Ko kun san musifun da za su iya tarwatsa duniya?

Wanne kokari ake yi wajen kawar da makaman nukiliya daga fadin duniya?
Bayanan hoto,

Wanne kokari ake yi wajen kawar da makaman Nukiliya daga fadin duniya?

Wani masani mai suna Steven Pinker, ya ankarar da al'umma kan manyan al'amuran da za su iya tarwatsa duniya.

Cikin abubuwan da ya zayyana har da makamin kare dangi wato Nukiliya.

Farfesan tantance tasirin kwakwalwa kan dabi'u a Jami'ar Havard kuma marubucin gaske ba da dadewa ba, ya bibiyi kadin matsayin tashin hankali a al'ummomin zamani.

Littafinsa na shekarar 2011 mai taken Kyawawan dabi'un da ke tattare da mu sun dakile yaduwar tashin hankali na tsawon lokaci.

Dangane da yakin nukiliya kuwa, ya dan yi kai-kawo kan yiwuwar mummunan al'amarin da ke shawagi a kan mu.

A ganawar da muka yi, ya ce mini, makaman Nukiliya sun saba wa kowane tsarin yakin al'ummar da ta ci gaba tattare da barazana mara kan gado mai haifar da kisan kan mai uwa da wabi.

Ya ce hakan zai jawo mutuwar dimbin mutanen da ba a san yawansu ba, inda guba za ta gurbata muhalli.

Sun zama makaman da ba su da tasiri tamkar makaman yakin da aka saba da su, sannan karfin aikinsu ya dogara kacokacam ga aniyyar shugabanni ta halaka miliyoyin fararen hula da ba su ji ba, ba su ga ni ba.

"Kuma mafi munin tashin hankalin shi ne, duk da cewa abin kunya ne yin amfani da su a tsawon karnoni biyu, yiwuwar sarrafa sun a iya aukuwa kwatsam ko in sun fada hannun 'yan ta'adda ba za a cire tsammanin amfani da su ba."

Ko me zai faru idan mafi munin lamari ya auku, inda a wani yanayin za su yi barna kamar yakin Nukiliya da zai yi faca-faca da duniya?

A ganin abokin aikin Nick Bostrom a cibiyar nazarin makomar mutane nan gaba, masanin Falsafa Stuart Armstrong cewa ya yi, nauyin da ya rataya a kanmu shi ne mu shirya wa hadarin da ke tattare da rayuwarmu ba wai kariya kawai ba, har ma da tsarin da muka yi na shirya wa al'ummar da za ta biyo bayanmu kan illolin da ka iya auka mata bayan aukuwar musifar.

"Abu guda da kawai za mu da fahimtarsa," kamar yadda ya fada mini, "shi ne ko za a sake kwata yanayin bunkasar masana'antu."

"Baya ga cewa mafi yawan musifun da suka auku akwai wadanda ke tsira. Ko za su iya sake farfado da bunkasar ci gaban fasahar kere-kere? Kuma mene ne za mu iya yi don tallafa musu su sake farfado da shirin?"

Wannan lamari ne mai tayar da hankali. Idan musifa ta tarwatsa mafi yawan ci gaban da aka samu dubban shekaru kadan da suka wuce.

Ko jikokinmu za su iya sake bunkasa ci gaban masana'antu .. sannan ko akwai abin da za mu iya yi don tallafa musu? Idan al'amura suka tafi a irin haka,, kusan komai muke yi a yau za a ji cewa akwai nakasun karancin tunani wajen aiwatar da shi.

"Idan musifa ta auku," Armstrong ya jajirce kan cewa, "kokinmu za su tsane mu saboda ba mu alkinta musu albarkatun da za su taimake su ba. Mun yi shirme wajen adana bayanai."

Al'ummarmu ta tara muhimman bayanai a faya-fayan CD da kundun kwamfuta ko kayan alkinta bayanai na zamani, inda muke da kyakkyawan zaton cewa duk sa'adda muka sanya su a na'ura za mu samu bibiyar abubuwan da ke ciki.

Idan nan gaba aka yi asarar wannan fasahar kere-kere, mafi yawan bin da aka tara na baya da nasarorin da aka samu shi ke nan an share su.

Bayanan hoto,

Don samun kyakkyawar makoma nan gaba, ya kamata mu bude ido don nazarin abin da muka dauka wasarairai a yau

Ko me muka iya daga daukacin wadannan al'amura? Kamar yadda na yi nazarin bayanan da na ji, ta bayyana karara cewa hasashen abin da zai faru a gaba na kin amincewa (da tsarin rayuwarmu) lamarin na da tayar da hankalin gaske; kokarin ganin dalilai na daban game da zamaninmu tare da kauce wa son rai za a amince da yadda muka kasance na daban.

Tabbacin da ake da shi, shi ne, nan gaba za a mayar da hankali ne kan halin da ake ciki fiye da sarayar da dimbin lokaci wajen bibiyar al'amuran baya.

Sai dai farkon karni na 21 namu ne, kuma muhimmin al'amari da yake karara shi ne: dole mu fadada tunaninmu fiye da bin kadin al'amuran da ke faruwa yanzu.

Don a tattaunawa ta karshe da marubucin kirkirarren labarin kimiyya Greg Bear ya bijiro mini da kimar karfin tunaninmu kana bin da zai auku nan gaba a matsayin daya daga cikin al'amuranmu masu matukar tabbatar da basira.

Kimar karfin kirkirarren labarin kimiyya, Bear ya yi kai-kawo da cewa; shi ne babu dimbin aikin da aka yi wajen hasashen abin da zai auku nan gaba, ta yadda za a juya kalar lamarin.

"Managartan littattafai sun kawo sauyi a tunaninmu," a cewarsa, " don haka, makomarsu ba za ta zama gaskiya ba, amma ba gaba dayanta ba."

Hakikanin gaskiya ba za mu kauce wa kyara daga al'ummar da za ta biyo bayanmu ba.

Shi ya sa idan har mun fahimci tabbacin abin da ka iya faruwa nan gaba, tare da tabbaci da jajircewa, za mu iya yin nasarar mafi nagarta da kowa zai yi fatan samu don kawar da munanan al'amura.

Mun yunkura wajen tabbatar da kyawawa managartan al'amura, ta yadda za mu gadar da al'ada (in ma ba a duniya ba) cikin kyakkyawan yanayi fiye da yadda muka same ta.

Yaya kake jin al'ummomin da za su zo nan gaba za su soki lamirinmu kan dabi'armu ta yau?

Sai mu fahimci lamuran a shafukan Facebook ko Google ko mu aike da sako ta Twitter.