Auren Mutu'a a Mazhabar Shi'a
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shi'a: Ba ma mut'ah da kananan yara

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron hirar da BBC ta yi da Sheikh Bashir Lawan, wani malami mabiyin mazhabar Shi'a a Najeriya kan auren mut'ah

Wasu malaman mabiya mazhabar Shi'a a Nigeria sun yi karin haske kan auren mut'ah, da wasu mabiya mazhabar suke yi.

Auren na mut'ah dai yana daga abin da musulmai suke da sabani a kansa tun a farko-farkon musulinci.

Ko a 'yan kwanakin nan BBC ta gudanar da wani bincike na musamman kan yadda wasu malaman Shi'a ke gudanar da auren mut'ah da kananan yara a Iraqi.