Hotunan kasaitaccen bikin addinin kirista na 'yan Oromo a Habasha

Woman in traditional costume

Dubun dubatan mutane ne suka hallara a bikin mai suna Irreecha wanda 'yan kabilar Oromo, wadand aita ce kabila mafi yawan jama'a ke gudanarwa a birnin Addis Ababa a karon farko cikin fiye da shekara dari.

A wata al'adar bikin na Irreecha, akan sanya furanni da ciyawar da aka yanko ba da jimawa ba a ruwa domin mika godiya da ubangiji saboda samun damina mai albarka da shigowar yanayin bazara.

People sprinkle water on their bodies as they take part in the Irreecha celebration, the Oromo thanksgiving ceremony in Addis Ababa Hakkin mallakar hoto Reuters

An samar da cikakken tsaro a yayin da dubban mutane suka fita bisa tiutuna har ma da babban dandalin birini Addis Ababa, Meskel Square. Jama'a sun rika rera wakoki da daga tutoci da furanni. Jami'ai na cewa kimanin mutum miliyan 10 aka sa ran za su halarci bikin.

People waving a flag and spraying water Hakkin mallakar hoto AFP

A shekarun baya an rika yin bikin ne a Bishoftu, gari mai nisan kilomita 40 daga Addis Ababa, ammaa an rika yin wasu bukukuwan a wasu sassa na yankin Oromiya a wasu lokuta daban-daban na shekara.

Crowds in Meskel Square in Addis Ababa Hakkin mallakar hoto AFP

Ana kiyasta akwai kimanin 'yan kabilar Oromo miliyan 40 a Habasha, wanda ya sa suke da kashi 30 cikin 100 na mutanen kasar.

Man in traditional costume

Wadannan matan ana sanye da kwalliyar da ake yi da duwatsu kamar kananan murjanai a goshinsu. Mutanen yankin Borena na Ormoiya ne ke yin irin wannan kwalliyar.

Men and women standing in a semi-circle

Wadannan maza biyun da ke kasa kuwa sun yi tafiyar kilomita 400 ne daga Bale a kudancin Habasha domin shiga wannan bikin.

Men in traditional costume

Wannan matar daga Hararghe ta ke wanda yana gabashin Habasha ne, kuma ita ma ta sanya kayan yankinsu na gargajiya.

Woman in traditional costume

Sai kuma wadannan mutanen Alaba, sun halarci bikin daga yankinsu da ke kudancin Habasha waje da Oromiya.

An Ethiopian man from the Alaba region dances during the Irreecha celebration Hakkin mallakar hoto Reuters

Firai ministan Habasha Abiy Ahmed shi ma dan kanbilar Oromiya ne.

Young people in traditional costume

Hotuna - Yadeta Berhanu (BBC), Amensisa Negera (BBC), Reuters da AFP.

Labarai masu alaka

Labaran BBC