Abubuwa 17 mafi ban dariya a duniya

An fara wallafa wannan labari ranar 15 ga watan Oktoba 2015. An sake sabunta shi.

DBIMAGES ALAMY

Asalin hoton, DBIMAGES ALAMY

Rayuwa na da ban sha'awa da ban mamaki, amma a wani lokaci ta kan iya zama mai ban dariya ko takaici ko maras kan gado ko ma sakarci.

A kan haka ne muka tattara wasu abubuwa 17 da suka fi ban dariya a duniya.

Biri mai katon hanci:

Ko da yake mutane za su iya ganin kamannin wannan biri kamar abin dariya kan yadda yake da katoton hanci, amma sauran 'yan uwansa birai masu katon hanci aka sin hakan za su yi tunani.

Saboda masana na ganin wannan babban hanci nasa yana ba wa matansu sha'awa har su so wanda ya fi babban hancin, wato dai kamar yadda dawisu yake jan hankalin tamatarsa da kyawun gashin jela.

Haka kuma wannan girman hanci yana iya sa namijin birin ya iya yin kara mai karfi domin fadakar da 'yan uwansa idan ya ga wani makiyi ko abin da zai cutar da su.

Bayan girman hanci kuma, irin wannan biri yana da wani abu na daban din kuma.

Wannan karin baiwa ita ce ta yin tikar abinci, kamar yadda shanu suke yi. Ana ganin shi kadai ne irin dabbar da ta yi kama da mutum da ke da wannan dama.

Asalin hoton, BLICKWINKEL

Namijin jimina yana jima'i ne na dan kankanin lokaci:

Namijin jimina na daya daga cikin 'yan kalilan din tsuntsayen da suke da azzakari, amma kuma shi nasa ba za a ce yana da kyau sosai ba.

Azzakarin mutum yana amfani da jini ne, abin da ke sa ya tashi kyam kuma ya tsaya a haka har tsawon wani lokaci ko mintina da dama.

To amma shi azzakarin namijin jimina daban yake domin yana amfani da ruwan jikin tsuntsun ne wajen tashi ba kamar na mutum ba da ke amfani da jini, saboda wannan ruwa bai kai karfin jini ba sai ya zamana azzakarin ba ya dadewa idan ya tashi matuka ya yi 'yan dakikoki.

Asalin hoton, NATURAL SCIENCE MUSEUM ALAMY

Farcen wucin-gadi na kwado mai gashi:

Wannan kwado mai gashi da aka samu daga kasar Kamaru, yana da wani makami na sirri. Kafafuwansa na baya suna da wani kambori ko farata (farce) da yake iya fadada su kamar na kyanwa.

Sai dai wadannan farata ba sa aiki kamar na kyanwarka ta gida. Farata ne na kashi kuma suna zaman wani bangare ne na 'yan yatsun kwadon.

A duk lokacin da yake ganin yana cikin wata barazana, sai ya karya kashin ya fitar da farcen ta cikin fatarsa.

Asalin hoton, DANIEL MIETCHEN

Dabbar da ta fi yawan kafafuwa a duniya:

Duk da sunansa na Ingilishi (millipede), wanda ke nuna miliyoyin kafa da yake da, shansani ba shi da kafafuwan da suka kai yawan 1000.

Akwai wani nau'in shanshanin mai kafafun da yawa da ya fi duk wata dabba da aka sani.

Kuma matan wannan nau'i suna da kafa da ta kai yawan 750. Ba dai wanda ya san dalilin hakan.

Ita dai wannan mata ta shanshani ana samunta ne kawai a wani wuri mai murabba'in kilomita 4 da rabi a California da ke Amurka, wurin da kuma aka ki bayyana shi ga jama'a domin kareta da sauran nau'in kwaron.

Asalin hoton, CHINAFOTOPRESS

Kwadi suna da gashin baki:

Wannan irin kwado (emei) yana da gashin baki mai tsini, wanda yake amfani da shi wajen fada da sauran mazajen kwadi saboda mallakar muhalli.

Gashin bakin wanda mazaje ne kawai suke da shi ban da matansu ba na gashi ba ne, illa dai ya fito ne a wurin da yake kamar gashin baki.

Shi yana da karfi wanda kuma ya fito ne daga gefen leben kwadon na sama.

Kowane kwado yana kokarin ya caka wa abokin fadansa gashin bakin domin ya huda masa ciki.

Asalin hoton, LOUISE MURRAY SPL

Shi ma gizo-gizo yana da gashin baki:

wannan irin gizo-gizo shi ma yana da gashin baki, wanda ba yana da shi ne kawai domin ado ba, yana amfani da shi ne wurin farauta.

Farin gashin yana fitowa fili a cikin duhun dare, inda ta haka yake jawo hankalin kwaro ko wani abin da zai kama.

Kwari ba sa sanin gizo-gizo ne a wurin saboda haka da sun biyo wannan farin gashi sai ya kama su.

Asalin hoton, IVAN KUZMIN ALAMY

Jemagu suna jima'i ta baki:

A kebe da daddare a cikin 'yan dakunansu na ganye, akwai 'yan kananan dabbobi masu gashi da suke jin dadin yin jima'i ta baki.

Musamman a China akwai jemagun da suke wannan da junansu.

A yayin jima'i tamatar jemagen ta kan sunkuya ta rika lasar wurin tushen mazakutar namijin, ta yadda za su dade suna saduwa.

Ko da yake mutane sukan yi jima'in ta baki, akwai wasu dabbobin kadan da su ma aka san suna yi.

Birai ma suna yi a wani lokaci, sai dai suna yi ne tsakanin matasan maza kuma kamar wasa ne suke yi ba a matsayin jima'i ba

Asalin hoton, WILLIAM A HADDAD POLAR BIOLOGY

Fyade tsakanin dabbobin ruwa;

Abin dariya, lokacin da aka bayar da rahoton wani namijin katuwar dabban ruwan nan da ake kira ''seal'' a Ingilishi ya yi jima'i da wata dabbar ruwan da ake kira ''peguin'' a 2008, sai abin ya zama wani babban labari a kafafen yada labarai na duniya. Da kuma lokacin da abin ya kara faruwa har aka dauki hotonsu a 2014.

Ba wanda ya san dalilin da ya sa babbar dabbar (seal) ta yi wa karamar (penguin) wadda ga alama ba da son ranta ba ne.

Wata dabbar da aka yi wa ma irin wannan fyade nan take 'yan uwanta suka cinye ta.

Asalin hoton, MARTIN BERNETTI AFP GETTY

Dabbar nan ta ruwa ''Penguins'' ba ta san dandanon kifi ba:

Karin wani mugun labarin akan wannan dabba da ake kira ''penguin''. Duk da cewa kifi shi ne abincin da wannan dabbar ruwa ta fi samu, bincike ya nuna ba su san dandanon kifi ba domin ba tauna shi suke yi ba sai dai kawai su hadiye.

Binciken wanda aka wallafa a watan Fabrairu na 2015 ya gano cewa ba sa iya sanin dandanon kifi, suna da kwayoyin halittar jin dandanon gishiri ne da tsami.

Asalin hoton, CHRISTINA GANDOLFO ALAMY

Shanu suna son kayan maye:

A Amurka da Mexico shanu suna cin wata ciyawa (Astragalus da Oxytropis) wadda take sa su maye, ka ga suna tafiya suna hada hanya, ko suna fadawa wasu abubuwa da sauran yanayi na maye.

Asalin hoton, VISUALS UNLIMITED

Tururuwa tana shan jinin 'ya'yanta:

Shan jinin wani abu ne maras kyau, to ina kuma ace jinin danka za ka sha, wannan ai abu ne mai muni sosai.

To amma wannan shi ne abin da wata turuwa (dracula ant) take yi. Sukan huda jikin 'ya'yan nasu su tsotsi ruwan jikinsu wanda shi ne daidai da jininsu.

Sai dai kuma 'ya'yan ba sa mutuwa saboda wannan sai dai jikinsu ya huhhuje.

A shekara ta 2014 ne aka gano irin wannan tururuwar, wadda take rayuwa a cikin rubabben itace a Madagascar.

Asalin hoton, MATTIAS ORMESTAD

Dabbobin da suke da takashi mai aiki iri-iri:

Nau'in wata tsutsar ruwa da ake kira ''sea cucumber'' da Ingilishi suna da takashin da suke amfani da ita ta abubuwa daban-daban.

Bayan kashi tsutsar tana yin nimfashi ta takashin, sannan kuma tana amfani da ita wajen kare kanta daga makiya.

Duk lokacin da wani kifi ko kaguwa ta neme ta da fada sai ta juya fuskarta ta kawo takashinta, ta bude sannan kuma ta feso wasu daga cikin kayan cikinta waje ana ganinsu suna yawo. Wata nau'in ma hatta kayan cikinta da take numfashi da su tana fitarwa ta takashin.

To amma ba tana yin hakan ba ne domin wata birge ba, domin wannan kayan cikin da ta fitar daga cikinta ta takashi za su nannade abokin gabar tata ne, ita kuma ta tafi abinta lafiya kalau. Daga bisani sai ta sake samar da wasu kayan cikin a cikin nata.

Asalin hoton, BRENT STEPHENSON NPL

Bayanan hoto,

Abin sha'awa

Feshin fitsari da dabbar ruwa (penguin) ke yi:

Tun da muna maganar takashi ne wannan dabbar ta ruwa da ake kira Penguin a Ingilishi tana da wata baiwa ta musamman.

Ba maganar yadda take jure rayuwa cikin tsananin sanyi ba, ba batun iya linkayarta a karkashin teku ba ba kuma maganar dabarar da take yi ta tashi sama daga ruwa. Wannan dabba ce da ta lakanci tusa.

A shekara ta 2003 masana kimiyya sun gano cewa wannan dabbar ruwa tana fitar da tusa da karfin iska linki biyar zuwa goma na yadda mutum yake tasa tusar.

Suna yin haka ne domin ka da su bata sheka ko gidansu. Ta hakan za su iya yin tusarsu ba sai sun fito waje daga shekara tasu ba.

Asalin hoton, BLICKWINKEL ALAMY

Kunkuru mai fitsari ta baki:

To idan kokarin da waccan dabbar ruwan take yi na tusa bai isa ba, wani nau'in kunkuru mai kokon baya mai taushi da ake samun irinsa a China, shi yana fitsari ne ta baki.

A duk lokacin da wannan kunkuru ya ji fitsari sai ya nemi inda ruwa ya taru kawai ya sa kansa ciki ya yi fitsarinsa.

Yana fitsarin ne kuwa ta wata halitta a bakin nasa mai kama da dan yatsa, wadda yana amfani da ita ne wurin numfashi, amma kuma ya ke fitsarin da ita.

Asalin hoton, WEN ZHONG WILEY

Kuda mai karin makale matarsa:

Wannan wani nau'i ne na kuda da ake kira ''scorpionfly'' da Ingilishi, wanda namiji yake da wani kari kamar na kunama a can wurin takashinsa ko mazakutarsa.

Namijin yana amfani da karin ne mai kamar na kunama wanda shi ya sa ake danganta sunansa da kunama (kudan kunama), ya makale matarsa idan suna saduwa.

Ya kan iya makale matar tsawon sama da sa'o'i biyu idan suna saduwa.

Asalin hoton, IVAN KUZMIN ALAMY

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Jemage kan shashantar da dan uwansa:

Can a sama inda suke shawagi, jemagun Mexico, sukan fafata yakin sauti, inda wani yake amfani da sauti ya kadar da hankalin wani jemagen dan uwansa da yake gab da kama wani abincinsa ko ma ya dauke abinci.

A binciken da masana suka yi inda har suka nadi wannan sauti, sun gano cewa jemagen yana shashantar da hankalin dan uwansa da yake gab da kama wani kwaro abincinsa, shi kuma ya dauke.

Mutane za su iya tafiya a kan ruwa a duniyar wata

Ba shakka mutane ba za su iya tafiya a kan ruwa ba a duniya, amma sukan iya yin hakan a wata duniyar.

Wani nau'in kwari da kadangare na iya tafiya a kan ruwa amma mutum ba zai iya ba saboda nauyinsa da kuma yadda ba zai iya yin saurin da ba zai nutse ba.

Za a ga kamar wannan binciken ba shi da wani amfani, amma za a iya amfani da abubuwan da aka gano ta hanyarsa wajen krea butun-butumin da zai iya yin wasu abubuwa da rayuwar mutane da dabbobi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The 17 most ridiculous things on Earth