Yau gawar Kofi Annan za ta isa Ghana daga Switzerland

Kofi Annan Hakkin mallakar hoto Reuters

A yau ne ake sa ran gawar marigayi tsohon babban sakataren MDD Mista Kofi Anan za ta isa kasar Ghana daga kasar Switzerland.

A ranar 18 ga watan Agusta Marigayi kofi Anan ya rasu bayan wata gajeriyar jinya.

Mista Annan ya mutu yana da shekara 80, kuma ya shafe shekara tara yana jagorantar Majalisar Dinkin Duniya.

Ya shugabanci majalisar ne a daidai lokacin da hare-haren da aka kai wa Amurka na 11 ga watan Satumba suka auku, wadanda suka zama sanadin harin da Amurkar ta kai wa Iraki a 2003.

Ya taka rawar gani wajen kawo sulhu a wasu daga cikin rikice-rikicen da suka hada da na yakin basasar kasar Syria.

Kofi Anan ne bakar fata na farko da ya zama babban sakataren MDD, kuma ya taka rawar gani a bangaren wanzar da zaman lafiya a nahiyar Afrika da ma duniya baki daya.

Labarai masu alaka