Yadda mutum-mutumi zai kwace ayyukan da muke yi

Wadansu mata Hakkin mallakar hoto Wang He
Image caption Matan Tibet na amfani da wayar hannu a wani kauye kusa da tafkin Yamdok a kasar

Kusan akai-akai labaran fasahar kere-kere iri guda ne daga lokaci zuwa lokaci; taken labaran manyan na'urorin Silicon Valley (katafariyar cibiyar hada-hadar kayan sadarwa, musamman na'ura mai kwakwalwa da wayoyin salula na alfarma).

Da dimbin bayanai ba kakkautawa game manyan wayoyin alfarma; mummuna hasashen yadda mutum-mutumin Robot zai kwace ayyukan da muke yi don neman abin gudanar da rayuwar yau da kullum.

Sai dai a daukacin fadin duniya, ci gaban da aka samu a fannin kimiyya da fasahar kere-kere kai-tsaye suke shafar al'ummomin da ba a cika bayar da labaransu ba, kan yadda rayuwarsu ta sauya da aikinsu da kuma yadda suke hulda da juna.

Fasahar kere-kere na haifar da wargajewar tarayya al'umma akai-akai, don haka yake da muhimmanci a gano inda lamarin ke aukuwa.

Wannan shi ne dalilin da ya sanya muka kaddamar da shirin Duniya ta Daban.

Wato wani sabon sashe a makalun BBC da zai rika bayyana labaran ban mamaki na mutane da ke kowane sako na duniya, wadanda ke amfani da fasahae kere-kere don inganata rayuwarsu - ko kuma suke fafutikar shawo kan matsaloli da kalubalen da fasahar t ahaifar musu.

A yau shirin Duniya ta Daban, mun tattara labarai daga dadaddun al'amuran kundin tarihinmu, kuma a watanni masu zuwa za mu fara wallafa su, kamar yadda aka ruwaito su daga sassan duniya.

Ga wadanda suke sabon shiga, za mu mayar da hankali ne kacokam kan rukunin mata kwararru da ake yin wasannin bidyo a kasar China don shawo kan kyara da bambancin da ake nuna wa jinsin mata a harkar hada-hadar wasannin kwamfuta da ake hada-hadar biliyoyin Dala.

Daga nan za mu tura a bibiyi Kadin al'amuran rayuwa tun daga kasar Somaliya zuwa kwarya-kwaryar saharar yankin Gabashin Afirka.

Al'amarin da zai zamo share fage mai ban mamaki kan yadda ake biyan kudin kasuwanci ta shafukan intanet, har ta kai ga yankin na hankoron zama al'umma adoron kasa da ba sa mu'amala da kudi.

Daga bisani, za mu yi nazarin kamfanin Indiya guda da ke cusda wasannin al'adar Japanawa na Karaoke a fina-finan talabiji na Bollywood da fina-finai don yada ilimin manya.

A wannan zamani da fasahar kere-kere ke kara kaimin wargaza tarayyar al'umma akai-akai, yana da matukar muhimmanci a san inda al'amarin ke faruwa - kuma wadanne mutane suka tasirantu da faruwar lamarin.

Ku biyo mu tafi tare don kutsawa cikin duniya tare da rukunin wakilanmu, wadanda za su kawo muku makaloli da hotunan bidiyo da za su kusanta ku da mutane na hakika, wadanda fasahar kere-kere ta sauya rayuwarsu.

Duniyar nan na da girma. Don haka za mu tabbatar da cewa a rika bayar da muhimman labarai.