Kun san yadda za a tunkari karshen duniya?

Hakkin mallakar hoto (Credit: Getty Images)
Image caption Lantarki ba zai dore na tsawon lokaci ba

Shekarun farko

Idan abincin da aka tara ya kare za ka fuskanci yunwa matukar ba ka fara noma na kashin kanka ba.

Ka shuka ganyayyaki da kayan marmari ('ya'yan itace) kai-tsaye, sai dai matsalarmu nawa ne a yau muka san yadda ake noma kayana binci nau'ukan tsirrai da alkama da shinkafa ko masara?

Duwatsun nika da ke da'irar ginin juya iska ko makwararar ruwa kamar wata fasahar kere-kere da aka fadadata daga tsinin hakoranmu.

Tsirrai rukuni ne an ciyayi, wwadanda ke suarin girma su samar da abinci nau'ukan hatsi, sai dai jikin mutum na da nakasu a tsarin halitta, domin ba kamar ssaniya ba, ba mu da cikuna hudu da za su ba mu damar narkar da ciyawa.

Sabanin haka sai mun yi aiki da kwakwalwarmu wajen warware matsala tare da kirkire-kirkire da kere-keren da za su taimaka wa jikinmu.

Muna bukatar abin da zai taimaka mana wajen nika alkama ta zama gari lukwi-lukwi har mu mayar da ita burodi da zai ba mu sinadaran abinci da jikinmu zai ddauka.

Don haka duwatsun nika da makaran juya iska ko da'irar juya makwararar ruwa suka kasance kamar fadada fasahar kere-kere daga tsinin hakoranmu, sannan wajen gasa burodi ko tukunyar da muke dafa shinkafa suka zama masarrafa abinci takun farko.

Matsalar farko ita ce ta yaya za a fara noma hatsi a samar da karin dimbin abinci, wanda shi ne jigon tafiyar da tsarin rayuwar kowace irin al'umma.

Idan mutum guda zai iya ciyar da mutum 10 sauran wadanda ba za su iya fantsama wajen aikin gona ba, kuma yana da kwarewa a sauran sana'o'i, to al'ummarku ta zama mai iya tsayuwa da kwarinta.

Kayan aikin gona da suka hada da garma da karafunan baje kasa na haro za a iya tono su ko a kirkiro su ta hanyar narkar da karafuna.

Sai dai muhimmiyar dabarar da ta sha kan manoman da ita ce yadda za su ci gaba da tarairayar sinadaran takin da ke damfare a kasar nomanka tsawon shekaru.

Idan har babu takin zamani kana bukatar sinadarin Nitrate don kara wa kasar noma karfi, ta hanyar amfani da kashin dabbobi da baje karmamin tsirrai nau'ukan wake da kanunfari da alfalfa ta hanyar cakudawa da hatsinka.

Narkar da kasusuwan sinadarin acid zai samar da sinadarin phosphates, sannnan watsa daddagaggen alli ko farar kasa zai kara wa kasa sinadarin acid.

Hakkin mallakar hoto Credit: Getty Images
Image caption Lantarki ba zai dore na tsawon lokaci ba

Farkon shekaru masu yawa

Lokacin da al'ummarka ta wadata sabanin tsakure-tsakuren abin da aka bari a juji, kana bukatar koyon dabarun kira da kera kayan aiki na akrafuna da juya akalar na'urori su rika aiki.

Tsarin rayuwa ya bunkasa saboda karfin makamashin sarrafa na'urori: makaranran sarrafa da'irar juya makwararar ruwa da makaran da'irar juya iska sai na'urar da ke sarrafa makashi wajen gudanar da ayyuka, don saukake wahalhalun motsa kwanjin naman mutum.

Managarcin tsarin rayuwar al'umma na bukatar makamashin mai.

Kafin karshen karni na 19 an rika amfani da kwal kafin daga bisani a koma kan fetur, inda jigon sinadaran da kimiyya ke ta'ammmali da su suka hada da acid da barasa (Alcohol) da ruwa-ruwa (Solvents) da kwalta duk an samar da su ne ta hanyar.

Konawa da sanyaya itace; akan yamutsa itacen katakon timber a iska, sannan a kwashe tururin da yake fitarwa daidai lokacin da ya zama garwashin gawayi.

Za ma ka iya amfani da irrin wannan makamashin a mota ta hanyar tatso iskar gas daga katako; a lokacin yakin duniya na biyu akwai motoci fiye da miliyan biyu da ak rika tuka su ta hanyar amfani da makamashin iskar gas da aka tatso don sarrafa injin motocin da ake tukawa a titunan Turai.

A lokacin yakin duniya na biyu akwai motocin da ke aiki da makamashin katako sama da miliyan biyu da ake tukawa a titunan Turai.

Babu man fetur din da za a bunkasa kasa (tsarin rayuwarmu tuni ya zuke fetur din da muka samu) za ka iya yin makamashin mai daga tsirrai ko kitsen dabbobi don sarrafa na'urori wanda zai yi hargagin taho mu gamu da sinadarin Methanol.

Wato (barasar da aka tatso daga itace, busashen iccen katako - timber) da Iye (wanda ke gwamuwar hargagi da soda da sinadarn tsami daga daddagaggen alli ko farar kasa).

A masana'antarka ta sarrafa sinadarai, sauran sinadaran da za a iya hakowa cikin sauki suna da dimbiin amfani.

Alal misali ethanol da ake samu ta hanyar tsima hatsi sannan a tace shi don samun barasa, ruwa-ruwan narkar da sinadarai ne kuma yana da karfin kawar da kwayoyin cuta.

Gawayi na da matukar amfani ba ma don dumama yanayi ko narka karafuna da tubalulan gini ko gilashi kawai ba, har ma yana cikin jerin siandarai da suke 'sakaka' saboda haka ake bukatarsa wajen dabarun kwakwulo karafuna daga duwatsu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Idan muka sake lale wajen gina al'umma ko yaya za ta kasance?

Karnonin farko

Tsawon lokacin da za a dauka mafita kawai ga al'ummar da ta wanzu bayan rugujewar karshen duniya don ci gaba, shi ne sake bunkasa ilimi, amma karfinta kan wannan ya dogara ne wajen fahimtar yadda za ta sarrafa wasu tsare-tsare don kirkiro fasahar kere-kere mai amfani.

Dabara mafi kyau ita ce samun kwarin gwiwar tantance yadda ake gudanar da ayyukan kimiyya, don samun karfin yin gwajin tsararrun mahangar tunani kan yadda al'amura duniya ke juyawa dabarar kimiyya ita kanta kirkira ce, wani nau'in ilimi da aka samar don juya akalar al'amura.

Akwai wani abu guda da ke da matukar muhimmanci kan yadda muke gudanar harkokin kimiyya ta daukacin tarihi.

Don samun kyakkyawar nasarar bibiyar nazarin duniya muna bukatar kayan aiki, sannan akwai wani abu guda da ke da matukar muhimmanci kan yadda muke gudanar harkokin kimiyya ta daukacin tarihi.

Sinadari ne mai karfi da ba ya hargagi kuma garai-garai yake. Wannan abin mamaki shi ne gilashi.

Kana bukatar gilashi don yin mazubin sinadarai na gilashi (Test-Tiubes) don fahimtar yadda sinadarai ke hargagi, sannan ka yi ma'aunin zafin jiki da, ma'aunin iska (muhimman al'amura da ake bukatar don bunkasa fasahar kere-kere irin na'urori ko injuna).

Kuma gilashi na iya sarrafa haske a kashin kansa; yin mudubin hangen nesa da tabaron likita (don duba kwayoyin cuta da ba a ganinsu sai da madubin likita).

Don yin gilashi cikin sauki kana bukatar sinadarai uku ne, wato silica da soda da lemun tsami, wadanda za a iya tara su kamar kasa da tsirran teku da alli ko farar kasa.

Kwatanta kokarin Robinsoe Crusoe zai taimaka maka wajen yin gilashi tun daga farko a gabar teku.

Don haka ake sa ran wadannan kayan aiki na mimiyya da kwakwalwa mai fadada tunani, sai ka yi fatan al'ummmar da ta rage bayan russhewar duniya za ta yi suarin farfadowa, tare da kokarin kauce wa shiga wani zamanin duhun jahilci.

Ta yiwu a dauki karni ko fiye, ammma sabon tsarin rayuwar al'umma zai bayyana daga rugujewar karsheen duniya.

Ko yaya irin waccan duniya za ta kasance ya ddanganta ga has ashen kowane irrin mutum, domin t ayiwu ma ta ta samu cci gaban da ya zarta na al'ummar zamanin da muka sani a yau.

Farfesa Lewis Dartnell mai binciken kimiyya ne, kuma marubuci a Jami'ar Westminster.

Wannan Makala ya samu kwarin gwiwar rubuta ta ne daga littafinsa mai taken: Ilimi: yadda za a fara gina duniya. (The Knowledge: How to Rebuild Our World from Scratch)