Kun san sirrin kifi mai kyalkyali?

Kayataccen kifi kan mamaye jikin halittun ruwa Hakkin mallakar hoto David Fleetham / NPL
Image caption Kayataccen kifi kan mamaye jikin halittun ruwa

Kayataccen kifi na da zayyana mai kayatarwa, wadda ke da manufar hayayyafa da kara yawan halittun da ke zaune a mazaunin da ake gani karara a cikin ruwa.

Sun sha rasa iyayensu mata, ta yadda a wasu lokuta kaya mara kyau kan yi magana da harshen Ingilishi.

Daukacinsu ana yi musu lakabi da zayyanar kifin majigin takala (Nemo).

Gaskiyar lamari: fim din zayyanar majigin kifin zanen takala na dauke da sautin da ke nuni da kimiyyar nazarin halittu.

Amma akwai nau'ukan daban-daban har 28 na irin wannan kifi mai dimbin kayatarwa da ke kan tudun karkashin teku, inda ko wanne ke samun dimbin alfanun kawance da furanni.

Muhimmai daga cikin dimbin tsare-tsaren rayuwar kayataccen kifi sun hada da sauya jinsi. Kamar yadda kowa ya sani, kayataccen kifi ba shi da sunaye.

Ni kwararren masani ne a fannin kimiyyar nazarin namun daji, kuma na damu kwarai kan yadda ba a bayyana muhimman al'amura game da dabbobi a kafafen yada labarai ba.

Wannan ne dalilin da ya sanya na zama mai wuyar sha'ani wajen zuwa sinima, musamman idan majigin da za a nuna ya shafi zanen takalar dabobi.

Hakkin mallakar hoto Alex Mustard / NPL
Image caption Kayataccen kifi (clownfish) na matukar gwada karfin kazar-kazar

Fim din Kung Fu Panda - yanyawar China, alal misali ba zan iya sanin dalilin da ya sanya abincin yanyawar Panda ya kasance miyar taliya, sabanin yadda aka santa tana cin bawon iccen kwangwala ba.

A fina-finan Ice Age na shiga rudu ganin yadda kuregen da ke cin nama ya raja'a wajen cin hatsi.

In an kwatanta da majigin zanen takalar kifi, sai a ga yanja dauke da dimbin gaskiyar da aka tantance a kimiyyance, amma duk da haka gaskiyar lamari game da wannan kifi mai kayatarwa da ke kan tudun kasar karkashin teku mai ruwa garai-garai, lamari ne mai rudarwar ban mamaki fiye da yadda mafi yawan mutane suka dauka.

A farkon shirin, ta macen kayataccen kifi (Coral) ke nuna sha'awarta ga halittun ruwa, inda ita da abokin zamanta (Marlin) ke zama (ko yin gida).

"Dimbin nau'ukan kayataccen kifi su kan mayar da hankalinsu a wajen," inji Coral.

Wannan shi ne nazari na hakika saboda hakikanin duniyar kayataccen kifi na nuni da karfin kazar-kazar kan halittun ruwa, wadanda daukacin rayuwarsa ta dogara kacokam, kuma da wuya su kauce wa wurin da ke bai wa sassan jikinsu kariya.

Tabbas a kebabben akwakun gilashi garai-garai kayataccen kifi na iya rayuwa cikin annashuwa ba tare da halittun ruwa ba, amma wannan kawai yana yiwuwa ne saboda babu masu kai musu farmaki.

Hakkin mallakar hoto Juniors Bildarchiv GmbH / Alamy
Image caption Gaskiyar lamari na da firgitarwa fiye da kage

Tamfar 'yan haya, nau'ukan kayataccen kifi na biyan masu gidansa tsirran ruwa abin bukata.

Su kan yi ga-da-ga wajen korar kifin malam buda mana littafi - butterflyfish da ke kai wa tsirran ruwa farmaki ya kassara sassan jikinsu.

Zaman kayataccen kifi na bai wa tsirran ruwa natsuwa, domin ana cinye musu sassan jiki da kimanin kashi 80 cikin 100.

Idan aka cire kayataccen kifi za su samu raguwa da kashi 50 cikin 100, saboda haka akwai bukatar a yi takatsantsan, domin wasu 'yan awoyi kadan ne ake jira kafin kifin -malam-buda-mana-littafi- butterflyfish.

Wannan ba shi ke nan ba.

Tamkar daukacin nau'ukan kifin da ke kan tudun karkarshin ruwa, kayataccen kifi na fitar dimbin sinadarin ammonia.

"Al'amari ne da za a iya fahimta cewa suna samar da taki ga masu masaukinsu ta hanyar kashinsu," a cewar Nanette Chadwick, masanin kimiyyar nazarin halittun ruwa a Jami'ar Auburn da ke Alabama ta kasar Amurka, wanda ya fadada nazarin dangantakar kayataccen kifi da halittun ruwa.

A wani kyakkyawan gwaji da aka gudanar aka wallafa cikin shekarar 2005, ita da abokan aikinta sun fito da manyan halittun ruwa zuwa dakin bincike suka daddatsa su gida biyu, suka yi wa kowane rabi ado da kayataccen kifi, inda suka kyale daya rabin ba tare da irin kifi da ke zaune tare da shi ba.

Rabi-rabin da ke damfare da kayataccen kifi da sinadarin ammonia cikin sauri ya farfado fiye da wanda babu kifin a tare da shi, al'amarin da ake ganin saboda tasirin sinadarin ammonia ne ya tiamaka wajen bunkasa ayyukan sarrafa abincin kananan tsirrai da ke bai wa halittun ruwa kuzari, inda su kuma bayar da wurin zama ga kifayen su rayu.

Hakkin mallakar hoto Georgette Douwma / NPL
Image caption Karamin kifi na taimaka wa masu masaukinsa (furanni) su rayu

Nan ba da dadewa ba, Chadwick da abokan aikinsa suka nuna cewa kayataccen kifi na taimaka wa tsirran ruwa su shaki iska da daddare.

Da rana kuwa, lokacin da rana ta yi haske, tsirran ruwa na sarrafa abincinsu ta hanyar samar wa furannin ruwa iskar oxygen din da suke bukata.

Yayin da duhu ya yi tsirran ruwa sun kwanta barci, kazar-kazar din kayataccen kifi na taimakawa wajen samar da iskar da furannin ruwa ke shaka.

Tun da mazaunan wannan bagire (na ruwa) suna tattare da dimbin alfanu, ba makawa dole ne tsirran ruwa da furanni su yi ta fafutikar yadda za su rayu idan babu kayataccen kifi.

"Idan ka cire kifi, to tsiro zai mutu," a cewar Chadwick.

Dangane da majigin zanen takala na Finding Nemo, gaskiya ce mai wuyar yarda saboda fim din ya zaburar da dimbin bukatar kayataccen kifin "Nemo."

"Ya fi sauki a ciro su daga cikin karkarshin ruwa fiye da amfani da dabarun kimiyya," inji Chadwick.

A gaskiya, binciken da aka gudanar a bara a kan tarin halittun tudun kasar karkashin teku a Austiraliya ya nuna cewa yawa-yawan nau'ukan kayataccen kifi babu su a inda aka san suna zama a da, inda aka dora alhakin aukuwar hakan kan tsamowar da ake yi.

Hakkin mallakar hoto David Fleetham / NPL
Image caption Qayataccen kifi dangantakarsa da dan tayinsa na da rauni

Za a iya karkarewa da cewa, akwai wani dalilin da ya sa ni ke ganin wuyar kirkurar majigin zanen takalarsa. An gaza bayyana tabbatacciyar gaskiya game da al'amarin kayataccen kifi:

Dakikoki kadan bayan macen kayataccen kifi (Coral) da namijin (Marlin) sun koma wajen halittun ruwa, sun kyankyashe kwayayensu wadanda suka girma a cikinsu, annashuwarsu a wannan wuri ta kan kwaranye saboda farmakin hamshakin kifi.

Mace mai kwai guda (wanda za a kyankyashe a matsayin kayataccen kifi) su ne kawai ke rayuwa. A hakikanin wannan duniyar, al'amura na iya sauyawa da yawa. "Idan macen ta mutu ko ta yi kaura zuwa wani wurin halituun ruwa daban, sai namijin ya sauya jinsinsa, ya zama mai karfin mamaya," inji Chadwick Cool.

Hakkin mallakar hoto Q Phia CC BY 2.0
Image caption Kayataccen kifin da aka shammace shi

Abin da ya rage, shi ne za a ga kankanen qayataccen kifi na da karsashi, ta yadda da zarar an kyankyashe shi zai fara kai kawo daga muhalinsa yana neman sabon rukunin mazaunin kifaye. "Idan har ba su yi haka ba, to manyansu na iya cinye su.," Kamar yadda Chadwick ya fada.

Saurin mutuwar kasusuwan kifin kan ingiza namijin kifi (Marlin) ya sauya jinsinsa, ta yadda zai iya cinye dan-tayinsa/yar-tayinsa. Wannan ya yi kama da hakikanin abin da aka kaga . Don haka wannan shi ne dalilin da ya sanya wajen nuna majigin Disney ba ya amfani da shi.

Bayanan da aka baza a shafin Twitter game da kayataccen kifin (clownfish):

Idan macen kayataccen kifi ta mutu, namijin sai ya sauya jinsinsa zuwa mace mai mamaya. Ta yiwu Mahaifin kayataccen kifi (Nemo) sai ya zama uwa?

Launin rawayar da ratsin farin kayataccen kifi na nuni da cewa suna cikin rukunin kayatattun kifayen da ake samu tare da halittun ruwa a yankuna masu zafi (Asiya da Austiraliya), wadanda daya ne kawai daga jerin nau'uka 28 daban-daban na kayataccen kifi

Hada-hadar kasuwancin akwakun gilashin halittun ruwa da ake gudanarwa an kimanta da shi da $200 zuwa 300 a ko wacce shekara.

Labarai masu alaka