Yadda tsarin rayuwar Yammacin Turai zai rushe nan gaba

Daga Rachel Nuwer

18 ga Afirilun 2017

Masanin dangantakar tattalin arziki da salon mulki (a tsarin siyasa) Benjamin Friedman ya kwatanta al'ummar Turawan Yamma na zamani da keken da ya daidaita da tayoyinsa ke wulwulawa saboda bunkasar tattalin arziki.

Da zarar wulwular tayoyin ta samu tsaiko ko ma ta dakata, turakun da ke kimanta matsayin al'umma a dimokuradiyya da 'yancin walwalar daidaiku da zamantakewar yarda da dabi'un juna da sauransu, to za a yi ta samun kwan-gaba, kwan-baya.

Duniyarmu za ta yi matukar muni, inda za a yi ta fafutikar mamaye 'yan albarkatun kasa tare da kin amincewa da duk wanda ba ya da kusancin danganta da rukuninmu.

Da zarar mun kasa motsa wadannan tayoyi sun ci gaba da juyawa, kawai za a samu rugujewar al'umma dungurungum.

Irin wannan rugujewar ta faru da dama a tsawon tarihin dan Adam, ba tare da ci gaba ba, ko la'akari da tumbatsarta, babu wata kariya da ke bijiro da hadarin da ke rusa al'umma ta zo karshe.

Ba tare da la'akari da kyatatuwar al'amura a halin yanzu ba, yanayin na iya sauyawa.

Fita batun rukunin halittu da suka kare al'amura irin farmakin kananan tairaruwa mai wutsiya (duniyoyin da ke kan falaki) da bazuwar makaman kare dangin nukiliya ko annobar yaduwar cututtuka, tarihi ya nuna mana cewa akwai dimbin al'amura da ke haifar da rushewar al'umma.

Wadanne iri ne, ya ya suke idan akwai su, ko sun fara bijirowa ba kakkautawa? Ba za a ji mamakin cewa al'umma na gudana ko ana tafiyar da ita bisa tsarin dab a zai dore ba, kuma rashin tabbas ne tafarkin da aka dauka, amma abin dubi shi ne ko kawai mun kusa yin nisan da ba ma jin kira?

Hakkin mallakar hoto (Credit: Getty Images)
Image caption An kona motar 'yan sandan afirka ta Kudu tana cin wuta lokacin zanga-zangar neman daidaito

Duk da cewa yana da wahala a gano hakikanin abin da zai faru nan gaba, lissafi da kimiyya da tarihi na bayar da haske kan ci gaba da kyakkyawar makomar al'ummomin Yammacin Turai.

Safa Motesharrei, masanin kimiyya zayyanar tsare-tsaren al'amura a Jami'ar Maryland ya yi amfani da kwamfuta don samun karin fahimta kan yadda al'amuran kasa ko fadin duniya za su dore ko su wargaje.

A cewar Motesharrei, abin da suka gano shi da abokan aikinsa, wanda aka wallafa a shekarar 2014, akwai muhimman al'amura biyu da ke da tasiri wato: gurbata muhalli da kimanta tattalin arziki mataki-mataki.

Ta fuskar muhalli an fi gano yadda lamarin ke da mummunan tasiri, musamman yadda ake karar da albarkatun kasa, da suka hada da ruwa da kasa da kifaye da dazuka, daukacin al'amuran da ake ganin sauyin yanayi na iya ta'azzara su.

Musifa na aukuwa ne daidai lokacin da shugabanni suka tursasa al'umma ta shiga mawuyacin hali, ta yadda mamaye dimbin dukiya da albarkatun kasa ke haifar da rushewarta.

Kimanta darajar tattalin arziki bisa mataki-mataki na iya haifar da rushewa a kashin kansa, ko kuma ta wani bangaren Montesharrei ya cika da mamakin lamarin shi da abokan aikinsa.

Domin a irin wannan yanayi jagorori kan tursasa al'umma ta shiga mawuyacin hali, ta yadda mamayar da suka yi wa dimbin dukiya da albarkatun kasa za ta haifar da rushewarta, inda za a bar talakawan da suka fi su yawa da kaso dan kadan ko ma su rasa komai kacokam, alhali su ke tallafa musu da aikin kwadago.

Kwatsam sai gungun 'yan kwadago su tarwatse saboda kason dukiyar da aka ware musu ba za ta isa ba, baya ga tarwatsewa saboda rashin aikin kwadago.

Rashin daidaiton adalcin da muke gani a yau a ciki da tsakanin kasashe tuni ya yi nuni da bambance-bambance da ke tsakanin al'umma (talakawa da shigabanninsu).

Haka kuma kimanin rabin al'ummar duniya suna rayuwa ne a kasa da Dalar Amurka uku ko wacce rana ($3).

A irin wadannan nau'ukan yanayi fasalin zayyanar lissafi na nuni da kimar nauyin da yawan al'umma zai iya dauka bisa la'akari da albarkatun da ke tarairayar zamansu a muhallin da suke na tsawon lokaci.

Idan aka jibga musu dimbin nauyin da ya fi karfinsu, to ba makawa al'ummar za ta wargaje. Ba makawa haka makomarsu take.

"Idan muka yi aiki da tunani na hankali don shawo kan irin wadannan matsalolin da suka hada da rashin daidaiton adalci da tumbatsar yawan al'umma, ta yadda ake kwashe dimbin albarkatu da gurbatu muhalli, sai a himmatu kan mai yiwuwa don kauce wa rugujewa don daidaita al'amura su dore ba kakkautawa," a cewar Motesharrei.

"Sai dai ba za mu taba yin jinkiri wajen yanke matsauya kan daukar irin wadannan matakan."

Hakkin mallakar hoto (Credit: Getty Images)
Image caption Daya daga manyan darussan da aka samu daga faduwar daular Romawa ita ce cukurkudaddun al'amura suka haifar da matsalar

Takaicin shi ne wasu kwararru na jin cewa irin tsauraran matakan da aka dauka sun sha gaban tsarin siyasa da karfin tunaninmu.

"Duniya ba za ta taba mikewa don tunkarar matsalar sauyin yanayi a cikin wannan karnin ba, saboda kawai lamari zai ci dimbin kudi na wucin gadi kafin a warware matsalar sabanbin yadda a ko da yaushe ake kwan gaba, kwan baya," a cewar Jorgen Randers.

Farfesan da ya kai makura a nazarin dabarun tarairayar yanayi a makarantar nazarin harkokin kasuwanci ta BI Norwegian, kuma marubuci littafin 2052:

Hasashen yanayin duniya nan da shekaru 40. "Matsalar yanayi za ta kara munana saboda mun ki zama mu yi aiki tukuru don cika alkawarin da muka dauka a birnin Paris da sauran wurare.

Duk da cewa a tare muke, wadanda suka fi talauci a duniya su za su tasirin radadin rushewar tashin farko. A gaskiya wasu kasashen sun zama wajen hakar kwal har ta kai ga sun kassara masu dimbin arziki.

Alal, misali Siriya sun yi ta hayayyafa na tsawon lokaci, al'amarin da ya sanya al'ummarsu ta karu. Mummunan farin da aka yi fama da shi cikin shekarun 2000, ta yiwu shi ya haifar da sauyin yanayi tattare da karancin ruwa, ala'amarin da ya kassara harkokin noma.

Wannan mummunar matsala ta jefa dimbin mutane musamman matasa cikin rashin aikin yi da damuwa. Da yawa sun fantsama cikin birane, inda suka mamaye albarkatun kasa da kayan more rayuwa da ke wuraren.

Tashin-tashinar tsakanin al'umma ta dada karuwa, inda aka karke da ruikicin tashin hankali.

Fiye da wannan ma rashin managarcin shugabanci wanda ya hada da jari hujjar jan ragamar kaya su samar wa kansu kimar daraja a kasuwa, al'amarin da ya kawar da tallafi a lokacin farin shi ya share wa kasar kafar afkawa yakin basasa a shekarar 2011, al'amarin da ke kokarin kaita kasa.

Wata alamar da ke nuni da cewa mun shiga da'irar hadari ita ce yawan aukuwar al'amura "kwatsam" sauye-sauyen da ba a zata ba da ke bibiyar duniya.

Dangane da Siriya tamkar na sauran al'ummomi da suka durkushe a daukacin tarihi ba abu daya ya haifar da lamarin ba, akwai dimbin dalilai da suka haifar da matsalar, a cewar Thomas Homer-Dixon, shugaban sashen nazarin tsare-tsaren duniya a Makarantar nazarin harkokin duniya ta Balsille da ke Waterloo a Canada.

Haka kuma marubucin littafi mai taken Jirkicewar al'amura (the Upside Down) Homer-Dixon ya kira daukacin al'amuran da karon-battar yamutsi bisa la'akari da yadda suka taru, sannan suka famtsama kwatsam, inda suka bankara duk wani tsari na daidaita harkokin rayuwa, wanda ke shawo kan matsalolin al'umma.

Baya ga lamarin Siriya, wata alamar da muke kutsawa cikin hadarinta, a cewar Homer Dixon ita ce yawan aukuwar abin da masana ke kira bijirowar rudani da rikice-rikice kwatsam ko aukuwar sauye-sauyen da ba a zata a tsarin tafiyar da harkokin duniya, kamar yadda a shekarar 2008 aka samu matsalar tattalin arziki da fitowar kungiyar ta'addanci ta ISIS da yunkurin ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai da zaben Donal Trump.

Hakkin mallakar hoto Credit: iStock)
Image caption Wasu al'ummomin da ci gabansu ya bunkasa kawai gushewa suke su zama cikin kundin tarihi ba tare da wani abu ya tarwatsa su ba, illa dai kawai za a ji takaicin lamarin

Faduwar daular Romawa ke nuni da rugujewar tsarin Yammacin Turai

Abin da ya faru a baya zai iya haska yadda nan gaba ka iya kasancewa. Alal misali bunkasa da faduwar daular Romawa.

Zuwa karshen karni kafin zuwa Almasihu Romawa sun karade yankin Mediterranean zuwa mafi yawan wuraren da ake iya kaiwa garesu ta ruwa. Kamata ma ya yi a ce sun dakata a can, amma sai kasura suke ta yi, har karfinsu ya yi ta karuwa har suka yi ta fadada mulkinsu tare da sarayar da dimbin dukiya.

Wannan daula ta kama kasa tsawon karnoni, amma da illar fadada mulkin da suka yi ta juyo kansu a karni na uku, sai suka yi fama da ya kin basasa da mamaya.

Daular ta yi kokarin kare hakikanin kasarta, duk da cewa ayyukan soja ya ci musu dimbin kudi ga tsadar rayuwa da hauhawar farashi lokacin da gwamnati ta karya darajar sulallan azurfarta don shawo kan dimbin kudin da take kashewa.

Yayayin da wasu masana ke ganin farkon rushewar daular ya auku ne a shekarar 410, lokacin da Visigoth ya kai wa babban birnin kasar farmaki, wannan mummunan al'amari ya samu nasara ne kan koma bayan da daular ta samu tsawon karni guda.

Al'amura sun kai yadda Rum ba za ta iya ci gaba da tarairayar cukurkudaddun mawuyatan harkokinta na dimbin al'amura da suka kwaso da fadi.

A cewar Joseph Tainter, Farfeser nazarin muhalli da al'umma a Jami'ar Jihar Utah, kuma marubucin rushewar al'ummomin da ke cikin mawuyacin hali, daya daga muhimman darussan da za a koya da faduwar daular Rum shi ne wuyar harkokin rayuwa ya haifar da shi.

Kamar yadda aka fada a dokokin kimiyyar nazarin sinadaran makamashi (ba za a iya samar da shi ko a watsar da shi ba), yanayin da ke bai wa makamashi juriya, yanayin bunkasar al'umma ba ya kauce wa tsarin.

Zuwa karni na uku, Rum na ta kara sababbin al'amura - yawan sojojinta sun rubanya, 'yan kibau an raba su Lardi-laradi ta yadda kowane rukuni na da hukumominsa da kotuna da matakan tsaro don kawai ta kare matsayinta daga rankwafawa ko koma-baya.

Kwatsam ya zamanto ba za ta iya ci gaba da tarairayar mawuyacin tsarinta da ya tyumbatsa.

Zuwa yanzu al'ummomin Yammacin Turai sun fara ja da baya wajen tarairayar irin wadannan alamun da ke bijirowa na faduwar bun kasar daula ta hanyar karyewar darajar makamashin fetur da bunkasar masana'antu inda amfani da makamashin fetur da iskar gas ya hadu da matsala a sheklarar 2008, lokacin da farashin mai ya yi ta haihuwa.

Tainter ya yi zaton cewa lamarin ba zai dore ba, sai dai "a yi tunanin cewa idan har za mu katange Manhattan daga teku, don kawai mu kareta daga guguwa da torokon igiyar ruwa," in ji shi.

Kwatsam sai zuba jarin tarairayar mawuyatan cukurkudaddun al'amura ya fara ja dabaya, al'amarin da hada-hadar kashe kudinsa ta samu tawaya, tattare da hadarin rushewa.

Don haka a cewarsa "har sai mun samu hanyar tarairayar wadannan mawuyatan al'amura, kamar yadda magabatanmu suka yi lokacin da suke tafiyar da al'umma ta hanayar amfani da makamashin albarkatun kasa (gawayi - kwal da fetur da iskar gas da ke tonowa a kasa)."

Hakkin mallakar hoto (Credit: Getty Images)
Image caption Gungun masu tarzoma a Argentina sun yi zanga-zanagar adawa da katsalandan din Amurka a rikice-rikicen siriya da Venezuela

Da yake kwatanta halin da Rum ta samu kanta, Homer-Dixon wajen hangen yadda al'ummomin Yamamcin Turai za su ruguje, al'amarin zai fara aukuwa kafin mutane su janye da albarkatu zuwa hakikanin kasar da suke.

Daidai lokacin da matalautan kasashe za su ci gaba da tarwatsewa saboda yake-yake da musifun da ke auka wa kasa, za a samu dimbin masu kaura da za su bar kasashen da suka tarwatse don fakewa a kasashen da ke zaune cikin lumana.

Yammacin Turai za su dauki matakin dakile yin kaura; ta hanyar ganuwa da yawa da za su ci biliyoyin dala da na'urorin shawagi a sama masu sarrafa kansu da ke sintiri da sojoji; tsattsauran tsaron saboda su wa, kuma mene ne fa'idarsa; da Karin mulkin kama-karya.

"Kawai dai kokarin yin garkuwar kariyar kan kasashe ce don kare matsayi da tunkuda matsala baya," inji Homer-Dixon.

Baya ga haka, za a samu wawakeken gibi tsakanin masu arziki da talakawa a tsakanin kasashen Yammacin Turai da ke tattare da hadarin wargajewa al'amarin da zai t ahaifar da tashintashina a cikin gioda.

"Nan da zuwa shekarar 2050, Amurka da Birtaniya al'ummominsu za su rabu gida biyu, inda matsakaitan manyan al'umma za su rika yin rayuwa mai dadi, sannan mafi yawan al'umma za su samu kansu a wani irin yanayi na koma-baya," in ji Randers. "Al'amarin da zai rushe daidaiton adalci ne."

Ko a Amurka ko Birtaniya ko a wani wurin daban, da zarar mutane suna kara rashin jin dadi (a harkokin rayuwa) tsoro ya dabaibaye mutane, Homer-Dixon ya ce, za su yi ta nanikewa a gungun jama'ar da suka fito ko alakar addininsu da launin fata ko tushen asalin kasa.

Za a yi ta karyata al'amuran da suka shafi rushewar al'umma da kin amincewa da hujjar da ke nuni da hakan.

Idan mutane suka yarda cewa akwai wadannan matsalolin, za su iya dora alhakin aukuwar matsalolin kan kowa wane mutum da tushen asalinsa ba ya cikin rukunin al'ummar da suka fito, ta yarda za a haifar da gaba.

"Tuni aka cusa tunani da gurbata zamantakewa da ke share wa tashin hankali fage," a cewar Homer-Dixon. Idan aka dawo gida tuni tashin hankali ya barke, ko wata kasa ko wani rukunin mutane da ya shirya kawo farmaki, da wuya a kauce wa rugujewar al'umma.

Turai mai kusanci da Afirka da dangantakarta da Gabas-ta-Tsakiya, tare da makawaftakarta da kasashen da ke fama da rikice-rikicen siyasa a Gabashi za ta fara jimn rugugin matsalar.

Ta yiwu Amurka ta dan jajirce na tsawon lokaci, saboda tekun da ya yi mata kawanya.

Hakkin mallakar hoto (Credit Getty Images):
Image caption Mummunan fari a Siriya ya jefa dimbin mutane, musamman matasa cikin rashin aikin yi, tare da bacin rai da damuwa, al'amarin da ake ganin shi ya haifar day akin basasa

Tsawon zamani ya sanya wasu daulolin sun durkushe ba su da wani tasiri.

Ta wani bangaren a iya cewa, al'ummomin Yamamcin Turai ba za su samu matsalar mummunan rikici da zai share su daga doron kasa ba.

A wani yanayin bunkasar tsarin rayuwar al'ummar ne zai gushe ya zama cikin kwandon tarihi. Daular Birtaniya ta kan wannan turbar tun a shekarar 1918, a cewar Randers.

Ko da yake ta yiwu sauran kasashen Yammacin Turai su karke da irin wannan makomar. Tsawon zamani za su kasance ba su da wani tasiri, domin wajen shawo kan tsilli-tsillin matsalolin da za su share su, za su watsi da managartan al'adunsu da sika dauka da kimar daraja a yau.

"Kasashen Yammacin Turai ba za su ruguje ba, amma kyakkyawan tafarkin da suka dauka da kyakkyawar mu'amalar al'umma za ta gushe, saboda rashin adalci zai tumbatsa," kamar yadda Randers ya yi kai-kawo.

"Dimokuradiyya da 'yancin al'umma ne za su gushe, yayinn da gwamnatoci masu karfi da suka tsayu irin su China za su kai ga gaci."

Irin wadannan hange-hangen al'amuran da ka iya faruwa tattare da alamun ankararwa tuni aka saba da su, saboda a hakikanin gaskiya tuni aka share musu fage.

Duk da cewa Homer-Dixon bai yi mamakin al'amuran da ke faruwa a kwanakin nan ba, ya yi hasashen aukuwarsu cikin littafinsa tun a shekarar 2006, sai dai bai sa ran kasancewar al'amuran da ke bijirowa ba kafin nan da tsakiyar shekarun 2020.

Bunkasar tsarin rayuwar al'ummar Yammacin Turai ba karkataccen tsari ba ne.

Sai dai in aka yi amfani da hankali da kimiyya wajen daukar matakin da ya dace, tare da kyakkyawan shugabanci da kyakkyawar dangantakar al'umma, al'umma za ta yi ta samu bunkasar ci gaba da walwala da zai kai matuka gaya, a cewar Homer-Dixon.

Ko da yake muna fama da damuwar sauyin yanayi da tumbatsar yawan al'umma da faduwar farashi da rashin tasirin kimar darajar makamashi, za mu iya tabbatar da dorewar ci gaban al'ummomi da kyautata yanayinsu.

Sai dai al'amarin na bukatar jajircewa da tarairayar tashin-tashina, yayin da duk aka ci karo da dimbin al'amura masu tursasawa da za su kasa hadin kan al'umma da taimakekeniya da aiki da hankali.

"Tambayar dai a nan ita ce, ta yaya za mu iya ririta kyautatawa da jinkan al'umma a daidai lokacin da irin wadannan sauye-sauyen rayuwa da ke tunkararmu?" in ji Homer-Dixon.