cikin masu ciccibar gawa. "Sai sun shawu su yi ta shirmen nuna damuwa."

Daya daga cikin abokansa, duk da cewa ta san cewa ba gaskiya ba ne, sai ta yi ta kuka da kallon jikinsa ba ya motsi a cikin akwatin gawa, kuma wadanda suka halarta suna ta yabonsa.

Wani abokin na cewa: "Ina fargabar cewa ba ka taba sanin yadda nake kaunarka ba." ''Yar Michael 'yar shekara 15 ita ke karkare bikin.

"Ta dora hannunta a kaina, sannan ta yi wani irin yabon nuna kauna mai ratsa zukata, dangane da matsayina a gareta. Kowa ya yi ta kuka."

Zayyanar wata mata tana ta yabon mamaci - Sian Butcher

A cewar Michael kusan kodayaushe yakan sha wahalar kulla alaka da mutane, har da akwai lokutan da a rayuwarsa yakan yi zaman kadaici.

Sai dai bayan da ya samu kansa kwance a akwatin gawa, inda ba shi da wnai zabi, illa dai kawai ya saurari yadda mutane suka dauke shi ko kimar matsayinsa a wajensu, a cewarsa lamarin ya bude masa sabon babin fahimtar rayuwa.

Yanzu yana jin cewa tamkar dama ta biyu ce ya samu" ta yadda zai kyautata dangantakarsa da mutane, tare da gyara kurakuransa na tsawon shekaru 40 da suka gabata.

Alamu na nuni da cewa wannan salon ya rikide ya zamo wani bikin al'ada.

A bikin wasannin nishadi da aka yi ba da dadewa ba (har ma da Shagalin sirri da aka gudanar a cikin lambu, bikin kade-kade da raye-raye tare da ruguntsimin wasannin nishadi da ake gudanarwa a da), tsunduma cikin wasan kwaikwayo na bai wa mutane damar zakuwa cikin damuwar bacin rai game da yadda aka gudanar da jana'izarsu.

"Muna son kawar da wannan al'adar zamanin Sarauniya Victoria a inda muke da zabi kawai," a cewar Daraktan gidan wasa, Martin Coat, mai shekara 38.

"An nusar da mu yadda za mu nuna damuwa dab akin ciki, yadda za mu sanya liyafa da irin dabi'ar da za mu nuna - muna son kalubalantar lamari, mu kawar da shi."

Bayan da dabarar yin jana'izar rayayyu ta bijiro musu, sai Martin da abokan aikinsa suka haka kabari da Majami'a (Coci) da wajen adana gawa (macuware) a matsayin shirinsu.

Kowane "mamaci" sai ya tuntubi kwararru da za su nusar da shi/ita yadda ake shirya jana'iza da zaben "wakoki" (mafi yawanci wakokin Disney ko shahararrun ruguntsimin kidan gambarar turawa na 'hip hop').

Sai mutuwa ta same su ta takarkata su zuwa wajen adana gawa don 'alkinta gawa ka da ta rube', yayin da 'cincirindon sahun' mahalarta za su rataye hoton tunawa da mamaci a kan bishiya.

Sai a yi "addu'o'i" da za a shafe tsawon mintuna 25, a cewar Martins, "mafi yawan lokauta lamarin na da ban dariya" abokai su yi ta zubo yabo.

Daga nan sai a shimfidar da mutum a akwatin gawa - an dan bula kafar da za su iya ganin waje - sai a yi kasa-kasa a kwantar a rami mai zurfin kafa 6 (mita 1.8) na kabari.

Yayin da shirin an yi shi ne da manufar wasa, tare da cusa tunanin damfaruwa da tuna abin da ya faru wanda ya hada da 'sadaukarwa' na butun-butumin yanyawa (teddy bear) da ake amfani da ita wajen farfado da gawar mutum ya farka.

Martin ya bayyana karara cewa a wasu lokutan lamarin na da matukar damfaruwar tunanin "son-kai' inda mutane ke zakuwar son jin kyawawan kalaman da mutane ke furtawa game da su.

Sai dai, a cewarsa, akwai kuma yanayin da kan cusa wa mutum sosuwar zuciya. "Mun taba samun wasu tsofaffin ma'aurata da suka taba sayen filin kabarinsu daf-da-daf suna makwaftaka da juna.

"Sun yi hakan ne don suna son jin juna da abin da za su furta game da junansu. Wannan shirin ya yi matukar girgiza daukacinmu.

Zayyanar mutum a cikin akwatin gawa, rike da modar gilashi yana shagalin bikin jana'izar kansa-da-kansa.

Sai dai ba fa ko wane ke yarda a kakaba masa manufar yin jana'zia ba. David ya ce mutane a mafi yawan lokuta ba sa son amfani da kalmar, sun fi son a ce "bikin karshen rayuwa."

Laur Green, wadda ke koyarwa a cibiyar tarairayar kula da lafiya ta Jami'ar Manchester, cewa ta yi, idan har za ta yi irin wannan, za ta yi wa lamarin lakabin "shagalin bikin bankwana" - amma Georgia na ganin cewa mu daina kokarin kauce wa ambaton mutuwa.

"Kamata ya yi ka/ki kulla alaka da mutuwa," a cewarta, "saboda haka za ka/ki kasance."

Hakkin mallakar hoto Sian Butcher

Haka lamarin jana'izar rayayyu ta kasance al'amarin da ke nuni da cewa ko mun fara samun natsuwa da mutuwarmu? Laura na ganin kaskanci ne in an gwama da al'adar da aka saba, sannan tattaunawa ce a bayyane game da al'amuran da ke tattare da karshen rayuwa.

Ana samun karin kasashe da doka ta amince a taimaka wa mutum ya mutu, a yanayin da mutane ke zabar mutuwarsu ta hanyar taimakon likitoci ko shan magani, kimanin fiye da shekara 30 da suka wuce (kodayake kasar Birtaniya ba ta cikinsu) - sai dai kuma tana bijiro da tattaunawa kan yadda ake shirya wa karshen rayuwa.

"Ina ganin jana'izar na cikin jerin al'amuran da ake tattaunawa da mutumin da ke 'mutuwar'," a cewar Laura, "sabanin wani abu daban da iyalai/zuri'a ke gudanarwa daga bisani."

A al'ummar da ake kara samun wadanda ba ruwansu da addini, mukan samu kanmu wajen kai-kawon tunanin yanke matsaya kan irin al'adu/bukukuwan da ya kamata a gudanar yayin mutuwarmu."

Akwai dimbin dabaru da dama wadanda mutane kan zaba da suke so a gudanar wajen jana'izarsu," a cewar Laura.

A gaskiya, Georgia cewa ta yi, idan ta ce wa mutane su shirya jana'izarsu alhali suna raye, sai ransu ya baci saboda ba su taba sanin al'amarin ba, kan cewa zabi ne da ke nuni da yadda masoyi ke mutuwa.

Ko mutum yana so, ko ba ya son halartar jana'izar kansa-da-kansa, ta yiwu wasu mutane za su samu kwanciyar hankali idan suka aiwatar da irin wannan zabin.

"Akwai wani abu bambarakwai da ake sa-rai a wajen jana'iza, wato kawata wajen da kyandira masu kamshin turaren lavender da kuma duhu dumdum," in ji Laura.

"Amma idan ka kasance mai tsananin son dabdalar shagalin biki ne, ta yiwu ka so yin shagalin. Mutane na son mutuwa a irin yanayin da suka rayu.