Yadda dubura ta samo asali

Wannan hoton dan kwikwiyo ne ya juyo bayansa

Bayanan hoto,

Dan kwikwiyo

Eh! Wannan hoton dan kwikwiyo ne, ya juyo bayansa. Ko da yake gaskiya ba za mu iya bayanin wannan labarin da hoton takashi ba, ko za mu iya yi a yanzu tun da kun san inda muka nufa?

Kafin mu fara tattaunawa a kan asalin ita takashi, bari mu dan koma baya kadan.

Wannan dai magana ce da ke tattare da abin da za mu iya cewa kunya ko kuma fadin gaskiyar lamari.

An fahimci abin da nake nufi? Saboda haka bari mu kokarta mu mayar da hankali, mu tambayi me ya sa ba wanda ya taba tunanin ya binciki wannan abu mai daure kai a baya?

Shin abu ne da ba shi da muhimmanci ko bai dace ba a yi bincike a kansa, ko kuma za a iya cewa rashin yin bincike a kai sauran masana kimiyya sun kasa kenan? Shin ko yin bincike ko rahoto a kai wani dan cibaya ne?

Idan muna da sha'awar sanin da yawa daga cikin muhimman tambayoyi kan yadda dabbobi suka samo asali da yadda suke aiki, to sai ka kama karatun wannan bayani.

Saboda ba dadewa masana kimiyya suka wallafa wani nazari a kan asalin takashi, kuma a sanadin hakan, sun nuna yadda maganar take da muhimmanci fiye da yadda aka dauka kafin a fara binciken.

Bayanan hoto,

A tsuntsaye takashi da farji a hade suke

Wannan shi ne saboda takashi na daya daga cikin muhimman sassan jikin dabbobi da yawa, wadda halitta ce da ke sauya yadda kayan cikin mutum, wadanda ke sarrafa abinci suke aiki.

Dan kuikuyonmu zai iya ci ya rayu ya kuma girma ba tare da takashi ba. Amma abin mamaki ba dukkanin dabbobi ba ne suke da ita.

Wasu suna da guda daya ce kawai wasu kuma suna da ita da yawa, yayin da wasu kuma tasu takan fito kuma ta bace.

Wadansu dabbobin kuwa suna da wadda, me za mu iya ce mata.... mai amfani ko ayyuka iri daban-daban?

Amma dai dabbobin da suke da takashi, halittar da ba ma iya ambatatonta sai mun ji kunya, ko kuma ma idan har mun fadi sunanta sai mu ji daban, suna da ingantaccen tsarin sarrafa abinci a cikinsu.

Za su iya cin abinci su bunkasa da kyau, kuma jikinsu ya kai wani mataki na girma sosai.

Saboda haka maganar yadda takashi ta samo asali, labari ne a zahiri na yadda dabbobi suka faro, suka rika sauyawa daga iri kaza zuwa iri kaza, har suka zama halittu masu siffa da sassan jiki da ke aiki iri daban-daban.

An wallafa sakamakon wannan bincike na asalin takashi ne a mujallar 'Zoologischer Anzeiger'

Masanin kimiyyar halittu Dakta Andreas Hejnol da Dakta Chema Martín-Durán, na jami'ar Bergen da ke Norway, sun gudanar da binciken ta wani bangaren saboda ba wanda ya yi shi.

A shekarunnan masana kimiyya sun yi kokarin nazarin yadda wasu kwayoyin halitta suke shafar samuwa ko bunkasar nau'ukan halittu da dama.

''Wannan shi ya farfado da sha'awar sanin asalin tsarin sassan jikinmu. Daga ina aka samu kwakwalwa? Ta yaya jini ya samu?'' Kamar yadda Dakta Hejnol ya gaya wa BBC. ''Duk da cewa an gudanar da bincike kan sauran sassan ayyukan jiki, kamar na motsin jijiyoyi da tsoka, kusan a ce kawar da kai a kan kofar takashi.''

Amma ta hanyar sauyin yanayin halitta, takashi ta kasance ta hanyoyi ko kamanni da dama, inda a wani lokacinma sai ta sake bacewa.

''Abu ne da ke da ban sha'awa a yi bincike kan yadda sauyi a yawan kwayoyin halittu, lokacin juyin halitta yake haifar da siffar yadda wannan kofa za ta kasance, in ji Dakta Hejnol.

Kasancewar takashi ba shakka abu ne da ke da alaka da juyi ko sauyin halitta na kayan cikin da ke sarrafa abinci a ciki.

Kayan cikin da ke sarrafa abinci na daya daga cikin mafi muhimmanci a jikin duk wata dabba, inda suke tabbatar da narkewar abinci da karbar sinadaran gina jiki wanda hakan zai tabbatar da dorewar jikin.

Duk da wannan wasu dabbobin ko halittun suna iya rayuwa ba tare da kayan cikin da ke sarrafa abinci ba, misali irin wadannan halittun da suka hada da tsutsar ciki da halittar nan mai kama da soso da ake kira 'sea sponges', wadanda kuma a zahiri ga alama ba su da takashi.

Wadannan halittu za a iya cewa suna da irin tasu takashin, domin kofa daya tak da suke da ita a matsayin baki da kuma takashi, suna amfani da ita wurin cin abinci da kuma kashi.

Bayanan hoto,

Wannan halittar (sessile Membranipora) tana da baki da takashi kusa da kusa

Halittun cikin ruwa da dama suna sarrafa abinci ne ta haka, kamar yadda nau'in tsutsar ciki da yawa suke yi, su ci ta baki su kasayar ta baki.

Dakta Hejnol ya ce wasu halittun ko dabbobi suna da baki da takashin ne kusa da kusa (ga baki ga hanci).

Akwai kuma wasu dabbobin 'yan kadan da suke da abin da Hejnol da Martin Duran suka bayyana a matsayin takashin da ke bacewa.

Wata halitta da ake kira ''Haplognathia'' da kuma wata '' Limnognathia'' wadda aka gano a 1994 suna da kofa ta wucin-gadi a jikinsu, wadda masu bincike suke ganin ta nan watakila take kashi a wani lokaci, ko da yake ba a taba ganin halittun na yin hakan ba.

Kokarin fahimtar lokaci da kuma dalilin da ya sa takashi ta samo asali abu ne mai wuyar gaske, saboda wani lokacin ana ganinta a wani lokacin kuma sai ta bace a jikin wasu dabbobin.

Bayanan hoto,

Tsutsa mai kamar faifai; tana da takashi da yawa

Yayin da wasu tsutsotsin da yawa masu kama da micijin ciki ba su da takashi, wasu nau'ukan tsutsar suna da ita. Wasu kuwa suna da takashin da yawa a bayansu.

Wasu dabbobin da suka hada da na ruwa da masu kashin baya kamar tsuntsaye da kifaye da masu shayar da nono kamar mutane suna da kofa a can bayansu ko kasansu ne.

Wasu dabbobin kamar su kadangare da wasu tsuntsayen takashin nasu tana hade ne da farjinsu. Amma kuma wasu dabbobin da ke wannan rukuni na halittu misali wadanda ake kira''sea stars'' ba su da takashin.

Tarihi da kuma aikin na takashi na kara shiga duhu, domin wasu dabbobin suna girma da ita amma kuma can gaba a rayuwarsu sai ta bata.

Wasu nau'ukan kunami su kan gutsire jela ko bindinsu domin su tsira daga wata dabbar da ta kama su.

A yayin da suka gutsire jelar tasu, sun rasa takashinsu a hakan domin tana jikin jelar ne.

Tun da jelar ba ta sake fitowa, kuma inda ta gutsire zai warke, kunamar ba za ta sake yin kashi ba kenan, sai sashen jikinta na baya ya rika girma ko kumbura da kashi.

Wannan abin da yake faruwa da wannan nau'in kunama yana nuna muhimmancin takashi biyu da wasu dabbobin suke da ita, a wurin kansu da kuma can bayansu.

Bayanan hoto,

Wannan kunamar idan jelarta ta katse ta rasa takashinta kenan

Dakta Martin-Duran ya ce dabbobin da suke da kofofi biyu wato baki da takashi maimakon kofa daya kawai, suna da amfani biyu.

''Da farko dabba za ta iya cin sabon abinci yayin da take sarrafa wani a cikinta,'' ya ce saboda abincin yana tafiya ta hanya daya ne a cikin jiki.

Amma dabbobin da suke da kofa daya kawai,sai sun jira sun gama sarrafa tsohon abincin da suka ci kuma sun kasayar da ci ta wannan kofa daya (wadda ita ce baki da kuma takashi) kafin su ci sabon abinci.

''Ka yi tunani ka gani idan sai mun jira har sa'oi tara kafin mu ci abincin rana, saboda kawai ba mu kasayar da abincin da muka ci da safe ba,'' ya ce.

Yanayin halittar wasu dabbobin kuma ba zai da ce ba idan kofa daya kawai suke da ita. Misali tsutsar da ke zaman dabbar da ta fi tsawo a duniya wadda ake kira ''ribbon worms'' wadda ta kai mita 60 (60 metres), za ta sha wahalar narka abinci, in ji Dakta Hejnol.

Ko kuma ka kalli lamarin ta wata hanyar, tsawon mita hamsin ko sama da haka ba karamin nisa ba ne da kashi zai je ya dawo.

Amma idan akwai wata kofar (takashi) a can baya ko karshen tsutsar sai ta fitar da kashin ta can kawai.

Bayanan hoto,

Abinci na tafiya mai nisa a cikin wannan tsutsar (Ribbon worm Llongissimus)

Abu na biyu kuma dabbar da ke da kofofi biyu, baki da takashi za ta iya raba ayyukansu, kowace kofa tana wani aiki na daban na musamman. Kamar yadda muka san ayyukan da baki yake yi da kuma wanda takashi ke yi, kuma kowanne da irin kwayoyin halittarsa.

Babban misali shi ne shanu a cikin dabbobi masu shayar da nono, domin saniya tana da gida-gida a cikinta da take amfani da su wajen sarrafa ciyayi da tsirran da suke da wuyar sarrafa wa.

Misali a kan mu kanmu mutane, muna tauna da bakinmu, mu sarrafa sinadaran abincin a cikinmu, ruwan madaciya ya taimaka wajen sarrafa sinadarin maiko, kuma a karshe jikinmu ya yi amfani da sinadaran ta hanyar karamin hanji.

''Abu ne mai wuya ka iya tunanin yadda za a sarrafa abinci da kyau da cikin da yake kamar jaka ko buhu ba takashi,'' in ji Dakta Martin-Duran.

Saboda haka amfanin takashi a nan abu ne da yake a bayyane. Abin da ba a gane ba sosai shi ne a wana lokaci da kuma daga ina takashi ta samo asali a a tarihin sauyin halitta kamar yadda masana kimiyya ke nuna asalin halitta.

Bayanan hoto,

Takashin saniya daban take

Tsarin inda takashin take kasancewa da kuma rashinta a jikin dabbobi abu ne mai ban mamaki sosai,'' kamar yadda Dakta Hejnol ya ce.

Nazarin Hejnol da Martin-Duran ya tabbatar cewa wasu jerin kwayoyin halitta biyu da ake kira ''brachyury da ParaHox, wadanda suke jikin kusan dukkanin dabbobi, suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da takashi.

Dabbobin da suke da takashi, kusan dukkaninsu suna da wadannan kwayoyin halitta a nama ko tsokar da ke wurin takashinsu, su kuma marassa takashin ba su da kwayoyin halittar.

Bayanan hoto,

Wannan tsutsar (Acoel flatworms) za ta iya ba wa masanan damar sanin asalin takashi

Duk da muhimmancin da aka gani na takashi, wani abin mamaki mai rikitarwa shi ne, nau'in wasu dabbobin a sauyin da suka yi na halitta, sun rabu da takashin, ba kamar yadda aka gani ba a jikin kakanninsu.

Wanda wannan ya taso da tambayar cewa me yasa suka rasa wannan muhimmin abu.

Masanan biyu suna karin bincike domin gano dalilin da ya sa aka samu wannan sauyi.

Suan da tabbacin cewa takashi ta samu ne daban daga sauran sassan jikin dabbobi fiye da sau daya. '' Amma asalinta mai tsawon tarihi abu ne da har yanzu ba a kai ga ganowa ba,'' in ji Dakta Hejnol.

Nazarin nasu ya samar da sheda mai muhimmanci, duk da cewa samuwar takashin na da alaka da wata halittar jikin wadda dabbobi ke amfani da ita wurin jima'i.

A yanzu suna gudanar da bincike a kan wasu dabbobi, wadanda halittu ne na da sosai. Wadanda suka yi kama da tsutsotsin da suke shafaffu, kamar allo, marassa kauri da kuma ba su da wani tsawo, kuma wadannan halittu suna rayuwa ne a teku.

Ba su da baki sam-sam, sannan ba su da takashi, kuma ba su da hanyar numfashi ko zagayawar jini a jikinsu.

A takaice jikinsu kamar dutse ne da babu wani abu a ciki. Amma kuma duk da haka suna fitar da maniyyi, wanda suke fitarwa ta wata kofa.

Dabbobi da yawa da ba su da kashin baya suna amfani da irin wannan kofa ce, wajen fitar da mani da kwayaye, kuma bincike ya nuna cewa ga alama samun wannan kofa na da alaka da asalin wata kofar, wannan kofa kuwa ita ce takashi.

Dakta Hejnol ya ce, '' nazarinmu shi ne kofar takashi tana da wata alaka da waccan 'yar kofa da mazan wadannan halittu suke da ita.

''Wannan ba shakka shi ya kara rikitar da al'amarin. Ko da yake haka tsarin halitta yake, domin ita halitta ba ruwanta da wani abu na kunya ko saba al'ada a cikin al'umma.''

''Abu ne mai wahala ku yi wata tattaunawa mai ma'ana a kan wannan batu,'' in ji masanin shi kansa.

Ya kara da cewa,''ya fi sauki sosai ka yi magana a kan asalin jima'i da abin da ya shafe shi kan ka yi magana a kan asalin takashi.''

Bayanan hoto,

Wannan halittar ruwan (Sea cucumbers) tana da takashi mai amfani iri-iri

''Wannan ya nuna abin da muke yi kullum masai ko salga karar abu ne da ya sabawa al'ada a kasashen da suka ci gaba.''

''Watakila bincikenmu zai iya taimakawa wajen kawo sauyi kan yadda ake daukar wannan lamari, ta yadda za a iya tattaunawa a kai a bayyane.''

Kuma da hakan watakila za mu iya samun wata hanya sabuwa, da ba za ta sa mutane dariya ba sosai, ta mutunta abin da mutane da dama har yanzu suke kallo a matsayin halittar jikinmu da ta fi ba da kunya.

Misali halittar nan da ake kira ''sea cucumber'' (kukumbar teku) tana da takashi mai aiki da yawa. Ba kashi kadai halittar take yi ba ta kofar hatta numfashi ma ta nan take yi.

Idan wannan bai burge ka ba, kana son ka ji wata kalma ce da za ta bayyana wurin yadda yake sai in yi tunanin amfani da kalmar minta da 'wurin da rana ba ta haske'. A ji da hakuri abin ne ni ma ya zamar min dole.

Bayanan hoto,

Ga 'yar mage, idan kana bukata

Ko kuma idan har yanzu shaukin maganar bai sake ba, to ga wani kyakkyawan hoton abar, amma a wannan karon ta 'yar mage ce.

Idan kana bukatar karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The origin of the anus